7

120 10 0
                                        

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIKO*
_*('Yar riko)*_

*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*Dedicated to all my fans*_

_*Ną яίЌ€ ąℓЌąώąяίŋ Ќί čίЌίŋ яąί ŋą ąjί¥€, ŋąЌ€ ¥ίŋ ţ$ąя๏ Ќµℓℓµ๓ ίŋą ţ$ी, βąčίŋ яąŋЌί βąŋą $๏ $Ђί ŋą Ќί¥ą¥€, ąί ţµŋďą Ќ€๓ą βąЌ¥ą $๏ŋ ŋą¥ί Ђąώी Ќ๏ďą βąЌί ŋąŋ Ќίŋą ŋąŋ ą źµčί¥ą. OЂ ŋί!ţąώąŋ ώ๏яď$ ąℓ๏ŋ€ čąŋ'ţ €жρя€$$ ๓¥ ℓ๏ѵ€ ƒ๏я у๏µ. Iŋą уίŋЌί ίяίŋ sosai ďίŋŋąŋ ๓µ 🅱K. Kί ďąď'€ Ќί¥๏ ЌąяЌ๏, ďµЌ яίŋţ$ί ďµЌ ώµ¥ą ąŋą ţąя€ ţąώąŋ (Sarkin masifa😝😝😝🙊 lah na manta ashe dai kece tawan ). Love you dearie😍😘😘.*_.

_*Wąŋŋąŋ $Ђąƒίŋ $ąďąµЌąяώą ŋ€ δąя€Ќί ţąώąŋ BίℓЌί$µ Z. Yąµ ( 🅱Ќ ).*_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*Page 7*_

Kwanaki sun ja, makonin sun tafi yanzu kimanin wata uku kenan da fara zuwa makarantan su Bintu. Alhamdulillah babu laifi suna gane karatun domin aƙalla Bintu zata iya rubuta sunanta da kuma three letter words.

Hakan yake wurin Luba itama babu laifi tana ƙoƙari, sai dai makarantan ya fara gunduranta domin babu ranar da ba'a basu aikin gida _(home work)_.

Zaune suka a falo suna kallo kasancewa yau weekend babu skul. Ammi ce ta shigo da sallama, wuri ta nema ta zauna tana faɗin " hala duk kun idda aikin gidan da aka baku a makaranta ne ko?"

"A'a Ammi saida yamma idan mun dawo daga islamiyya" Yusrah ta bata amsa, Luba kam ko jinsu bata yi hankalinta duk ya tafi ga kallon da take.

"Toh sai kun dawo, don Allah banda wasa kun ji Yusrah."

"In Shaa Allahu Ammi."

Daga haka Ammi bata ƙara cewa komai ba suka ci gaba da kallon su.

_(All work without play make Jack a doll boy, please a riƙa bari yara suna ɗan samu hutu, ba wai kullum cikin karatu ba, lol. Allah ya albarka ci zuri'a mu, ya basu ilimi mai amfani da albarka.)_

Da misalin ƙarfe biyu na rana suka shirya cikin uniform ɗin su na islamiyya Luba sai turo baki take. Murmushi Yusrah ta yi ta ce "mu tafi karda mu yi latti."

"Mtsw! wai ashe haka ake a birni kullum kenan baku da aiki yine sai zuwa makaranta, nidai wallahi na gaji."

Dariya Yusrah ta tuntsire dashi " I told ai na ce wataran sai kin ji makarantar ta ishe ki gashi tun ba'a kai ko'ina ba har kin fara mita."

"Toh gani na yi abin bana ƙarewa ba ne, babu ranar hutu fa har da Alhamis sai anje wani wai shi tahfiz."

Ita Yusrah bata kuma cewa da ita komai illa dariya da take faman yi har suka isa makaranta.

Suna isa makaranta ko waccen su ta nufa ajinta. Zaune Luba ta iske Bintu ko sallama bata yi mata ta ce "wai ke Bintu ba ki gajiya kullum sai kin riga kowa zuwa."

Murmushi ta yi ta ce "so nake na ɗan sannu na yi nazarin karatu na kafin mall. ya shigo."

"Mai zai hanaki yi a gida?" Luba ta faɗa, sannan ta nema wuri kusa da Bintu ta zauna. Zaman ta ke da wuya sai ga Mallamin su ya shigo da sallama ya nema wuri ya zauna sannan ya masu umurni da suzo su biya karatu.

"Mtsw! Bintu don Allah ɗan tuna min nan kafin na je wannan mugun ya mazgeni."

