*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIƘO*
_*('Yar riƙo)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*Dedicated to all my fans*
_*Be happy not because everything is good, but because you can see good in everything.💃🏼💃🏼💃🏼Happy me.*_
_*Ban manta ki Fatima Ahmad, ina matuƙar godiya ga yanda kike nuna soyayyarki ga littafin nan, kece ta ɗaya a jerin fans ɗina. Ina yinki irin sosai ɗin nan😍😘.*_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_Manzo S.A.W ya ce: Duk wanda yabar sallar la'asar haƙika ya ɓata ayyukansa._
_*Page 14*_
"Kuluwa yanzu ni kika sa Luba ta yi wa rashin kunya?" Baba ta faɗa cike da mamakin abinda Luba ta yi.
"Don Allah kiyi haƙuri Baba wallahi…"
"Dalla rufe mani baki, sai kace bake bace a nan kuke ta tirjewa ke da Ahmad ba ku son riƙon baz oho yanzu na gane nufinki watoh shi yasa kika koya mata rashin kunya don ki muna min *ILLAR RIK'O* ko?. Toh baki isa, ba rashin kunya zaki koya mata ba wallahi ko sata zaki koya mata ku zaku riƙe…"
"Wallahi daidai da rana ɗaya Ammi bata taɓa koyan rashin kunya ba, ai da hankalina kums duk abinda ke faruwa akan ido na ya ke faruwa, don kullum idan kinzo gidan nan haka za ki sa Ammi gaba kina mata faɗa koda kuwa muna gun zaune, shi yasa nima yau na ce sai na rama mata" cewan Luba wacce ta katsewa Baba zance da take.
"Innalillahi...! Luba in kina yiwa Allah kiyi shiru" Amma ta ce cikin ruwan murya, juyawa ta yi gun da Bana take tsaye ta ce " Baba don Allah kiyi haƙuri".
"Yo ai dole ki ban haƙuri tunda kinsa ta yi min rashin kunya, Allah ya dawo da Ahmad zai zo ya sameni domin da na baku riƙo bance ku koya mata rashin kunya da fitsara ba, ai wannan idan ta je gida zata yiwa uwarta ma rashin kunya tunda ta iya min " cewan Baba wacce daga jin maganar zaka tabbatar ranta ɓace yake.
Yusrah dai na gefe tunda tayi gaisuwa bata kuma cewa komai, a gefe ɗaya na zuciyarta kuwa murna take na gani Luba na kwatarwa Ammin su 'yancinta, yayin da dashi guda na zuciyarta na ganin rashin dacewar hakan.
Haƙuri Kuluwa ta sake bawa Baba kannan daga bisani ta kira Luba ɗakinta, faɗa Ammi tayi wa Luba haɗi da nuna mata rashin dacewar abinda ta yi daga ƙarshe ta haɗa da cewa " Babba komai rashin gaskiyarsa ba'a ba zaki tsaya yana faɗa kina faɗa ba, don Allah kar ki sake maimaita haka kin ji?".
Gyada kai Luba tayi alamar eh.
"Yauwa ɗiyata Allah yayi ma ku albarka".
" Ameen Ammi " Luba da Yusrah suka faɗa a tare.
Su Ammi basu jima da shiga ɗaki ba sai ga Abba ya shigo da sallamar cike fara'a, turus ya tsaya ganin Baba hakimce akan cushion, ras yaji gabansa faɗi a zuciyarsa faɗi yake " ko da me Baba tazo yau?, Allah dai yasa lafiya", cikin falon ya ƙaraso ya isa dab da ita ya risina har ƙasa ya gaida ita cike da ladabi da nuna farin cikin zuwa ta.
Amsa maishi ta yi sannan ta ce " gwamma da ka dawo yanzu, dama kai nake zaman jira".
Murmushi ya yi ya ce " toh baba, wai yana ganki ke ɗaya ne, mutune gidan basu san da zuwan ki bane suka barki ki nan zaune?"
" Yo tunda matar gidan bata ganin mutuncina ina zaka gansu zaune, wallahi Ahmadu kuluwa bata sona jifa tun ɗazu nake nan zaune amma ko ruwa bata bani ba, sai ma Luban da ta saka ta min rashin kunya sabida ta nuna min iyakata" Baba ta ce haɗa fashewa da kuka.
Ganin Baba har da kuka ta yi abin ya sosa zuciyar Ahmad, kusa da ita ya matso sannan ya ce " Baba don Allah kiyi haƙuri, In Shaa Allah hakan ba zata sake faruwa ba" yana gama faɗin haka ya kwala wa Ammi kira. Da sauri Ammi ta iso don amsa kiransa nasa sabida daga yanayi kiran ta tabbatar ransa a ɓace yake.
