13&14

248 4 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD

*Wannan page din nakine Phatermarh kankia  Allah ya kara daukaka da girma gami da  lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Deey musy, my Dejja, ki sani nayi missing dinki sosai da sosai Allah ya maido man dake duniya social media lafiya sannan ya baki sa'ar karatun da kikeyi,  ina maki fatan alkhairy ta wajena*

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 13⏩14

Tunda suka shigo gida suka tadda Mama zaune tayi tagumi ga dukan alamu abun duniya duk ya bi ya isheta, da sauri Yaya Jamilu ya ida isa wajen Mama yana cire mata tagumi da tayi ɗaura kanshi yayi bisa cinyarta yana mata alamun lailashi, suma samun waje sukayi suka zauna duk sunyi shiru sun rasa abunda zakuce ma Mama, Yaya Fatima tayi karfin halin cewa. " Mama kin san dai mutum baya cika cikaken musulmi har sai yayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, itace ake kira da jarabawar rayuwa, Mama Allah kaɗai yasan irin kaddarar da Auta ta zano a rayuwarta kuma ba wanda ya isa ya wannan kaddarar, to mu mai zamuyi ma Auta Mama? Auta a halin yanzun tana bukatar Addu'armu muyi mata fatan faɗawa a hannun na gari." shiru tayi tana sauke numfashi dan halin da ta tadda Mama ta bata tausayi sosai kuma tabbas Mama tana son kula da ban magana mai dadi wanda zai sa hankalinta ya dan kwanta koda ba duka ba.

Kama hannunta Yaya Aisha tayi tana murzawa sannan tace. "Mama dan Allah ki yafe mana sannan ki yafe ma Auta, dan Auta ko tayi kuskure babba da tasa ƙafa ta gudu ta barmu ba tare da tayi wani tunani ba, kuma insha Allah zamu sa a nemo mana ita duk ind... "Aisha na yafe maku itama Khadija na yafe mata, amman ku sani ba wanda zaisa aje neman Khadija tunda ba wanda ya fidda sannan kuma ba'a aiketa ba, tabbas ba zanyi ma Khadija baki ba a halin sa take ciki sai dai nace Allah ya bata sa'a akan abunda tasa gaba nike na fita haƙinta a matsayin ta na marainiyar Allah ni kuma a matsayina na mahaifiyar ta mai son ganin farin cikinta, kuma da ta sani bata gudu ba da yau sai tayi dariya amman yanzun tunda har ta gudu ba baki ba watarana kuka zatayi da idanunta tana da nasani marar iyaka sai dai bani fatan Allah ya barni da rai na har wanann rana tazo, inalillahi wa'inna'alaihijirun Allah kana ganin halin da yarinyar ta samu ciki, ya Allah ka kareta daga sherin duk mai sheri, Allah karka ba wani damar kama ma ɗiya hannu da sunan yin fasiƙanci da ita koda kuwa ita ta kaimai kanta da kanta, ya Allah ka duba rayuwar marainiyarka wanda bata da uba sai uwa da yan'uwanta, Allah.... Kuka Mama ta fashe dashi kuka mai ciwo da ɗaci dan ita kaɗa tasan abunda takeji a zuciyarta.

Yaya Amina ce tayi karfin halin cewa. "Dan girman Allah kuyi hakuri addu'a dai zamu cigaba da yi kuma Mama kinsan jinin ya hau fa inji likita ya dace sausauta wannan damuwar, sannan Mama kika ce da yau  zatayi dariya, wace dariya zatayi ko kin fasa aura mata Alhaji ne."?  Girgiza kai Mama tayi sannan tace."Aa Amina ina bakata nayi mata aure, bayan Alhaji yazo zun gaisa da Auta sai na tafi nayi mashi rakiya zai koma gida, dan ita Auta suna gama magana ta tashi ta shiga ɗakinta, bayan mun gama ya tafi sai Aminu saurayin Auta yazo ya gaidani yace man ya shigo gari sannan yana ta kiran wayar Khadija a rufe shine yazo Allah yasa lafiya? Nan nace mashi yayi hakuri aure za'ayi mata take ya fara hawaye yana salati yana cewa maiye aibunshi da har Khadija ta fidda miji bata fidda shi ba, ni kuma tausayi ya bani sosai dan naga yana sonta sosai shine na gaya mashi abunda ya faru da ita da auren da zan mata da Alhaji ban boye mashi komai ba, amman abun mamaki maimakon yace bai aurenta sai yace man ai shi yana sonta a yanda take koda kuwa ta haifi cikin to zai aureta bayan ta gama shayar da abunda ta haifa sannan ya rike abunda ta haifa har yayi mashi aure, amman idan har na yarda a fasa auren da Alhaji shi zai aureta, amman sai nace mashi yaje ya dawo yau dan zanyi tunani, sannan ya shiga motarshi ya tafi bayan ya shigo da tsarabar da ya kawo mata, ni kuma ina dawo na tadda ta a parlour zaune, ban kai da yi mata maganar ba aka kira sallah na tashi na shiga dan yin sallah ina fitowa ban tadda ta a parlour ba sai na shiga kitchen na dafa mata abinci na haɗa mata ruwan wanka shigar da zanyi na tadda ta gudu, kuji abunda mukayi da Aminu."

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now