31

80 7 7
                                        

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIKO*
_*('Yar riko)*_

*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*Dedicated to all my fans*_

_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_

*Page 31*

"Meye haka kuma? Daga zuwa sai kuka. Toh ni dai ɗaga ni idan kukan zaki yi, sai ki yi ci gaba abin ki " Cewan Inna.

Ko gizau Bintu bata yi balle Inna ta saka ran tashinta, illa ma ci gabawa da ta yi da kukan..

" Ki tashi nace kan na taɓa..." Sallamar su Jabir ne ya katse mata zance ta, amsa masu tayi tana mai faɗin " ashe tare kuka taho, wannan rigimammiyar bata sanar sani ba ba. Haulat ɗan shiga ciki ɗauko masu tabarma."

Da toh Haulat ta amsa mata sannan ta shiga ɗakin ta ɗauko masu tabarma ta shimfiɗa masu. Ɗakin ta sake komawa ta ɗebo masu ruwan a randa tazo ta ajiye masu. Godiya sukai mata, ko zama bata yi ba tayiwa Inna sallama ta tafi gida da cewan zata dawo zuwa anjima idan baƙin sun tafi.

Gaidasu Inna ta ƙara yi haɗe da tambayar su yanda suka baro gida. Da farha suka amsa mata da lafiya kalau. Yayin da ita Bintu  tun bayan shigowar su da wasu mintina ta tashi zaune dalili irin hararan da Jabir yake ta aika mata dashi, a zuciyarshi fadi yake "wannan yarinyar idan ta samu wuri ba ƙaramin shagwaba zata yi ba, ji yanda tabi ta kanannaye tsohuwa kamar zata karya mata ƙafa."

_Nikam nace ina ruwan ka,😏😏_

Laurat matar Salale ce ta fito daga ɗakinta jikin murya mutane, gaidasu tayi sannan take ta taho masu da abinci. Ɗakin ta ta koma don ta basu wuri su tattauna da Inna.

Daƙyar Inna tayi dasu Jabir suka ci abinci, yayin ita Bintu babu yanda Inna bata yi da ita ba amma taƙi ci komai, Yusrah ce ma ta ɗan tsakura abincin.

Bayan sun kammala Bintu ta kimtsa gun, sannan ta dawo ta zauna daga gafen Inna, dyk suka yi shiru, jin shirun yayi yawa yasa Inna tayi gyaran murya ta ce " Ɗan nan ina dai fatan kowa lafiya dai ko?. "

"Lafiya kalau Inna" cewan Jabir.

"Toh madallah, Amma ya nagan ku da kaya riki-riki haka kamar masu shirin barin gari, ko dai gudun hijira zaku yi ne?"

Murmushi duk suka yi da jin abinda Inna tace, sannan Umar ya ce "Inna ba gudun hijira zaku yi ba, mun dai dawo da Bintu gida ne saboda wasu dalilai masu  ƙarfi."

"Subhanallah! Ince dai ba wani mugun abun Bintu ta aikata ba?" Inna ta ce tana dafa ƙirjinta.

"Ko ɗaya Inna, Bintu 'ya CE da kowa zai so ya samu a matsayin 'ya, natsuwa ta, kamalanta, duk abin burgewa ga duk mutum nagari. Sai dai kash wani dalili zai gabata ci gaba da zama damu. Amma duk da haka In Shaa Allah za'a ci gaba da ɗaukar ɗawaniyyar kamar yanda aka saba lokacin da take gun mu, tun ga cinta, makaranta da dai sauransu. In Shaa Allahu yau ɗin nan kan mu bar garin nan zamu nema mata makarantar da zata ci gaba da karatun ta, don ka Inna muna bukatar ki kwantar da hankalin ki" cewan Umar.

"Toh mungode kwarai da gaske da wannan taimakon, Allah ya saka maku da mafificin alkhairi, kuma ina mai sake baku haƙuri idan ta maku wani laifi ku yafe mata " Inna ta ce ta mai ɗauke dubanta daga Bintu da sai sharan kwalla take.

ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon saloWhere stories live. Discover now