9&10

274 4 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD

*Wannan page din nakine Ɓingel Allah ya kara daukaka da girma gami da  lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Yar'malam My Yar' Malam ina maki fatan alkhairy ta wajena*

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 9⏩10

Washe gari da safe Yaya Aisha ce ta fara zuwa asibiti ita da mijinta da yake ita bata da mota sai tare suka shigo dan ta gaya mashi komai ya faru dani ina zaune muna labari nida Dija sama sama  sai gasu sun shigo suna shigowa muka gaidasu sannan suka zauna wa'azi mijin Yaya Aisha yayi man sosai sannan ya tafi yace zuwa mangariba zai dawo ya wuce da ita gida, rakashi tayi sannan ta dawo tace. "Auta ya jikin naki."?  Da yake haushinta nikeji bugun da tayi man, dan komai ya faru dani a yanzun gani nike itace silar komai shiyasa bance mata komai ba na kauda kaina gefe, samun waje tayi ta zauna sannan tace. "Khadija  nasan kina kullace dani akan abunda nayi maki amman ki sani a lokacin hankali ya gushe shiyasa na biye ma Mama mukayi maki haka, dan Allah Khadija kiyi hakuri ki yafeman ko naji saukin abunda nikeji a zuciyata mudun baki yafe man ba wallahi Khadija ba zan sake farinciki ba, dan Allah Auta ki yafeman."hawaye take yi tana maganar, kinsan ace yar'wa rabin jiki ba'a shiga tsakanin yan'uwa take nace na yafe mata har abada kuma ya wuce wajena muna cikin haka Yaya Amina da Yaya Fatima suka shigo lokaci guda suma da breakfast dinsu haka muka gaisa sukayi man ya jiki sannan suka saman abincin naci suna ban labarin ban dariya har na koshi nasha Magani, waya suka kira Yaya sukace kar yazo da abincin rana sunzo dashi, likita yazo yayi man allura yace masu zuwa anjima zai sallamaini dan yaga jikin da sauki sosai sannan sai sun kara kula da lafiya ta sosai sannan ya fita, bayan Yaya yazo ya sake dubani sannan yace masu su taso su tafi nan suka ce man zasuje su dawo kafin anjimar sannan suka tafi.

a asibiti suka bar motar Yaya Amina suka tafi  da mota biyu, gidan Baba Ali suka nufa da yake a kwaɗo katsina bayan sunyi parking suka shiga suka fara gaisawa da matanshi sannan suka shiga parlourn shi samun waje sukayi suka zauna sannan suka fara gaidashi bayan sun gaidashi shiru ne ya biyo baya sannan Yaya Jamilu ya fara magana.

"Baba daman munzo ne mu gaya maka wata magana." kallonshi Baba yayi sannan yace. "Jamilu maike tafe daku Ku dukanku? lafiya kuwa dan naga kamar baku cikin natsuwarku."?  Yaya ne yace. "Ba lafiya Baba, daman munzo mu gaya maka Mama ce tace zatayi ma Auta Aure kuma wai Alhaji Salahu zata aura mata." cikin zafin nama Baba Ali yace. "Wai ni maike damun Hafsat ne dan Allah dan Annabi? Ita Mamana rasa masoya tayi shiyasa zata hadata da sa'ar haihuwata ko ta isheta ne."?  Girgiza kai Yaya yayi sannan yace. "Aa Baba kaddara ce ta hau kan Auta, ciki tayi amman ya zube yanzun haka tana asibiti, to dan tayi ciki shine tace zata aura mata shi wai dan ya rufa mata asiri ba yanda bamuyi da ita ba amman sai tace idan muka sake yi mata maganar sai ta tsine mana albarka." cewa Baba Ali yayi. "Subuhanalillah assha ai kaddara ce kuma hannunka baya rubewa ka yanke ka yarda ku kwantar da hankalinku yanzun nan zan tafi nayi magana da ita komai kenan zakuji ku tashi ku tafi Allah yayi maku albarka." "Amin ya Allah Baba." suka ce sannan suka tafi suna fatan dacewa.

Koda Baba Ali yaje gida wajen Mama bai damu da tarbar da tayi mashi ba, dan daman ba shiri suke ba tunda ya nemi ta bashi Yaya Amina ya rike da Babana ya rasu tace bata ba kowa ɗanta ita zata rike daga nan suke yar'ga maciji bayan sun gama gaisawa yace mata. "Hafsat nazo ne kan maganar aurar da Mamana da kikace zakayi ba tare da izinina ba ni kanan ubanta kinsan nine dai madaurin aurenta kuma an bata aure ko zuwa gaisuwar iyaye babu."?  Cikin masifa Mama ta fara yi mashi magana. "Wato Ali zuwa sukayi suka hadani dakai ko? Dan sun kasa to bari kaji wallahi baka isa ka hana wannan auren ba nan da kwana sha ukku za'a daura masu aure, dan ma kun samu Alhaji Salahu zai rufa maku asiri zai aureta a haka, ai nasa bayana zaka goya a matsayinka na mai hankali da hangen nisa ba nasu ba,amman sai naga akasin haka to kasani aura tuni akayi shi aka gama ko dakai ko babu."

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