39&40

161 3 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 39⏩40

"Ni banga amfanin kukan naki ba Dejja, zakiyi ciwon kai ne a banza a wofi kuma kinsan banson abunda zai samaiki ko ya yake a rayuwa." Murmushi tayi tana goge hawaye  sannan tace "baki son abunda zai samaini ko Aunty Auta? Sannan kuma baki san kiga ɓacin rai na ko Aunty Auta."? Nima Murmushin nayi sannann na ɗaga mata kai alamun eh, bata ce komai ba har muka iso hostel, muka biya mai naped kudinshi sannna muka shiga ciki, bayan mun gama ajiye kaya na tashi na shiga wanka ina fitowa itama ta shiga wankan bayan mun gama shiryawa tazo ta zauna kusa dani, kallona tayi sannan naji ta dafani tace "da gaske Aunty Auta baki san kiganni cikin ɓacin rai? Sannan kuma baki san damuwa ta ko ya take."? 

Tsayawa nayi ina kallonta sosai, dan ta bani mamaki ai nasa mungama wanann maganar kuma, dan nasan dai maganar gizo bata wuce ta ƙoki inji hausawa, Murmushi nayi sannan nace "Dejja kenan, a shirye nike na sadaukar da farincikina saboda naga ke kina cikin farinciki Dejja, sannan kuma ko ɗaya bani son naganki cikin damuwa hakan ya kan sa nima na shigeta Dejja, Dejja keɗin ɗiyatace kuma ƙawata ce ke sannan kuma aminiyata wanda banda kamarta, keɗin haske ce mai haskaka sararin samaniya keɗin kin wuce komai da kike tunanin zan faɗi Dejja kina taka rawar gani a rayuwata kina kula da duk wani al'amarina taya za'ayi ace ni kuma naso naganki cikin damuwa ko kuma ɓacin rai? Ko ɗaya bani fatan hakan ke ni Dejja kullun addu'a nike Allah yasa na rigaki mutuwa ba ki ragani ba, dan ban iya jure rashinki yar'uwata."

Murmushi tayi tana share hawaye sannan tace. "Tabbas hakane Aunty Auta, amman ina da saurin alfarma a wajenki kuwa."?  Kama hannunwata nayi ina murzawa sannan nace. "Kece ko keda alfarma a wajena, ki nemi ko wace irin alfarma ce ni kuma zanyi maki idan har bata fi karfi na ba Dejja." itama ƙara kama hannuna tayi sannan tace. "Alfarmar ɗaya ce Auntyna ina son dan Allah ki fidda wannan mumunan kudirin a zuciyarki na kashe Nurandeen, ba ruwanki da shi ki maida hankalin ki wajen karatu sannan kuma ki maida hankalinki wajen masoyanki guda biyu uncle Aminu da Dr Umar sannan kuma ki maida al'amarinki wajen Allah ina ganin hakan zaifi da ki tsaya cewa zaki kashe wani Nurandeen ɗin banza."

Miƙewa tsaye nayi zan barmata ɗakin, dan banyi tunanin abunda Dejja zata tambayeni kenan ba, ji nayi ta kamo hannuna tana cewa. "Daman nasan banda wata alfarma a wajenki Aunty Auta, amman bakomai hakan ma nagode dan hakan ya nuna man matsayina a wajenki sosai, ina ma rayuwarki fatan alkhairi."

Murmushi nayi mai ciwo sannan nace. "Naji na dauki alkwari ba zan kashe shi ba, shikenan ko Dejja."? Na faɗi ina goge mata hawayen fuskarta Murmushi itama tayi sannan ta rungumeni tana cewa. "Eh shikenan Aunty Auta, Allah ya barni da ƙanwar Babana." lakutar mata hanci nayi sannan nace. "Allah ba zai bar maki ki ni ba Auta, mutuwa dole ce kuma tana bisa wuyan kowa da komai na duniya harta dutse da kuma bishiyoyi." Murmushi kawai tayi sannan tace. "Hakane Allah yasa mu cika da imani kuma muyi kyawkyawan karshe."
"Amin ya Allah."

