19&20

238 9 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 19⏩20

"Tunda muka raba room da Dejja Aunty Asiya, ba sake wata sabuwar rayuwa dan bani karatu ban damu da nayi karatu ba, abu yayi nisa ko lecture ban cika zuwa sai randa nayi niya sannan zan tafi, koda naje bai zama dole agama dani ba."

"Inalillahi wa'inna'alaihijirun, Auntyna kiyi man uzuri nasan labarina yana ɓata maki rai ko? Hmmm! Dole tasa nima nike baki shi, dan bani son ina tuna da abunda ya faru dani a baya." na karashe maganar ina kuka, dan sai yanzun na yarda na tabka babban kuskure wanda bai gyaruwa a wajena sai dai nayi addu'a Allah ya yafeman, amman ko na bar dama Allah ya bani dama amman ni nayi watsi da damata, na biye ma son zuciyarta, nazo daga baya ina dana sani,kallon Aunty Asiya na sake yi ina kuka sannan nace "nasan kina cewa Aziza ce sillar lalacewar rayuwata ko? Ko ɗaya ba ita bace duk tana da wani ƙamasho a ciki, amman nice mai laifin tunda bani ɗaya ta fara yima tayin ba harda Dejja, amman da yake ita Dejja ba haka ta zano kaddararta sai ta tsalake, ni kuma da yake haka tawa kaddarar take sai na faɗa a tarkon nata sosai."

Kallona Aunty Asiya tayi sanann tace"tabbas Khady kin tabka babban kuskure, duk bansan ina labarin naki zai kware ba, amman ina jinki Khady." murmushi nayi sannan nace, bari nayi sallahr la'asar sannan mu cigaba da labarin namu." itama tashi tayi tana cewa. "Har wanka ma kiyi, nima bari nayi wanka na gyara jikina sai na yi mana girki muci abinci." tashi mukayi a tare kowa ya wuce yaje yayi abunda yayi niya, sai da na fara yin wanka sannan nayi sallah, na shafa mai sannan na fito lokacin da na fito har Aunty ta gama dafa mana taliya fara da manja da yaji, sai yan'keke da tayi mana, zama mukayi muka ci abinci sanan tace "bari na kai kwanonin kitchen na dawo ki cigaba da ban labarin ko."? Murmushi kawai nayi bance mata komai ba, haka taje ta wanke su sannan ta dawo ta zauna tace "ina jinki Khady ki cigaba da ban labarin nan, bansan ya kaimu gobe, tun safe muke labarin." dariya nayi sannan nace "Aunty kenan, ni banga abunso a labarina ba, labarina da babu abun burgewa a ciki sai dai kayan haushi da taƙaici." itama murmushi tayi sannan tace "na yarda da maganar Aziza da tace maki Yaro Yarone, inbanda abunki Khady, ai labarinki shine abunji musamman ma ga yan'matan zamanin nan, masu son abun duniya irinki da kuma masu biye ma son zuciyar, da wanda suka dauki soyayya da muhimmanci har ya kaisu da aiki da nasani irin naki, so nike ki gama bani naki labarin sannan nima na baki nawa." ɗukar da kaina ƙasa nayi ina share hawaye, dan kuwa duk abunda Aunty tace gaskiya ne sai dai ance DANASI ƘEYA CE, KUMA TANA BAYA tabbas haka maganar take, cigaba da cewa nayi.

