41&42

163 7 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 41⏩42


Shiru nayi na wani dan lokaci sannan nace. "Dr ina bukatar ka bani dan lokaci nayi tunani gami da shawara please." cewa yayi. "Haba Matata har zuwa wani lokaci zan baki? Kinsan yanda zuciya take azubtaka a kanki kuwa? Kinsan yanda nikeji gami da sonki da ke ɗawainiya da ni Khadija? Khadija wallahi ina sonki sona gaskiya so na tsakani ga Allah, ni idan so samune ki bani dama cikin satin nan ayi bikinmu bcox ilove you more and more, wallahi ina iya rasa numfashina idan na rasaki Khadija dan Allah ki taimaka man ki anshi soyayyata, wallahi zan saki farinciki ba zan taɓa saki kuka ba Matata ya dace ki tausayaman Matata."

Sosai na kasa motsi mai karfi dan maganganun Dr Umar sun shiga jikina sosai,amman sai nayi Murmushi nace. "Naji Dr Umar karka damu, amman duk da haka ka bani lokaci nayi tunani dai."  ji nayi yayi shiru duba wayar nayi naga ya kashe wayar, Murmushi kawai nayi na ajiye nima na cigaba da karatuna hankali kwance Dejja ce ta shigo tana waya, zaunawa tayi kusa dani naji tana cewa. "Haba Uncle Aminu wallahi ka yarda muda komai ba abunda bamu dashi fa." bansan abunda yace mata a bangarenshi ba naga dai ta kalleni sannan tace. "Gata nan zaune tana ta karatu, kuma lafiyarta lau ka kwantar da hankalinka ba abunda ke samunta fa." dariya naga tayi sannan ta miƙa man waya, ma'ana nayi magana da shi, ansa nayi cewa yayi. "Myluv fatan kina lafiya? Wallahi zuciyata ke bani kina cikin damuwa fatan ba abinda yake damunki ko."!? Cikin tsoro yayi tambayar dan duk ya shiga damuwa yanayin maganar kawai ya nunaman haka, Murmushi nayi sannan nace "wallahi ba abunda ke damuna ina cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali." ji nayi ya sauke ajiyar zuciya sannan yace."sure."?  Ɗaga mashi kai nayi kamar yana gani na sannan nace "yes, ya kake kaima."?

Murmushi yayi sannan yace. "Gani nan dai Myluv, kinsan ban taɓa samun natsuwa da kuma jindadi har sai randa na mallakeki ki zama tawa, wallahi Khady jikina yana bani kamar har yanzun baki sona dan Allah Khadija ki daure ki soni ko ya yake koda kwatan yanda nike sonki ne, ni hakan ma yayi mani nasan watarana kema zaki soni kamar yanda nike sonki, kice rayuwata Khadija wallahi rasaki ni nasan a ranar zan bakunci lahira inasonki ina kaunarki inason komai naki, kina burgeni Khadija, nidai fatana da addu'a ta Allah ya bani ke a matsayin mata kuma uwar ƴa'ƴana."

Murmushi nayi sannan nace. "Allah dai ya tabbatar mana da alkhari, amman karka damu nima ai ina sonka kabar sama ranka baka samu karbuwa a wajen Khadija Bello ba, sai dai indan na tuna da wani abu sai naji ban dace da nayi aure ba Aminu, koda ya dace nayi auren bai dace da na aureka ba Aminu, dan na kasa manta abunda nayi maka Aminu na kasa manta kazamar ra... "Enough please Myluv, karki sama ranki damuwa akan haka, wallahi Khadija har abada ba zan taɓa yi maki gori ba, Khadija haka kika zano qaddararki wallahi ba wanda ya isa ya chanza maki qaddara kuma mu dukanmu mu yarda da qaddara fatana dai Allah ya bani ke, sannan dan Allah idan kika dawo ki bani dama ayi maganar aurenmu dan na kosa naganni dake a matsayin mata da miji Myluv."

