*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIƘO*
_*('Yar riƙo)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*Dedicated to all my fans*
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_Aikata alkhairi komin ƙanƙancinta wataran zai maka rana. Allah ka bamu ikon aikata alkhairi 🙏🙏🙏( Ameen)._
_Never lose hope and trust in the power of Dua, Allah will grant you everything you want as long as it’s good for you._
*Page 26*
Ɗakin Jabir ya dawo riƙe da akwatin kamar first aid box a hannunsa wuri ya nema ya ajiye box ɗin gefen gadon, sannan ya ciro allurai da ya haɗa, kusa da Bintu ya ƙaraso wacce take kwance har yanzu a kan cinyar Ammi kamar yanda ya barta sai kuka take " ke dalla rufewa mutane baki " ya faɗa cikin daka tsawa, ai ba shiri sai ga Bintu ta tsuke baki ta yi shiru, ba zaka ce wacce ake ta faman rarrashi bane tun ɗazu ta k'i shiru ba.
"Miƙe tsaye " ya ce in a commanding tune, ai da sauri ta miƙe ta zauna jikin ta har rawa yake, sai a sannan Ammi ta yi magana ganin irin yadda jikin Bintu yake rawa, ta ce " Ya haka,? ai sai ka kara rikita ta, kai da zaka bita a hankali, haba mana."
"Yi haƙuri Ammi" ya ce sannan ya juya ga Bintu wacce ke zaune, ya ce "tashi zaki yi daga tsaye ,ko kin taba ganin inda aka taɓa yin allura a zauna?"
Zaro ido ta yi waje jin an anbaci allura, (😂 wa yagan tawan sarki tsoro, ga ƙawa nai maki 😜), juyawa ta yi ƙurawa Ammi, narai-narai tai idanuwanta kamar wacce zata yi kuka ta ce cikin sanyin murya " nidai bana son allura, nama fa ji sauƙi fa."
Murmushi Ammi ta yi sannan ta ce " Yanzu fa kike ta faman kuka har da su birgima, ki je kawai ya yi maki hannunsa babu zafi, kin ji Bintu na," Ammi ta ƙarasa zance cikin sigar rarrashi.
Cike da shagwab'a har da hawaye Bintu wacce takewa Ammi kallon Innarta ta ce " ni wallahi na ji sauƙi fa, dama ciki ne yake min ciwo ɗazu, amma yanzu ya daina ciwo," ta ƙarasa maganar tana sharan kwalla.
"Nifa ina da wurin zuwa, gara ki zo ki ƙarbi alluranki tun wuri, don wallahi bara ki sani asaran su ba," Jabir ya faɗa cikin ɗaure fuska.
Ƙin zuwa ta yi, ta yi tsaye bayan Ammi sai faman sharan kwalla take, tana yi tana yarfa hannunta kamar wacce aka ce za'a yanka. Ganin haka Ammi ta ce " rabu da ita kawai tunda bata so, ga dukkan alama ta ɗan ji sauƙin ciwon ko."
"Haka dai ta ce, amma nasan ƙarya take, salon da daddare tazo ta hana mutane barci" ya faɗa yana kallonta da wutsiyar ido, " Menstrual pain ne ki ne ke damunki?" Ya kuma jefanta tambaya.
" A'a, bashi bane " ta bashi ta amsa a takaice.
" Ok, Ammi please ku bamu wuri don na tabbata sabida ganin idonki yasa take wannan shirmen" Ya Jabir ya ce ganin tana ɓata masa lokaci.
Murmushi Ammi ta yi taja hannun Yusrah dake faman dariya ganin dramar da Bintu take yi, " please banda mugunta, kaji?" Cewan Ammi
"In Shaa Allah Ammi, trust me" cewan Jabir yana murmushin yaƙe.
"I do dear" Ammi ta faɗa sannan suka nufi hanyar fita, kan su kai bakin kofa har Bintu ta rigasu ko, kafa tasa zata fice daga ɗakin kenan, taja ta tsaya cak sakamokon murya ya Jabir da ta ji yana faɗi cikin daka tsaya " ina kike tunanin tafiya?"

ESTÁS LEYENDO
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Historia CortaEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.