17&18

232 5 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 17⏩18

"Murmushi Aziza tayi sannan tace"haba Beauty maiyasa har yanzun baki waye ba? Kina university girl amman ace kanki yana cikin tukunya? Ai nasa zuwan da nike dake wajen samarina kina ganin yanda muke soyayyarmu nasa kina daukane kema zakiyi haka da saurayinki ashe akwai aiki babba a gabana tunda baki iya ba saurayinki kanki kuji dadinku, gaskiya idan har haka ne kuwa Beauty ƙawayenmu sai sunyi maki dariya kamar yanda akeyi ma Dejja wallahi." Ni kuma tunda naji tace za'ayi man dariya sai na shiga damuwa dan sai naga kamar zina ce zanyi, kallon Aziza nayi sannan nace mata "amman Aziza yin haka zina ce fa baki ganin za'a iya samun matsala watarana."!? Cikin tsoro nayi mata maganar na tsorata da alamarin sosai, kuma idanuwana sun kasa manta abunda naga su Aziza sunyi a cikin mota, budurwar zuciya Allah ya ƙara rabumu da budurwar zuciya Aunty Asiya wallahi sai naji inason nima nayi sex dan sosai abun ya burgeni take na fidda tsoron a raina so nike ma nayi dan nasan tabbas da dadi sosai yanda naga su Aziza suna ihu ita da Sadiq, murmushi nayi na kalle Aziza nace mata "karki damu, ƙawata zan iya ba saurayi na komai nawa na jikina mudun ina sonshi kuma zan aure shi." Kallona Aziza tayi tana murmushi sanann tace " haba Beauty yanda kike da kyaun nan masha Allah wallahi zakiyi samari kala kala kuma masu kudi, idan kika basu abunda ya kawosu wajenki na tabbata har mota wani sai ya baki dan nasan zakiyi dadi sosai, amman idan kika ce zaki barma mutun ɗaya kawai ya mora shi ɗaya raina ki zaiyi yaga bai takara da kowa dole ya ringa yi maki abunda ya gadama dan yasan kina sonshi sosai, amman idan kika tara samari dole ya riƙe damƙe wajen nuna jajarcewarshi wajen takara da abokan hamaiyarshi."

"Hmmm! Allah sarki da nasani ƙeyace, tabbas na tamka babban kuskure wanda har na mutu Aunty Asiya ba zan daina kuka akan abunda na aikata ba, kinsan abunda nace ma Aziza data gama kaya man wannan maganar."?

Girgiza kai Asiya tayi sannan tace "tabbas bansan abunda kika ce ma Aziza ba Khady, sai dai ke komai ya faru dake harda laifinki da kuma sakarci gami da sakaki da shashanci, dan ko tunda nike duniya ban taɓa ganin sakara irin ki ba Khady, kin biye ma son zuciya da kwaɗayi kinyi abunda bai dace, bayan kina ganin ita yar'uwa Dejja tana maida hankali wajen karatunta amman banda ke, ina sauraranki naji abunda kika ce ma Aziza."

Share hawaye na nayi, dan nasan duk abunda Aunty Asiya ta faɗi akaina gaskiya ne dan koni ban taɓa ganin sakara kamar ni ba, da kuma maison abun duniya ba son zuciya ta na biyemawa har na aika babban kuskure wanda gyara shi yana da wahalar gaskiya, cigaba da ce mata nayi.

"Dariya nayi sannan nace ai Aziza kin tuna dani abunda na manta kuwa, dan ni niyata wallahi saurayi ɗaya zanyi wanda zamu sha soyayarmu yanda ya kamata amman wani hanzari ba gudu ba, har yazun bani da saurayi fa ba wanda yace yana sona Aziza abun na damuna sosai." dafa kafaɗata Aziza tayi tana murmushi sannan tace "yaro yarone, inbanda abunki Beauty waye zance yana sonki a haka? Kullun kina yawo cikin ƙatuwar hijab kuma ko poder nan ta zamani baki shafawa balle muje ga janbaki a haka wani zai ce yana sonki? Ai wannan zamanin ba namijin da zaizo yace yana son BAGIDAJIYA, wanda bata iya ɗaukar wanka ba ai sun fi son irinmu wanda muka iya ɗaukar wanka ga kuma uwa uba iya soyayya, Khadija idan kin shirya fara soyayya kiji dadin duniya to sai kiyi man magana ni kuma zan ɗauraki a hanya, mu shiga ciki nayi wanka sai muci wannan kazar da Sadiq ya kawo mana."

Ina son nayi ma Aziza tambaya amman ta hanani tace dai idan na shiya fara soyayya nai mata magana, muna shigowa room dinmu na tadda Dejja tana karatu dan mun kusa fara test, kallona tayi tana murmushi sannan tace "Aunty Auta andawo kenan."? Da yake haushinta nike ji sai nace mata "ban sani ba, gulmaima, kina wani tambayana na dawo da ban dawo ba da kin ganni, nafa lura Dejja kina son fara raina man wayau bari na kira Yaya na gaya mashi irin rainin da kikayi man kinga sai yayi ma tuƙar hanci."

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now