Murmushi nayi sannan nace. "Allah yasa.".... "Amin ya Allah." nan muka kara gaisawa naba Dejja wayarta sannan na tashi na dauko mana abinci muka fara ci, ji nayi wayata tana ringing dauka nayi sai naga number din Dr Umar ce, ƙin dauka nayi na cigaba da cin abincina, shi kuma bai fasa kira ba, kallona Dejja tayi sannan tace. "Wa yake kiranki haka kuma Aunty."?  Taɓe baki nayi sannan nace. "Dr ne wallahi ." murmushi tayi sannan tace. "Bawan Allah, wallahi shima yana sonki sosai Aunty Auta, karki so kiji yanda Baby yake gayaman son da yake maki, ni kuma naga kinfi dacewa da Uncle Aminu wallahi saboda shi Uncle Aminu baya da mata shi kuwa Dr Umar yana da mata duka duka basuyi two years da aure ba fa, amman ki dauka kiji abunda zaice maki pls."

Dauka nayi kafin nayi magana naji yace. "Matata fito gani nan a bakin gate dinku pls." kallon Dejja nayi sannan nace mashi. "Amman kuma Dr... "Please ineed to see you pls, kuma Seriou magana nike son yi dake Mywife." cewa nayi." ok gani nan zuwa." na kashe wayar, kallona Dejja tayi sannan tace. "Wai zuwa yayi ba tare da ya tambayi izininki ba."? Ɗaga mata kai nayi sannan nace. "Aikuwa kinga muna cikin waya naji yayi rejecting ashe zuwa zaiyi bari na gama cin abincin sai naje ko."? Ɗaga man kai kawai tayi sannan muka cigaba da cin abincinmu muna gama wa na shiga wanka na shirya sannan na tafi wajenshi.

Ina fitowa na kirashi dan naji yana ina, dan bansan motarshi ba balle na tafi wajen, wani waje ya gaya man yana can cikin black mota, gaka naje ina zuwa ya fito da yake wajen ba mutane sosai dan mutanan wajen basu wace ukku ba, shiyasa ya fito dan bai zama dole ace sun sanshi ba, tunda ya fito ya zubaman ido yana kallana sai kace bai sanni ba, dauke kaina kasa nayi sannan nace. "Ina wuni."? Iska ya furzar a bakinshi sannan yace. "Lafiya lau Matata, kinyi kyau sosai kamar na saceki na gudu fa." Murmushi nayi sannan nace. "Ina godiya sosai." shiru mukayi na wani dan lokaci sannan yace. "Na kasa hakuri Khadija, sannan kunnena basu iya daukar maganarki ta waya idan ba kallon idonki nayi ba, nasan nafi fahimta ta haka ma, Khadija inasonki sosai bai kamata ace ba zaki anshi tayin soyayya ta ba har sai kinyi tunani ba, nasa zuciyarki zata baki result a kan soyayyata kuma nasan ta baki ansarce kawai ta gagari a gaya man ita why Khadija."?

Murmushi nayi dan mamaki ma ya bani dan ni zuciya ta bata bani wani result ba akanshi, kallonshi nayi sannan na dauke kai nace. "Dr please kayi hakuri na... ''Nayi hakuri fa kakace Khadija? Kina nufin ban samu waje a zuciyarki ba? Khadija kinsan ko mai ake kira da so? Kinsan irin son da nike maki kuwa Khadija."!? Yayi man questions din cikin wani yanayi dan idanuwanshi cike suke da hawaye gani nayi hawaye sunabin fuskarshi, da sauri na girgiza mashi kai nayi sannann nace.



"Ba haka nike nufi ba Dr, ina nufin da ka daure ka barni dai nayi tunanin sai naga kamar haka zaifi."



Murmushi yayi sannan yace. "Khadija ina jin tsoro, na fahimci baki sona Khadija kuma ni ina sonki Khadija dan Allah ki daure ki aureni koda kuwa baki sona Khadija zanyi hakuri na zauna dake a haka, amman wallahi kika aure wani ba ni ba ina iya mutuwa Khadija, wallahi baki dace da kowa ba sai ni Khadija, please Khadija karki gujeni ki soni dan Allah." ya ida maganar yana hawaye kamar wani karamin yaro, kallonshi nayi sannan nace....


Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now