Sau biyu nasa 13&14 nayi mistake

224 5 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t
*ga link nan ku shiga amman ki tabbatar da zakiyi comment, fan's two ne, fans one ya cika kuma naga kuna man magana akan na saku a group ga shi nan na bude maku wani amman comment dole*

*Wannan page din nakine Dejja musy, ina maki barka da dawowa online, kuma naga comment dinki ina gdy sosai dan comment din ya sani nishaɗi sosai💃, Allah ya kara daukaka da girma gami da  lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Phatermarh kankia , my Temarh,   ina maki fatan alkhairy ta wajena*

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 13⏩14

Tunda su Yaya suka tafi Mama ta tashi tayi kalaci sannan tayi wanka ta zauna, duk da abun duniya ya isheta amman hakan bai hana Mama yi man addua ba,tana zaune Yaro yayi sallama yace. "Wai Aminu yace yana son magana da Khadija." shiru Mama tayi tana kallon Yaron da Aminu ya aiko sannan tace. "Maza kaje kace mashi ya shigo daga cikin gida." tafiya yaron yayi yana cewa. "To shikenan." bayan ya fita compound din gidanmu ya tadda Aminu jingina a jikin motarshi sannan yace mashi. "Mamanta tace ka shigo daga cikin gida." murmushi Aminu yayi sannan yace. "To shikenan nagode sosai kaji boy." tafiya yaron yayi yana murna, haka Aminu ya shigo har parlour sannan ya zauna ya gaida Mama, ansawa Mama tayi sannan tace. "Aminu ya ka baro gida da kuma mutanen gida."?  Cikin jin kunya yace. "Duk suna lafiya Mama, kuma suna gaisheku." murmushi Mama tayi duk da tana cikin damuwa amman tayi kokarin boye ta tace. "Allah sarki ina ansawa, Aminu sai dai kayi hakuri dakai ni mu baki ɗaya, amman Am... "Mama dan Allah karkice ba zaki auran man Khadija ba dan wannan kaddarar ta hau kanta, wallahi ina sonta a haka mudun ba Khadija ba ba zan iya auren ko wace mace ba, na roƙeki karki yi man haka."ya ida maganar yana hawaye, itama Mama hawayen take dan tasan nayi rashin masoyin gaskiya, girgiza kai Mama tayi tana murmushi mai ciwo sanann tace. "Da ina hali da gobe zan sa a daura maka aure da Khadija da na yi imani da kana kaunarta sai dai bani da yanda zanyi dan Khadija ta haɗa kayanta ta gudu ta barmu dan kawai nace zan ɗaura mata Alhaji Salahu." tashi yayi tsaya yana cewa. "Inalillahi wa'inna'alaihijirun, Allahunma'ajirni fi'masifati wa'akirni khari manha(note:-Idan kunga mistake wajen rubuta Addu'a ba laifina bane bani da zaɓi ne dan ba komai na iya rubutawa da hausa ba, dan hausa tana da wahala sosai😢, sai kuyi man uzuri my dear's fan's 🥰)  hawaye yake sosai sannan yace. "Mama tunda kin yarda da zaki aura man Khadija nayi maki alkwarin zan nemota duk inda ta shiga a faɗin duniyar nan, dan itace rayuwa ta, Allah ya jarabeni da ciwon sonta dan Allah Mama karkice banda kunya ina faɗin haka a gabanki bason ya zanyi control din son Khadija bane, ni zan tafi neman Khadija Mama." tashi Mama tayi da sauri ta rike hannun rigar Aminu tana hawaye tace. "Aa Aminu ban yarda kaje neman Khadija ba, dan ko kaje ba ganinta zakayi ba kuma Jamilu ya bada cigiyar ta, kaje ka zauna gida idan ta dawo zan gaya maka, idan kuma ba'a ganta ba sai kayi hakuri sannan kayi Addu'a Allah ya baka wanda tafi Khadija." kuka Aminu ya tashe dashi sannan yace. "Mama nine ya dace da nemo Khadija duk inda ta shiga a kasarnan ba Yaya Jamilu ba, tunda ni zan zama miji a gareta dan Allah Mama na roƙeki ki barni na nemota abunda nike bukata a wajenki shine ki saman albarka a matsayinki na mahaifiya ta Mama." ya ida maganar yana haɗa hannun wanshi waje ɗaya, cewa Mama tayi. "Allah yayi maka albarka Aminu amman ban yarda da kaje neman Khadija ba, sannan ban cika son musu ba." ɗaga kai yayi alamar to sanann yace. "To Mama ba zanje ba, amman Mama ba zan taɓa yin aure ba har sai Khadija ta dawo gareni zan mata addu'ar dawowa lafiya, zan tafi Mama na barki lafiya." haka ya tafi ya bar Mama tsaye ko motsi ta kasa, sai yanzun take yin nadamar abunda tayi sai yanzun ta gane abunda su Yaya Jamilu suke gudu kenan amman ta kasa fahimta cewa tayi. "Kaicona ni Hafsat, tir da mai hali irin nawa mai shegen zuciyar tsiya da zafin rai, na biye ma zuciya naƙi yarda da kaddarar da Alllah ya kawo man a gida, gashi nayi sillar gudumwar marainiyar Allah, wayyo Allah na." haka Mama ta kama cewa tana kuka mai tsuma rai.

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt