47&48

206 11 3
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 47⏩48

*Sannunku da kokari myreal fan's, kuna nuna man kauna wajen karanta wannan buk din gami da yi man comment, sannan kuma shi comment dinku maganar gaskiya yana sani farinciki sosai da Sosai, fatana dai Allah ya bar kauna ta fissabilillah, dan kuwa ina maku son fissabilillah 💜*

*Tom page din yau sai dai ayi hakuri, dan dole a samu winner da kuma loser tsakanin TEAM UKU, da Team din AMINU sai  Team din Nurandeen sannan kuma Team din Dr Umar🌚, Allah yaba mai rabo sa'a kawai nidai zani ce😊*

Numfasawa Nurandeen yayi sannan yaci gaba da cewa. "Haka muka tafi unguwar su Aziza dan samun wanda Allah zai sa yace ya santa dan, dan kuwa addu'a tun ina wanda na sani har sai da yakai da ina yin addu'a kawai amman bansan abunda nike cewa ba tsabar shiga tashin hankali da nayi a ranar, cikin ikon Allah muka isa unguwar majoji nan muka raba ƙafa kowa da hoto a hannunshi muka fara nuna ma mutane ko sun san wannan baiwar Allahr, amman ansa ɗaya a'a bansan sanda kuka ya ida ƙwaceman ba saboda shiga ruɗu da nayi nidai bani ansa gawar Aziza saboda gidanmu ba'a santa , idan n kaita mai zance masu game da ita? Ita ba accident tayi ba balle na kaita gidanmu nace ba'a san danginta ba su taimakaman ayi mata sutura akaita gidanta na gaskiya, amman a hotel ta mutu suna zina, kinga dole mutuwarta tayi suna a faɗin nigeria Khadija, nidai bansan ina nike takawa ba kawai jefa ƙafa nike, sannna duk wanda na gani sai na nuna mashi picture dinta koda kuwa ƙaramin yaro ne wanda baisan kowa ba a unguwar, cikin ikon Allah naga wani matashin saurayi kamar ni koda ya girmeni ba zai wuce ya girmeni da shekara ɗaya ba, amman bada shekara biyu ba, zaune yake bakin wani shago a unguwar ga dukan alamu shagon nashi ne ma, ida zuwa nayi wajen shi na nuna mashi picture din nace ko ya santa, kallona ya tsaya yi sannan yace man ina na samu wannan picture din? Ce mashi nayi gidansu yarinyar ake nema a unguwar nan, dan Allah idan ya sani ya taimaka ya gayaman dan ana son gani iyayenta ne, girgiza kai mutumin yayi sannan yace ai na santa karka damu bari na kulle shagon na kai ka har gidansu, ai bansan sanda na rungume shi ba,na kuma fashewa da sabon kuka, kallona yake yana mamaki sannan yace kukan mai kakeyi ne bawan Allah, girgiza mashi kai nayi sannan nace nidai dan Allah abokina ka kulle shagon ka kaini gidansu kaji komai maiye idan muje, muna cikin magana muka hadu da mutumin da mukazo dashi , kallona yayi sannan yace fatan kai ka dace ka samu wanda ya santa ko? Bansan sanda Murmushi ya kauceman ba, na ɗaga mashi kai ina nuna mashi mai shagon nan, shima zuwa yayi yace mu tafi."


"Nan muka tafi mu dukanmu ba wanda yake  magana, kowa da abunda yake saƙawa a cikin zuciyarshi Khadija, wani babban gida muka iso, dan gida yana da kyau ba laifi tsayawa mukayi bakin gate wannan mutumin ya shiga ciki bai jimaba sai gashi yace mu shigo, tare muka shigo dan harda police muke ni ban ma lura da wasu police ba sai lokacin da zamu shiga cikin gidansu, muna shiga aka kaimu part din baƙi nan muka zauna munyi jiran kusa ten minutes sai ga wannan mai shago ya shigo mana da ruwa da lemu yace kuyi hakuri mun barku zaune, ga Baban nan zuwa yanzun ya dawo baya gida, amman na kira shi waya yama shigo ya shiga part din shi dan ya rage kayan jikinshi, da sauri na ɗago kaina aiko muka haɗa ido biyu da wannan mutumin nan naga yana yar'kama Aziza, sauke kaina nayi kasa ban sake ɗagowa ba, can sai ga Babanta ya shigo da sallama a bakinshi, ansawa mukayi sannan muka bashi hannu aka gaisa, bayan an gama angaisawa aka fiddo picture din Aziza aka nuna mashi aka wannan yarinyar ƴarka ce."?

"Allah sarki ɗaga kai yayi kawai amman baiyi mana magana ba, kuma na lura tunda aka nuna mashi picture din Aziza fuskarshi ta chanza ta tashi daga walwala ta koma rashin walwala, tunda muka lura da yanda yanayin shi ya koma sai muka kasa yi mashi bayanin abunda ya kawo mu, daurewa wannan mutumin yayi sannan yace Alhaji hannunka ba zai ruɓeba ka yanke ka yada, duk abunda Aziza tayi maka ya wuce dan Allah ka yafe mata, dan yanzun ba abunda Aziza take bukata a wajen ku idan ba wannna yafiya ba, sannan kuma addu'a idan har kuka yi mata haka to kun gama mata komai kuma kunyi mata abunda ita ta kasa yi maku, dan Allah Alhaji karkace ba zaka yafema ƴarka ba ƴarka ce ta cikinka komai tayi maka ayi hakuri kar a tuna baya a yafe mata."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 30, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now