“wata rana da ban taɓa mantawa ba,ranar da fita zani kasuwa dan yi mana cefene sakomakon kayan abincinmu sun ƙare bamu da komai sai dai muci kayan lakumashe kayan da samarin Aziza suka kawo mata idan sun gama *SOYAYYAR MINTIN SU*  take kawo sai muci, gajiya nayi da zaman yunwa yasa na shirya dan zuwa kasuwa nayi mana provision, tunda na shiga kasuwar na hadu da gani gaye ya fito cikin wata elentra kallo ɗaya nayi mashi naji ya tafi da zuciyarta, dan wani irin mugun sonshi naji ya kamani daurewa nayi naƙi yi mashi magana saboda class da nike son ƙankaroma ƙaina, shago ɗaya muka shiga dashi shima ga dukan alamu yazo yasan wani abu ne, samun waje nayi na zauna ina jiran wanda na iske a shagon su gama abunda ya kawo su sannan nima nayi, shima kusa dani ya samu waje ya zaune ya ƙuraman ido yana kallona, da yaga zan ɗago idanuna sai yayi sauri ya maida hankalinshi a wayarshi, abunda bai sani ba shine duk abunda yake ina sane dashi dan hankalina yana kanshi saboda na kamu da sonshi, bayan wanda muke jira sun gama ya sun tafi sanna na tashi na fara kwasar kayan da nazo siya, shima zaƙewa yayi yana ɗibar kaya, dan kuwa duk abunda na dauka shima sai ya dauka kuma ba ɗaya ko biyu yake ɗauka ba sai ya dauki guda uku zuwa hudu, haka muka gama siyayarmu akayi mana total kafin na fiddo kudi naji yace "ka dauki kudin harda nata." yana miƙa mashi atm dinshi, kallonshi naɗago inayi kafin na fiddo kudin nima nace, malam ka haƙinka ka saman kayana cikin shopping bag sauri nike yi, murmushi guy din nan yayi sannan yace "haba yan'mata wa yake maida hannun kyauta baya? Ni nayi niyar biyaki ba tambayata kikayi ba." harararshi nayi sannan nace "nagode sosai, amman ka barshi zan biya da kaina, haka ya matsa sai da ya biya sannan yasa aka kwashe kayan aka kai a boot din motarshi kallon shi nayi sannan nace"ya haka Malam."?

Murmushi yayi sannan yace"kyawkyawar budurwa kamarki bai kamata ace tana hawan keke naped ba, sannan kuma bai kamata ace ta dauki kayan nauyi ba da kanta, idan kuma nayi laifi ayi man afuwa yake kyawkyawa wanda tafi ko wace mace a faɗin duniya kyau." Allah sarki ban san sanda murmushi ya kauce man ba, dan naji dadin yanda ya koɗani sosai buɗeman gaban mota yayi ni kuma na shiga nan muka kama yawace kasuwa ina sayen abunda nayi niya harda wanda banyi niya ba, dan bani ke binyan kudin ba shine yake biya, haka muka gama sannan ya kawoni hostel ya kuma anshi number ta nan yake gaya man sunanshi yace. "Ni sunana NURANDEEN, kefa."? Murmushi nayi sannan nace mashi. “Khadija."murmushi yayi sannan yace “woow! Nice name, My life anjima zan dawo muyi soyayyarmu ko."? Murmushi nayi ina ɗaga mashi kai, sannan na fito nasa aka daukar man kayana na shigo ciki, nan nagaya ma Aziza irin kamun da nayi, nan tace “banyi mamaki ba, kuma nasan zakiyi wanda yafi shima, abunda nike so dake shine ki bashi abunda yake so, ke kuma zai jiƙaki da ruwan kudi." cikin jindadi nace “ai daman zan bashi abunda yake so tunda inasonshi, sai dai daga shi ba zan kwara yin saurayi ba, dan yayi man kuma aurenshi zanyi." wata irin dariya Aziza tayi sannan tace “Beauty kenan, har yanzun ke yarinya ce, amman idan kika fara soyayya dashi kikaji dadi, da kanki zaki nemi wani ki ƙara haɗawa yanda zakijiki zamײdake." nidai bansake cema Aziza komai ba, na shiga wanka na fito nan ta fara bani wasu magunguna tace nasha zasu taimakaman wajen soyayyar da zani fara yi a yau.

A bangaren Dejja ta taitarani ta ajiye gefe tana cigaba da hidimar gabanta, kuma karatu take sosai duk da tana sane da halin da nike ciki na rashin zuwa lecture kuma bani test balle assigment, amman bata da zaɓi tana dai yi man adduar shirya kuma tana mani fatan nasara.

Koda dare yayi haka na shafa mayamayai iri iri duk Aziza ta bani su, sannan ta tsaraman kwaliya mai kyau, ta fesa man wani turare ta kuma shafa man wani a jiki sannan ta bani wata sweet tace nasha idan ina hanyar zuwa wajenshi kafin na ida isa na shanye, nidai da to kawai nike binta dan tunda ta nasha maganin da tabani nike jina wani iri hakuri kawai nike ina daurewa, tana gama dauraman dan'kwali ya kira waya yace yana bakin hostel, kara gyarawa nayi sannan na jefa sweet a baki na tafi wajen Nurandeen....

*Sannanku da hakurin jirana da kukayi, biki nayi shiyasa amman yanzun komai zai zama normal insha Allah tunda na gama, amman fa ku cigaba da zubaman ruwan comment kamar yanda kuka saba😍*

Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now