3&4 kuyi vote and comment pls

447 17 3
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD
Idan kinsan baki comment karki shigo pls

*wannan page din nakune A SANADIN SOYAYYAR MINTI FAN'S da ZEE-ABU HAUSA NOVEL DA BAN RAINA ALLURA BA FANS kuyi yanda kuke so dashi dan naji dadin comment dinku sosai inason ku cigaba da yi man haka, yana kwaraman kwarin giwwar  yi maku typing sosai da sosai, ina maku son fissabillilah🤗❣️*

Page 3⏩4

"Wallahi mudun ka kuskura ka taɓa Khadija to sai na tsine maka albarka, mutumin banza wanda baya kishin uwarshi."

Cikin kuka Yaya Jamilu ya matsa kusa da Mama yana cewa. "Dan Allah Mama ki man rai kar ki biye ma kizo daga baya kina da na sani karki manta Autarki ce ba kwance cikin wannan halin, kuma hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yada."

Shiru Mama tayi ta share hawaye, tsaki tayi ta bar mashi parlourn dan mudun ta tsaya cikin parlourn tsab zata tsine ma Jamilu, haka itama Aisha tabi bayan Mama, kallona Yaya Jamilu yayi sannan ya ida isowa wajena ya daukeni cikin sauri ya fita dani ya sani cikin motor dinshi sannan muka dauki hanyar asibiti, sosai yake ba motarshi wuta ikon Allah ne kawai ya kaimu dan gudu yake ba na wasa ba, muna zuwa ya ruga ya kira nurse suka turo bisa keken mararsa lafiya, haka aka turani rai hannu ga Allah, direct emergency room aka wuce dani, tsayawa Yaya Jamilu yayi baki emergency din yanata safa da marwa.

Niko tunda aka shiga dani likito suka dufuha kaina dan cito raina da abunda ke cikin cikina dan jini nike zubdawa bana wasa ba, sun kusa awa uku suna abu guda sannan suka samu suka tsada jinin, allurai sukayi man sannan suka kaine dakin hutu, fitowa likitan yayi yace ma Yaya Jamilu. "Alhaji Jamilu ina son ganinka a office dina." cikin damuwa Yaya Jamilu yace mashi. "Allah yayi mata cikawa ko."!?  Kallon shi kawai likita yayi sannan yace."komai dai mainene meet me in my office." gwaɗa mashi kai kawai Yaya yayi sannan suka tafi office dinshi, duba da yanayin da yake ciki yasa likita ya bashi ruwa mai sanyi yasha sannan ya fara magana yana cewa. "Alhaji sai dai ayi hakuri, dan muso mu cito cikin da ke jikinta, amman Allah ya kaddara sai ya zube sakamon faduwar datayi har cikin ya bugu, sannan magana ta biyu sai anyi mata wankin ciki kuma mahaifarta bata kwari bai zama dole ta sake daukar wani cikin ba inba wani ikon Allah ba, hakuri zakayi haka Allah ya kaddara sannan zaka sa hannu domin zuwa gobe idan Allah ya kaimu ayi mata wanke cikin idan Allah ya kaimu."

Cikin tashin hankali Yaya yace. "Innalillahi wa'inna'alaihijirun, abokina kaidai kasan komai Auta bata taba aure ba, kaddara ce ta hau kanta wanda ba mai tsalake kaddara idan Allah ya kawota, ba wani abu da za'ayi mata wanda ba sai anyi mata wannan wankin ba, dan da matsala ace za'ayi ma budurwa wanki ciki ka duba dan Allah."

Kallon shi Doctor yayi cikin tausayi dan yasan abokinshi yana cikin damuwa balle yasan yanda suke son autar tasu, cewa yayi. "Wallahi Abokina babu wata hanya idan ba wannan ba, da ace anyi hakuri an raini cikin ta haifeshi da lafiya lau, dan kaddara ce kuwa, wannan yana cikin kudin kaddarar Khadija, amman garin ya hakan ta faru har Mama ta bari ta faɗi har haka."?  Cikin takaici da bakin ciki Yaya Jamilu yace. "Ai daman abunda Mama take so kenan, cikin nan ya zube, taddawa nayi ita da Aisha sun mata dan'banzar duka, dakyal na samu ta barni na kawota asibiti, amman ka bani lokaci naje na gaya ma Mama halin da ake ciki komai kenan sai ka jini."

Kasa cewa komai Dr Dikko yayi, dan baiyi tsanmanin jin haka daga wajen Mama ba, cewa yayi. "To shikenan ka dawo lafiya, sannan ka dawo da wanda zata kulla da ita mutun daya, kasan dokar asibitin nan ba'a kwana amman tunda gidane mutun daya zai kwana, fatanmu Allah ya bata lafiya."