Zaunawa nayi na dauko handout dina na cigaba da karatun da Dejja ta hanani na ida ta jani kasuwa har nayi baƙin gani, sosai nike karatun kuma inajin dadinshi dan yana shiga sosai ji nayi wayata tana ringing Murmushi nayi dan nasan ba mai kirana indan ba yangidanmu ba ko kuma Aminu, amman ni raina Aminu ya bani ya kirani daukar wayar nayi sai naga bakuwar number, ajiyewa nayi na cigaba da karatuna sake kira akayi naki dauka sai da aka kira kusan sau ukku sannan nayi picking.

Jinayi an sauka wata naunauyar ajiyar zuciya sannan aka ce. "Alhmdulillahi, wallahi bakiji yanda na shiga damuwa ba, da baki dauki wayata ba Khadija." nidai ba muryar Aminu naji ba sauke wayar nayi daga kunnena sannan na kalli wayar na maimaita maganar a zuciyata, maida wayar nayi a kunne ji nayi yana cewa.  "Hello Khadija, baki ce komai ba amman koda yake nasan ba zaki ce komai ba tunda baki san da wa kake magana ba, sunana Dr Umar Garba Ali, Khadija Allah ya jarabaini da ciwon sonki tunda na daura idona a kanki na faɗa tarkon sonki ba tare da nasani ba Khadija, naso na ba zuciyata hakuri ta hakura amman na kasa dole tasa na amayar da abunda ke cikin raina a kanki shine ina sonki kuma ina kaunarki aurenki zanyi."

Zufa ce ta keto man na kasa cewa komai cewa ya sakeyi. "Please Khadija ki sani a cikin jeran masoyinki nima na nuna maki yanda nikejinki a cikin raina wata kila idan da rabo ni sai nayi dace na zamo na ɗaya a cikin su." nidai shiru nayi na kasa magana dan bansan abunda zan ce mashi ba, kuma ina mamakin yanda mutun kamar Dr Umar yake gayaman kalaman soyayya har haka mutumin da bai shiga sabgar kowa bai damu da kowa ba, a depertment kowa tsoranshi yake dan yanda yake ba wasa gareshi ba, amman shi yake man wannan kalamai tsunkulin kaina nayi naji zafi nan na tabbatar da idona biyu ba mafarki nike ba katsaman tunani yayi wajen cewa. "Kinyi shiru bakice komai ba Khadija."

"Khadija." ya kira sunana a sanyaye kamar mai jin bacci, cikin in-ena nace. "Na..am Dr." sake sauke wata ajiyar zuciya yayi sannan yace. "Ina saurarenki matata." kirjina ya buga sosai da naji ya kirani da matarshi, dan ni yanzun saurin tsorata gareni kuma ina tsoran dadin bakin namiji, daurewa nayi sannan nace. "Daman ni tsakani da Allah Dr ni b... "Karki damu da abunda ya faru dake Khadija ni na ɗaukeshi a matsayin kaddara ni Umar ina sonki a haka koda kuwa yaro kika haifa a duniya kuma ba na sunna bane naji na yarda zan aureki a yanda kike." ya ida maganar, bayan ni ba haka naso gaya mashi ba take ya kulleman duk wata hanya da zan bi naga na yaki ceshi a rayuwa nidai ban sake yarda nace mashi komai ba, cewa yayi. "Ina sauraren ansa ɗinki Khadija, amman ki sani ina sonki."

Shiru nayi na wani dan lokaci sanann nace.....


*afuwan jiya banyi maku posting ba, naje ganin doctor kunsan masu asthma wannan lokacin nasune  dan haka kuyi man Addu'a Allah ya bani sauki da duk wani marar lafiya ngd.*

Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now