*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIKO*
_*('Yar riko)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com_*Dedicated to all my fans*_
_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
_*Page 32*_
Ras Luba taji gabanta ya faɗi.
" Ya naji shiru, ke nake saurare" cewan Inna jin shirun tai yawa.
" Em-umm dama, um-em.." Luba ta ce cikin i-ina.
" Ke kema dai bana son shashanci, ki buɗe baki ki min magana kuma ki faɗa gaskiya don nasan yanda zan bulluwa lamarin."
Koro zance Luba ta fara yi tun daga kan abinda ya haɗa su da Suwaid har yanda ta maida abin kan Abba, kawo ga maidota gida da su Jabir ya yi.
Bisa ga mamakin ta taji Inna Gaje ta ce " ai kin burge ni, duk ban so wannan sakacin da kai ba, wa ya ce maki ana sakarwa saurayi jiki, Allah dai yaso kina da wayo da ya kai ya baro. Ai dama wannan ɗan nasu kika ce, me ma sunan? "
"Wai kina nufin Ya Jabir?"
" Wannan dai miskilin, wanda kwanaki na zama likita nake nufi. Kiga da shine da kin huta, ga kuɗi, ga kyau, ga kuma kuruciya."
"Hmm! Ke dai bari Inna wallahi ina nima shi naso, amma tsoro da kwarjinin shi yasa na ƙasa. Karki so ki ga yanda ya min ranar kamar zai makeni, tun daga sannan yake jin haushina" Luba ta ƙarasa zance tana kwaɓe fuska.
" Toh ke meye naki na damuwa? Manta dashi kawai, ba dai kince Bilki ta yi na'am da lamarin ba?"
Gyaɗa kai Luba ta yi alamar eh.
"Toh meye naki na damuwa, ke dai ki kwantar da hankalin ki kuma ki bar wannan maganar a iya mu kawai. Karki kuskura ki faɗawa kowa abinda ya faru, kina jina? "
Nan ma kai Luba ta sake gyaɗa mata.
Ɗora hiran su Ammi ta yi har Luba tana ganin kamar bata mata adalci ba saboda kirkinta, da yanda ta riƙe da amana. Ai nan take Inna Gaje ta hure mata kunne da nuna mata kanta kawai yakamata ta riƙa tunani babu ruwan ta da kowa. Haka dai taita hure mata kunne har Luba ji zata iya yin komai don ta mallaki Abba su samu su raji rabon su. Haka dai suka ci gaba da hira can Luba ta tashi taje ta kwanta don ta huta.
**************
Ɓangaren su Jabir kuma haka suka koma gida zuciyoyinsu cike da kewan Bintu, fatan su Allah yasa haka ya zame masu alkhairi baki ɗaya.
*BAYAN KWANA BIYU*
Maganar dawowar Luba ya karaɗe ko'ina kasancewar shi ƙauye, a bakinsu mutanan gari Talatu mahaifiyar Luba ke jin dawowan ta don ta kwana biyu bata je gidan nasu ba saboda zazzaɓin da take fama dashi. Haka ne yasa yau ta shirya ta fi gidan nasu don jikin nata da dama.
kan Talatu ta kai gidansu nasu nuna ta ake ta yi, da ƙaƙanun maganganu da suka dawo kunnenta akan Luba yasa tana ta Allah- Allah ta je ta ganewa idonta Luba. Da sallama da shigo gidansu inda ta samu zaune gindin murhu tana sanwa, dukuwa har ƙasa Talatu ta yi ta gaida mahaifiyar ta sannan ta ansa ta ƙarasa mata, kwashewa abinci tai cikin kula takai ɗaki inda ta sami Luba kwance tana game. Ajiye abinci ta yi sannan ta ce " sannu 'yan birni"

BINABASA MO ANG
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Short StoryEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.