4

173 6 0
                                    

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIKO*
     _*('Yar riko)*_

            *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*Dedicated to all my fans*_

_*My namcy Aeshat Aliyu nagode da kauna da kulawar da kike nuna min. Ina yinki irin sosai dinna. Kiyi komai ba komai mummy's friend taku ce.*_

_*I dedicate this whole page to you Aishat Aliyu ( ILLAR RIKO FANS GROUP). Kiyi yanda kike so dashi.*_

_*Afuwan dudes jiya nayi mistake a gun numbering, na sake page 4 instead of 3, toh yanzu dai wannan shine page 4 so don't be confused zaku ga page 4 ya zama biyu._

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*Page 4*_

_*BAYAN SATI ƊAYA*_

Yusrah ce zaune a balcony kan kujeran tsuguno, Luba na tayata tsifa sai hira suke Luba na bawa Yusrah labarin kakkararsu. Yusrah sai dariya take duk wanda ya gansu a wannan yanayin sai rantse ya da kanwa ne.

" Yusrah! Yusrah!!......." Ammi ke kwalawa Yusrah kira daga nisa kan ta iso inda suke zaune.

Tana isa gun ta ce " wai har yanzu baku gama tsifan ba, wani lokaci zaki kitson kenan?"

" Yanzu zan tafi Ammi kalban bai fi saura huɗu da zan tsefe ba " Yusrah ta bata amsa.

" Toh maza kuyi sauri ku tsefe kin dai san yanda gun kitso yake da layi ranar lahadi. Luba da fatan kema kin yi tsifan ko?."

" Eh na tsefe " Luba tabawa Ammi amsa.

" Maza ku tsefe in yaso sai ku tafi tare domin kema gobe In Shaa Allah zaki fara zuwa makaranta."

" Yehhh " Yusrah ta daka tsale cike da murna " thanks Ammi yanzu zan samu 'yar uwan da zamu dinga tafiya skul tare."

Har kasa Luba ta risina ta mata godiya.

Murmushi Ammi tayi ta ce " tashi abin ki Luba ai matsayin 'ya na ɗauke ki, da ke da Yusrah duk ɗaya kuke a guna. In kun gama tsifan ku sameni a ɗaki."

A tare suka amsa da " toh Ammi."

Ammi na bari wurin Yusrah da Luba suka rungume juna cika da murna. Labarin skul ɗin su Yusrah ta fara bai wa Luba har suka idda tsifan.

Suna idda tsifan ɗakin Ammi suka nufa kamar yadda ta umurce su, zaune suka sameta tana linke kayakin da kwaso daga shanya, da sallama suka shigo suka ƙaraso gun ta " Ammi mun gama" cewan Yusrah.

Yayin da ita kuma Luba ta ɗauki ɗaya daga cikin kayakin zata tayata linkewa.

"A'a barshi abinki, bari na baku kuɗin kitson kuyi tafi" Ammi ta ce tana ajiye kayan dake hannunta, purse ɗinta ta ciro daga sif ta basu dubu ɗaya ta ce " maza ku tafi, don Allah banda tsayawa wasa a hanya, kar wani ya kiraku ku tafi, kuna jina ko?"

Jinjina mata kai suka yi alamar eh, sannan ta ci gaba ta ce " Allah ya tsare mani ku, ya maku albarka."

"Ameen" suka amsa a tare sannan  suka fice daga ɗakin, ɗakinsu suka nufa suka ɗauko hijabi da kayan kitso, sallama suka yi wa Ammi suka tafi kitso.

。。。。。。。。。

Bintu da Rahma ne a bakin famfo suna wanke kwanoni. Rahma na wankewa, ita kuma Bintu na ɗauraya, labarin yanayin garin Rahma ke bawa Bintu. Bintu sai murmushi take tana kwaɗayin fita ta gan yanayin garin domin tun zuwanta ko gate bata sake leƙawa ba.

" Lah..lah..lah...... wallahi sai na gayawa mummy. Ba mummy ta ce mu daina wasa da ruwa ba, ke kin zo nan kina ta wasa da ruwa."

" Toh sannu uwar gulma, faɗa min wani wasa da ruwa nayi?, ko ba wanke-wanke kika ga ina taya Bintu ba?" Rahma ta bawa Ummi amsa.

" Toh wa ya saki tayata?, Wallahi sai na faɗawa mummy " Ummi na gama faɗin haka ta sheƙa a guje tana kwalama Jameela kira " Mummy! Mummy!!......"

Da sauri Jameela dake kitchen tana girki ta fito " lafiya Ummi kike kwala min kira haka."

Ummi ta ce " Mummy anti Rahma ce take wasa da ruwa a bakin famfo, kuma nayi mata magana wai ita tana taya Bintu wanke-wanke ne."

" Iye muje ki nuna min ita, toh har wuyan Bintu yayi ƙwarin da zata ce Rahma ta tayata wanke-wanke?" Mummy ta faɗa cike da masifa.

" Yo Mummy ai Bintu bata da laifi, laifin anti Rahma ne da ta sakar mata fuska."

Kwafa mummy ta yi sannan ta ce " ta kuwa gamu dani, sakarya kawai kamar bani na haifeta ba." Mummy bata bar masifa har suka isa wurin. Kan isar su Bintu ta roki Rahma ta bar wanke-wanke kar mummy ta yi mata faɗa amma fafur ta ƙi yarda. Suna cikin haka Mummy ta iso gun da zuwanta ta riƙo Rahma ta kifa mata mari, cike da fushi ta ce " you are very stupid, ba ce maki nayi karda na ganki wurin sanyi ba, ko so kike sai ciwonki ya tashi?"

" Mummy ki yi haƙuri wallahi ba wasa da ruwa nake ba kwanuka nake taya Bintu wanke wa" Rahma ta faɗa cikin muryan kuka haɗa da dafa kuncinta.

Inda Bintu take tsugune Mummy ta fisgota itama ta kwasheta da mari sannan ta riƙe mata kunne ta ce " wannan ya zame maki na farko kuma ƙarshe da zaki ce Rahma tayaki aiki, wai ke ance maki Rahma sa'arki ce?, toh bari ki ji na faɗa maki wallahi bazan kashe kuɗin na a banza ba, aiki zaki min har sai na fashen kuɗina dama ilimi ba'a samunshi a wasa" tureta ta yi sai ga Bintu ta faɗa cikin kwanukan da take wankewa. Ko ta kanta Mummy bata bi ba ta yi tafiyanta.

Ummi ma bayan Mummy tabi tana yiwa Rahma gwalo.

Suna tafiya Rahma ta ƙaraso inda Bintu take ta miƙar da ita " Bintu don Allah ki yi haƙuri laifina ne,  dana bari kin yi aikin ki ke ɗaya duk wannan bazai sameki ba." Bintu dai ba ta ce komai ba illa kukan da take yi, sannan ta ci gaba da wanke-wanken ta.


_*Taku ce*_

_*Mummy's friend*_

ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon saloWhere stories live. Discover now