*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIƘO*
_*('Yar riƙo)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*Dedicated to all my fans*
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_*Manzon S.A.W ya ce : Duk wanda ya karanta Subhallahi wa bi hamdihi a cikin yini sau d'ari, Allah zai yafe/kankanre masa kurakuransa, ko da ya kasance misalin kunfar teku.*_
*Page 23*
Farkawa ta yi tana murza ido, kai ta ɗaga ta duba agogon dake jikin bangon " innallahi wa ina ilahi raji'un" ta faɗa ganin har 7:30pm ta yi. Miƙewa ta yi da sauri da nufin tashi, da sauri ta koma sakamokon wani irin zafin da ta ji daga kasanta. Sake tashi ta yi wannan karon a hankali haɗi da dafa bango taje wurin da jakan makaranta ke ajiye, ta ciro rigar makaranta ta sanya. Zama ta yi tana jiran shigowar Suwaid don data farka bata ganshi a ɗakin ba.
Jim kaɗan sai gashi ya shigo ɗakin riƙe da Leda ganin ta zaune ya ce " baby har kin tashi, ya jiki?"
"Ka maidani gida " ta ce maimaikon amsar tambayar da ya yi mata.
"Haba 'yan mata take it easy now oo, kin san bana son ɓacin ranki, so don Allah ki amsa min ya jikin naki?".
"Da sauƙi" ta faɗa a takaice sannan ta miƙe tsaya ta ce " nidai don Allah ka maidani gida nasan Ammi nacan... " zanceta ya katse sakamokon haɗa bakinsu da Suwaid yayi guri d'aya, ture shi ta yi da iya ƙarfinta, tana sauke numfashi kamar wacce ta yi gudu don tuna baƙar wahalar da tasha ɗazun.
Murmushi Suwaid ya yi yana sosa kai ya ce " yi haƙuri babyna "
Shashak'ar kukanta da ya ji ne yai sanadin ƙatsewan zance ta ya ce cikin sigar rarrashi "
Subhanallah baby ya haka kuma?, don Allah ki bar kuka wallahi kukanki na sanya ni jin wani raɗadin cikin zuciyata, sai naji kamar zuciyata zata hudo waje, ki taimaka ki bar kukan nan ko zan samu sassauci.. " ya ƙarasa zance yana nufota zai sake rungumar ta, ta ce cikin " kar ka taɓani, nidai ka maidani gida... " ta fashe da matsanancin kuka tana mai dana sanin biyoshin da ta yi." Babu fa abinda zan maki, rarrashi ki nake so na yi amma tunda baki so na bari, ɗauki jakar ki muje na maida ki gida" Suwaid ya ce, makullin motarsa dake ajiye a kan fridge ya ɗauka sannan ya fita daga a ɗakin Luba na biye dashi a baya riƙe da jakar makarantar ta.
________________________________________________________________________
Ammi kuwa har police station suka kai cigiyar Luba amma har yanzu shiru babu amo babu labari. Haka Yusrah ta dawo daga makaranta ta cimma Ammi zaune a falo ta yi nisa cikin tunani hawaye na bin fuskarta bata ma san sanda Yusrah ta shigo ba. Wuri Yusrah ta samu ta zauna kusa da Ammi sannan ta kwanta kan cinyarta, firgigit Ammi ta yi jin mutum a cinyarta. Dagowa Yusrah ta yi ganin Ammi ta firgita ta ce " Ammi lafiya?".
" Lafiya kalau Yusrah, yaushe kika shigo?".
Turo baki Yusrah ta yi cike da shagwab'a ta ce " tun ɗazu na shigo ina ta sallama baki amsa min ba ina kuma nagan ki nata hawaye, shine nace bari na kwanta kan cinyar ki wata k'il ki farga. Ammi don Allah me ya sameki kika zauna ke d'aya a falo kina kuka?" Yusrah ta ƙarasa zance cikin sanyin murya kamar itama zata yi kuka.
" Yusrah, Luba ce, wallahi Luba ce... " shiru Ammi ta yi ganin kuka nason cin ƙarfin ta.
Tashi Yusrah ta yi daga kwance da take, bugun zuciyarta ya tsananta ta ce " Ammi meye ya sameta?, ko dai mutuwa ta yi?, Ammi don Allah ki faɗa min abunda ya sameta.. " ta ƙarasa zance cikin rawan murya kamar wacce zata yi kuka.
"Ina ma ace ina da amsar wannan tambayoyin, wallahi Yusrah bansan abinda ya sameta ba" labarin abinda ya faru Ammi ta bata tun zuwan driver ɗaukan ta a makaranta har zuwa yanzu da ba'a ganta ba, sannan ta ce " Yusrah me mutane zasu ce?. Wasu fa cewa za su yi ina musguna mata ne shi yasa ta gudu, wasu kuma cewa zasu yi kila wani gurin na turata, barin ma Baba wallahi ba zata taɓa yarda cewa b'ata ta yi ba, cewa zata yi me saya ke baki ɓata ba, sai Luba. Kaicona! Ni nagan illar riƙo kullum Luba cikin ja min magana take."
"Ammi ki kwantar da hankalin ki In Shaa Allahu za'a ganta" Yusrah ta ce tana mai kwantar wa Ammi hankali.
________________________________________________________________________
Tuki yake hankalinsa kwance. Sai satar kallonta yake yana lashe baki a zuciyarsa ya ce " gaskiya bai kamata na kyale wannan yarinyar haka sai naci moriyanta, amma bari zan dai ɗan ɗaga mata ƙafa."
A ɓangaren Luba kuwa tunani ƙaryan da zata yiwa Ammi take wanda ba zata zargeta ba, murmushi ta yi ganin ta samu ta fita. Wanda ya yi daidai da tsayuwar mota ƙofar gidansu. Juyawa gefenta Suwaid ya yi da nufin faɗa mata sun iso ko, gani ya yi tana murmushi ya ce " yanzu Lubna har murna kike zaki tafi ki barni, anya kina so... " bata jira ya ƙarasa maganarsa ba ta ɓalla marfin motar ta fita sabida tasan in baka haka ta yi zai iya bata mata plan. Murmushi ya yi don ya gane nufin ta sannan yaje motarsa ya tafi.
Bakin gate din gidansu ta ƙarasa, ta riƙe ciki kuka ta fara yi tare da daga murya yanda mai-gadi zai jita sannan ta fara ƙwankosa ƙofar gate ɗin, da sauri Baba Habu ya ƙaraso gun, buɗe ƙofar ɗan yi, da sauri ƙarasa buɗe kofar ganin Luban da ya yi tsugune riƙe da ciki sai rusa kuka take, da sauri ya fita ya taimaka ya shigo da ita sannan ya koma ya rufe kofar. Taimaka mata ya yi har cikin falon, zaune Ammi take kan sallaya ta yi tagumi, Yusrah na gafenta tana bata baki.
*Mummy's friend ce🤩*

ESTÁS LEYENDO
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Historia CortaEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.