33&34

155 5 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 33⏩34



Tunda Dejja ta taho naga tana dariya nasan da magana a bakinta, kallonta nayi sannan nace "fatan dai yaci abinci ko."?  Dariya tayi sannan tace "kwantar da hankalinki Aunty Auta yace baya iya cin komai har sai ya saki a cikin kwayar idon shi." Murmushi nayi kawai sannan nace  kice yau Aminu baya cin abinci, dan ba idan zani har sai yaci abinci kije ki gaya mashi haka injini." marairaice fuska Dejja tayi sannna tace "haba dan Allah Aunty Auta ya kamata ki tausaya mashi mana, yana bukatar ganinki hankalinshi ba zai kwanta ba har sai yayi tozali dake please kisa ma ranki soyayyar Aminu, dan shine masoyinki na gaskiya wallahi ko Aunty."

Naunauyen numfashi na sauke sannan nace "zanyi kokari insha Allah Dejja je kice mashi gani nan zuwa yanzun nan." Murmushi kawai tayi sannan ta wuce, tana zuwa tace mashi. " to Uncle Aminu sai hankali ya kwanta ga Aunty nan fitowa tace tana zuwa yanzun." Murmushi yayi sannan yace "Daughter anshi wannan gift ne na kawai kin gayaman dawowar Auntynki sannna gudar kyautar kuma sai kin jini." Murmushi tayi sannna tace "ina godiya sosai Uncle Allah ya barka da Aunty Auta." ɗaga hannu sama yayi sannan yace "Amin ya Allah." tun daga nesa naga ya kafeni da ido sai kallona yake kamar zai haɗiye, ban san na fara dabarbarcewa ba wajen tafiyar dan kallon yayi man yawa sosai, kallonshi Dejja tayi dan taga hankalinshi baya wajen ta gani tayi nice na taho shiyasa attention dinshi baya wajenta tashi tayi tana dariya ta bar mashi wajen tana zuwa dai dai setin kunnena tace "ki daure pls Aunty Auta nasan zaki iya ma, dan nasan Auntyta jaruma ce." Murmushi kawai nayi sannan na ida isa wajen shi, sallama nayi na shiga kasa amsa sallamar yayi kallona kawai yake samun waje nayi na zauna sannan nace "ina kwana." Nan ma shiru baice komai ba sai da aka dan jima sannan yace "Amin wa'alaikumus sallam, masha Allah Alhmdulh, Allah nagode maka da ka maido man da matata gida, lafiya Noor fatan kina cikin koshin lafiya."?  Kasa nayi da kaina ina wasa da hannuna sannan nace "lafiya lau, fatan kaima kazo lafiya."?  Murmushi yayi sannan yace "lafiya lau Alhmdulh, ina sonki ina kaunarki Khadija bansan ya zan misultamaki son da nike maki ba Khadija, ban son sonki a jinin jikina yake ba har sai da kikayi mana nisa, Khadija nasha wuya sosai wallahi baki san halin da nashiga ba,amman na wahala sosai dan Allah karki sake yi mana nisa ni Aminu inasonki duk yanda kike wallahi."

Kasa ce mashi komai nayi, danni alamarin Aminu mamaki yake bani na yarda yana sona, kuma so na gaskiya da amana, amman ni zuciya ta kasa yarda da hakan dan kuwa duk maganar da ya gama yi man jinshi kawai nayi amman banji komai a zuciya ta ba, amman nasa ma raina zan koya zan tusa ma zuciya ta sonshi dan shine masoyi, ya isa a kirashi da suna masoyi wanda ko wace ƴa mace take burin samu a duniya, tabbas inajin soyayyar Nurandeen a cikin zuciyata dan ta kasa mantawa da shi,amman wannan karan zanyi yaƙi da zuciya ta ba kori son da take ma mayaudari mahaƙinci na tusa mata son masoyin gaskiya wato Aminu, ji nayi yace "dan Allah Khadija karki juyaman baya a wannan karon karkiyi fatali da soyayya ta, ina sonki ina kaunarki ban cancanci kora a wajen ki, ki amince da aurena zan koya maki sona please Khadija." take naji ya bani tausayi daman ashe haka so yake? Tambayar da nayi ma kaina kenan, son maso wani koshin wahala, amman insha Allah zanyi iyakar kokari na Murmushi nayi wanda bansan nayi shi ba, kuma ba komai ya sani Murmushin ba sai  maganar Dejja da ta fado man a rai da tace tabbas nasan zaki iya, saboda Auntyna Jaruma ce, take nasa ma kaina iyawa nace mashi. "Karka damu Malan Aminu, Allah ya tabbatar da abunda yafi zama alkhari a tsakaninmu, ya kamata kaci abinci idan baka ci ba niko ba zan ji dadi ba gaskiya." Murmushi yayi take naga kuzarinshi ya dawo kallona yayi sannan yace "duk banjin yunwa amman zanci abincin nan idan har hakan zai saki farin ciki da nishiɗi da kuma annashuwa." fari nayi mashi da ido sannan nace "hakane mudun kaci zanyi wannan abubuwan da ka lissafo, amman idan har baka ci ba zan rasa abubuwan da ka lissafo." zuba mashi nayi sannan na tashi na bashi waje yaci yanda yasan ba zance bai ciba, sannan ya kira Dejja yace tace man ya gama ina zuwa muka kara gaisawa sannan ya bani sabuwar Samsung galaxy S10 sabuwa yace gashi nan yasan yanzun banda waya harda sim duk ya saya man ya sanya man, ansa nayi nayi godiya sannan na raka shi har bakin mota ma dawo na nuna ma yan gida suka taya ni murna.

Tunda Aminu ya bani waya kullun sai munyi waya dashi idan bamu waya to muna online muna chatting sosai yake nuna man kulawa yana nuna man soyayya tsantsa wanda har mamaki take bani idan naga yana rawar ƙafa a kaina sai kace baisan abunda ya faru dani ba.

Nima a wajena ba laifi dan na fara koya kuma ina iyakar bakin kokarina wajen nuna mashi kulawa da kuma soyayya kuma ina addu'a Allah ya tabbatar da alkhari, su Mama sunje Kano da Aunty Asiya wajen family din Mamanta kuma sunyi murna da ganinta sosai, da sun so ta zauna wajen su amman tace aa ba yanzun ba su bata lokacin, basu yi mata gardama sannan sun amshi number wayarta da yake Yaya Jamilu ya siya mata waya haka sukayi kwana biyu sannan suka dawo suna dawowa da sati ɗaya muka shirya muka koma makaranta .


*yawan comment yawan typing ba zan sake yi maku complaining ba yanda kukayi nima haka zanyi insha Allah🥴*

    

Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now