Murmushi Bintu ta yi sannan ta tuna mata, yana tuna mata kuwa ko bita bata yi ba ta tashi da sauri ta je ta biya masa, babu laifi yau bai ranƙwashe ta ba saboda ta iya. A haka har daliban suka idda biya sannan ya ɗira masu darasi akan allola. Daga bisani ya masu addu'a bayan ya tabbatar da yawancin daliban sun gane darasin.

Suna hanyarsu komawa suna hira Bintu ta ce " anti Rahma yau an koya mana yanda ake allola, daman idan baki kusa shirme nake tafkawa amma yanzu na iya."

"Yauwa sisina haka nake so, a ci gaba da sa ido kin ji?"

Gyaɗa mata kai Bintu ta yi alamar eh sannan ta juya ga Ummi da suke faman hira da su Yurah ta ce " Yusrah,Ummi ku mai aka koya maku yau?"

" Yau ba'a mana darasi ba, en sauka aka fidda a cikin ajin mu kuma har dani cikinsu" Yusrah ta faɗi cike da murna.

"Luba, Ummi, ya na ji kun yi shiru baku ce komai ba?"

Turo baki Ummi ta yi ta ce ₦ni ba'a saka suna ba sabida kawai ina barci sanda ya shigo ban sani kuma na je gunshi ya ce na fiye wasa bazai saka ni ba,wallahi anti ina walima bana ƙara zuwa makarantan nan kullum kenan babu hutu" caraf Luba ta kama zance ta ce "kamar kin sani, anya ni zan ma bari sai na sauka?. Wallahi makarantan ta ishen ga malaman sai cin zali suke."

"Babu mai dukan ku idan har kun yi abinda ake buƙata da ku, mu mai yasa ba'a bugun mu. Makaranta kuwa yanzu kuka fara ta. Mtsw!wallahi ko Fareed baya wannan shirmen da kuke yi " Rahma taja tsaki don abin nasu ya fara isanta.

Ranar lahadi da safe bayan Bintu ta kama aiyukanta da misalin 11.30 ta kwaso uniform zata wanke kenan har ta saka su a ruwa sai ji ta yi ance "ke! ke!! tsaya meye zaki yi."

Murya na rawa sakamokon murya mummy da ta ji ta ce " Uniform zan wanke."

Matsowa kusa da ita Mummy ta yi ta riƙo kunninta ta murd'a " ban hanaki wanki da kan ki ba, salon Daddyn Ummi ya ganki ya ce ina musguna maki ko? "

Girgirza kai Binti ta yi cikin murya kuka ta ce " don Allah ki yi haƙuri, wallahi ba laifi na bane Ummi ce ta ce min kin ce wai na wanke nawa da kaina._

Kunne ta sake murd'ewa haɗa da mata da rankwashi sannan ta sake ta "stupid kawai, gobe ma ki sake zaki gan abinda zan maki" tsaki ta ja sannan ta yi tafiyarta cikin gida ta barta nan tsaye.

Duk abinda ke faruwa akan idon Ummi ya faru Mummy na shiga ciki, Ummi ta ƙaraso wurin da Bintu take tsaye tana kuka, kwalo ta yi mata sannan ta ce " wai in ba Mummy ba harda housegirl za'a yiwa wanki, bari ki ji na gaya maki wallahi gwanda ma kin koya wanki tun yanzu sabida nan gaba ke zaki dinga mana wanki, stupid girl, 'yar ƙauye kawai."

Sokoko Bintu ta yi tana kallonta a zuciyata ta ce "toh wai meye ma'anar *hazgel*" ci gaba ta yi da wanke kayanta tare da ɗaukawar kan koma In Shaa Allah sai ta nemo ma'anar wannan kalmar.

________________________________________________________________________

Washegari Monday during break Bintu ce zaune suna hira ita da k'awayenta ta ce " yawwa Maryam don Allah ko kin san meye ma'anar *hazgel*?"

Dariya Maryam ta tuntsire dashi ta ce "kai Bintu housegirl aka cewa ba *hauzgel* ba."

"Oho dai ai nama yi ƙoƙari, nidai don Allah ki faɗa min ma'anar da hausa."

Maryam ta ce " ina jin 'yar aiki saboda haka na ji ana kiran Uwani 'yar aikin mu amma karki damu zan tambayo maki."

Murmushi ta yi sannan ta ce " nagode Maryam."

Wannan kenan

_*Kuna jin daɗin wannan labarin kuwa?*_

For comment,advice and any correction contact this number

08146960525

Please banda zagi🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼.

_*Mummy's friend ce*_

ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon saloWhere stories live. Discover now