♀🙆🏼♀ *ILLAR RIƘO*_*( Ƴar riko)*_
_Sabon Salo_
*Na*_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com_*Dedicated to all my fans, ina yinku irin sosai ɗin nan*_
_*BISMILLAHIR-RAHIM-RAHEEM*_
_Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah Ubangijin talik'ai wanda ya bani ikon kawo maku wannan labarin mai suna *ILLAR RIƘO ('yar riƙo)*, ina fatan zai wa'azantar haɗa da faɗakar daku kuma ya zame shiriya ga masu irin wannan halin da musulmai baki ɗaya._
_*Wannan labarin ba sabo bane illar riƙo na yi editing, na sabonta don jindaɗin ku masoya na, da fatan zaku bani goyan ba ya ta hanyar comment*_
_*Page 1*_
"Bintu...,bintu... wai mai kike a ɗakin nan har yanzu baki fito ba, kin dai san tafiyar dake gaban ku nisa gareta ko!, gashi har rana ta yi ".
" Yo inna ina ita Bintu ta sani tunda ba zuwa ta taɓa yi ba, ki bari ta kintsa a hankali tunda tafiyar ba ta dawowar yanzu ba ce."
"Ke dai Jameela baribna tashi na dubota, wallahi baki san shiririta irin na Bintu ba ne..." Inna ta faɗa sannan ta miƙe ta nufa ɗaki.
Zaune ta iske Bintu ta haɗa kai da gwuiwa sai kuka take yi. Da sauri ta ƙaraso wurin sannan ta da fata " Bintu birnin ne baki son zuwa ko wani abun ne ya faruwa?", gyaɗa kai ta yi ido cike da kwalla sannan ta ce " Inna ni dai babu inda zani".
Murmushi Inna ta yi ta ce " haba 'yar lelen na baki son ki yi ilmin ne kuma, kiyi kuɗi ki siyan min mota da gida mai kyau?"
"Ina so Inna amma ni bana son barin ke ɗaya. Idan na tafi yanzu Inna wa zai dinga zuwa rafi ɗebo maki ruwa?"
"Karki samu damuwa, ni dai buri na kiyi ilmi ki zama wata a rayuwa domin burin mahaifinki kenan kafin rasuwarsa."
"Toh Inna na ina sonki Inna,hawaye ta goge mata ta ce " nima ina sonki Bintuna, maza tashi muje ku hanzanta tafiya kinga tun ɗazu take jiranki."
Zaune suka sameta gunda suka barta Inna ta ce " sannu Jamila mu barki kina ta jira." Murmushi ta yi ta ce " babu komai Inna ai ba wani daɗewa kuka yi ba."
"Toh Jamila ga Bintu nan, kema dai kinsan yanda muke da ita,don Allah ki riƙe ta amana ki ɗauke ta tamkar 'ya da kika haifa, don Allah ki maye mata gurbin mahaifiyarta."
"In Shaa Allahu, Inna zanyi iya bakin ƙoƙari na," tashi ta yi ta ce "toh bintu muje ko."
Tashi Bintu ta yi da nufin tafiya, tana yi tana waigawa ga Inna wacce itama kwalla ya ciko idanuwanta sabida sabon dake tsakaninta da Bintu sai Allah. Bintu na kaiwa daidai baki kofar fita ta juyo a guje ta rungume Inna tana kuka, rarrashinta Inna ta shiga yi da k'yar ta samu tw rabata da jikinta, ta yi shigewanta gidan tana mai goge hawaye daka zubo mata.
。。。。。。。。。
"Assalamu alaikum......" wata 'yar dattijiwa ta yi sallama a falon haɗa da banko ƙofar falon ba tare da ta jira an amsa mata sallamar ba.
_Idan na samu comments yanda ya kamata zan ci gaba da maku posting._
_*Mummy's friend ce*_

YOU ARE READING
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Short StoryEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.