"Amin ya Allah." cewar Yaya Jamilu sannan ya fita, sai da ya fara biyawa gidanshi ya gayama matarshi halin da ake ciki sannan yace ta shirya ma Dija babbar diyarshi wanda muke sa'a daya da ita yace ta tafi dan kula dani shi kuma zaije gida suyi magana da Mama, haka aka aiko man da Dija shi kuma ya wuce gida wajen Mama.

Koda ya shiga sallama yayi ya tadda parlourn ba kowa wuce wa yayi ciki na ya tadda yaiyaina mata guda hudu duk sunzo dan an gaya masu abunda ke faruwa, sai hakuri suke ba Mama dan Yaya Aisha tunda taga halin da Yaya Jamilu ya fidda ni tayi da nasanin bugana da tayi, dan kuwa Mama bataji komai ba Yaya Fatima ce tace. "Mama ya kamata ki sama ranki hakuri, mu dauki kaddara wanann abu jarartace ya kama mun zamo masu cikon imani, ke kuma Aisha kin bani mamaki wallahi bai kama ki biye ma Mama ku bigi Auta ba, ya kamata ace kin ba Mama hakuri ba ki tayata wannan mumanan aika aika ba." cikin jimami Yaya Amina tace. "Ni ko wani hali Auta take ciki amman dan Allah Mama kiyi hakuri." ita dai Yaya Khausar bata ce komai ba, dan abun duniya yayi mata yawa so take taji muna wani asibiti domin taga lafiya ta, shigowar Yaya yasa duk suka miƙe suna tambayar shi halin da nike ciki, samun waje yayi ya zauna ya nemo jarumta ya sama kanshi, sannan ya gaya masu halin da ake, ai take suka fara koke koke, dan Yaya Aisha tafi su dan kuka take tana nadamar buguna da tayi abun Mamaki ba abunda Mama tace inba kallonsu da take ba, hawaye ne kawai suke zuba bisa idonta, kallonta Yaya sannna yace. "Mama baki ce komai ba kinji halin da ake ciki Auta tana buƙatar taimako."

Tashi Mama tayi zata bar dakin, Yaya Fatima ta riko ta tana cewa. "Mama dan Allah ya kamata ki yafema Khadija, ki anshi kaddarar da tazo mana tana bukatar taimako."

Zaunawa Mama tayi sannan tace. "Bintu mai zance? Aje ayi Allah yasa a gama lafiya." Tana gama fadin haka ta tashi ai take Mama ta wanke jiki ta fadi kasa tana amain jini, da gudu sukayi kanta suna kiran suna ta.

Daukarta Yaya yayi suka wuce asibiti, gado aka bata sannan aka sama mata drip dan temper dinta ce ta hau sannan Yaya ya cike takadar da za'ayi man aiki, sai wajen mangrid Mama ta farko haka ta matsa aka sallamaita ni kuma aka barni da Dija, duk da nima na farko amman ba sosai nike yin magana ba.

Washe gari da safe Doctor ya shigo ya duba jikina, hana bani komai yayi yace 10am za'a shiga dani ayi man wankin ciki, sanann ya tafi wajen 9 na safe Yaiyane duk sunzo sun cika asibitin suna duba lafiya, goma nayi aka zo tafiya dani za'a yi man aiki haka na bar yan'uwana suna kuka, dan bansan wani hali nike ba nidai naga suna kuka.


Wajen Mama kuwa tunda ta koma gida take kuka, dan tanajin ciwon abunda ya faru dani sosai, dan ma anbar mata Yaya Amina a gida ita ta kama kwantar mata da hankali tana gaya mata maganganu masu dadi wanda zai sa taji sanyi a zuciyar ta.

Kallon Yaya Amina tayi sannan tace. "Amina bakisan abunda nike ji ba shiyasa, amman na yafema Khadija Allah yasa ta dauki darasin duniya, daman ita duniya haka take tafi bagaruwa jifa, na yafe mata Allah yasa iyakar kaddararta kenan kinga ta biye ma san zuciya ta lalata rayuwar ta a banza."

Haka aka kirasu waya aka gaya mata anshiga dani dan yi man aiki, tayi man fatan fitowa lafiya.

*Allah Sarki, rayuwar Khadija da ban tausayi sosai wallahi nan bakuji komai ba😭, nima lokacin da take gaya man nayi kuka har na godema Allah, fatan dai Allah ya kara tsaremana imanin mu Amin, ya karemu da aikata aikin da na sani*

Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now