"Sannu da zuwa Abban Yusrah ya aiki?" Ammi ta ce bayan ta ƙaraso falon.
" Lafiya " ya bata amsa a takaice. Tashi ta yi da nufin kawo masa ruwan sha ya dakatar da ita da faɗin " zauna magana nake son muyi", komawa ta yi ta zauna sannan ya fara magana ya ce " wai meyasa kike wulak'anta min mahaifiya,kullum idan tazo sai kin mata rashin mutunci wannan bai isheki ba shine sai kinsa 'yar da kike riƙo ta mata rashin kunya?, toh wallahi bazan yarda da irin haka" fad'a sosai Ahmad yake mata ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kamar ya sami ƴar shi.
Mamaki ne ya kashe Ammi sabida ganin yadda Ahmad ke mata faɗa kamar wata ƴar yarinya, magana ta fara yi cikin sanyi murya, muryata har rawa yake ta ce" Baba don Allah kiyi haƙuri , Allah shaida na daidai da rana ɗaya ban taɓa zama da Luba na ce tayi maki rashin kunya ba domin ni kallon 'yar cikina nake mata." Shiru ta yi na wasu dakika sannan ta ci gaba " Abban Yusrah kai a ganin ka zan iya sa Yusrah tayi wa Baba rashin kunya?, toh idan har ba zan iya saka Yusrah ta yi mata rashin kunya ba haka Luba ma bazan iya saka ta yi mata eas5hin kunya. Baba Allah ya gani na ɗauki ne a matsayin uwar da ta haifeni kuma ni ban san abinda na maki ba amma ina roƙon ki don girman Allah idan nayi maki laifi ki yafe…" k'asa ƙarasa zance tayi sakamakon kukan da yaci ƙarfinta, tashi tayi ta nufa ɗakin tana mai bakin cikin rashin dacen uwar miji da tayi.
Baba kuwa faɗin irin murna da farin cikin da take ciki bata misaltuwa, ji take kamar ta tashi ta taka rawa.
Abba kam jikin shi ya yi sanyi matuƙa ganin duk irin haykurin Ammi sai da ya sanyata kuka. Juyowa ya yi ya ga Baba ya ce " don Allah kiyi haƙuri. "
Hannu ta sa tana goge hawaye da suka fara bushewa kan fuskarta sannan ta ce " babu komai Ahmadu nayi tunda akan idona ka nuna min girmata, amma ina son idan zan koma gida mu tafi tare da Luba in yaso sai tayi koda kwana biyu ne tunda ka gan yanzu kusan shekara biyu kenan tayi bata je ba".
" Toh Baba daman ranar laraba zasu yi hutun mid-term in yaso sai ku tafi bayanta dawo daga makaranta, ko ya kika gani?"
" Hakan ma da kace yayi, Allah ya maka albarka" cewan Baba
" Ameen Baba, bari na je na watsa ruwa a jiki wallahi yau a gajiye nake" Abba ya ce sannan ya tashi ya wuce ɗaki.
。。。。。。。
Inna ce zaune ta kurawa Bintu ido tana son gano matsalar ta don ita gaskiya bata yarda da zance da Bintu ta faɗa mata ba tana ji a jikinta da abinda take ɓoye mata.
" Inna wannan kallon haka sai kace baki saba ganina ba" cewan Bintu.
"Hmm Bintu kenan ai dole na kalleki domin kin sauya daga Bintun da na sani, kin tabbatar babu abinda Jameela take maki?" Inna ta ƙara jefo mata tambaya.
"Kai Inna!ni babu abinda take min,ai da tana min wani abu da kin ganewa idonki ".
"Toh ya na iya tunda kince haka, kodai zaki bani ki ɗan yi kwana biyu?" Inna ta ce tana kafe ta da ido.
" Tab! toh nayi ya da makaranta, nidai ba zani ba sai mun yi hutun school".
"Ja'ira kawai, idan kika yi tsiya wallahi tare zamu tafi dake" Inna ta ce tana hararanta.
"Haba Inna ai kin san bamu haka dake " Bintu ta ce sannan ta kwanto cinyar Inna ta ci gaba da maganar ta ta ce " Innata nayi kewarki sosai musan ma wannan cinyoyinki."
Murmushi Inna tayi tana shafa kan Bintu har bacci ya ɗauke ta. Inna na jin tayi shiru ta leka fuskarta ta gan har Bintu ta yi bacci ko, kwanciya ta gyarata mata, sannan ta tofeta addu'a.
_*Mummy's Friend ce🤩*_

YOU ARE READING
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Short StoryEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.