37&38

136 9 1
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 37⏩38

Wani banzan kallo tayi mashi sannan tace. "Kai ɗin banza kai ɗin wofi, wallahi wallahi cikinka uwarka bata ɗauka ba balle har ta haifoka a cikin duniyarnan, idan da kayi nasara akan Aunty Auta to ka sani Nurandeen yanzun ba zaka taɓa yin nasara ba a kanta, abunda nike son kasani shine wata shara'a sai a lahira to kasani wani abun da kayi mata sai ranar Allah zai ansar mata da haƙinta." tana gama faɗin haka ta fisge hannu muka fito shagon turaren da bamu saya ba kenan, dan ko ni ba abunda nike sai kuka dan ganin da nayi ma Nurandeen ya tuno man da abubuwa da dama wanda bani fatan sake tunasu a rayuwata, tsaye muka barshi kamar gunki ba abunda yake sai hawaye, kallona Dejja tayi sannan tace “Aunty Auta idan na fahimta har yanzun son wannan tsananen dan'iska mazinaci kuma fasiki yana cikin zuciyarki ko? To wallahi tun wuri kiyi ma kanki fighting, dan ba wanda zaiyi maki wallahi ko kuma ki sani mudun kika ce zaki sake kulashi to wannan karan ba zan maku ido ba Baba kawai zan kira waya na gaya mashi kin sake komawa ruwa sai su san abun yi, dan na tabbata mudun Nurandeen ya dawo cikin rayuwarki ida lalata maki rayuwa zaiyi ya kama gabanshi ya barki da kuka, amman ki sani wannan karan kikayi kuka ba wanda zai saurareki sannan ba wanda zaiji tausayinki sai ma tsanarki da za'ayi, abunda zai baki mamaki shine cikin mutane masu tsanarki nice kan gaba wallahi wallahi wallahi Aunty Auta nayi rantsuwa mudun kika koma ma wannan bunshunrun bani ba dake har gaban da abada wallahi ko."


Da sauri na ɗago kai na ina kallonta dan furincinta ya bani mamaki da al'ajabi sosai gami da ban tsoro, wai ni Dejja take cewa bata bani har abada saboda wani soko banza wanda a faɗin duniya bani da maƙiyi kamarshi wanda ko fuskarshi bani son sake gani a rayuwata, da ace nasan zanga Nurandeen a cikin kasuwa da ba abunda zai kawoni cikinta dan babu amfanin zuwan nawa, amman ace kamar ni ina ƙanwar ubanta take gaya man magana haka san ranta nima cikin fushi nace. “ban san iskanci da shirme fa Dejja, wai shin na tambayeki mana? Kin fini tsanar Nurandeen a rayuwa? Ko kuma kin fini jin zafin rabani da budurcina da yayi? Ko kuma kin fini jin ciwon yaudarata da yayi? Sannan kin fini jin ciwon maidoni baya a akayi a makaranta duk  A SANADIYAR SOYAYYAR SHAN MINTIN DA NAYI DA NURANDEEN? ko ɗaya baki fini ba Dejja, asali ma ni har na mutu na koma ga ubangijina Allah ba zan manta da wannan abubuwan ba a rayuwata kuma ba zan daina kuka ba koda kuwa kukan zuci ne Dejja." kuka na ƙara fashewa dashi sannan na cigaba da cewa. “wallahi wallahi Dejja da ace yau ni Khadija Bello ina yawo da wuƙa a cikin jikka to wallahi a yau ɗinan sai na lumama Nurandeen ita a ƙahon zuciya sai dai nima a kasheni idan na kashe shi, kinsan kukan mai nikeyi ne Dejja."? Itama hawaye take ta girgiza man kai kawai dan Dejja ta fini saurin daukar fushi da zuciya shiyasa ta kasa magana, Murmushi nayi mai ciwo sannan nace. “ina kukan baƙin ciki ne yau naga maƙiyina wanda nafi tsana a duniya wanda nike fatan Allah ya haɗani da shi na dauki fansar abunda yayi man, burina akan Nurandeen shine na zama a jalinshi Dejja kuma wallahi insha Allah ni Khadija Bello sai na zama a jalin Nurandeen, ina mashi fatan haduwata ta biyu dashi lokacin zai baƙunci lahira wannan kuɗirina ne, dan ni bani auren kowa tsakanin Aminu da Dr Umar, dan ban dace dasu ba banda abunda zanyi taƙama dashi a gidan miji  Nurandeen ya ansheshi cikin dubara ba tare da na fargaba, Dejja tabbas A SANADIN SOYAYYAR MINTI NA ƁATA RAYUWATA😭, rayuwata bata da amfani dan bani iya auren wani ban kai mashi budurcina ba hakan na iya sa zuciyata ta bugu, kinga kenan banda amfani a duniya mutuwa ce tafi dacewa dani dan haka zan kashe Nurandeen sannann na kai ƙaina a hukuma nima daga ƙarshe a kasheni hakan shine dai dai kuma haka shi yafi dacewa dani Khadija Bello."

Kuka Dejja ta fashe dashi tana girgiza man kai dan tasan ni sarai idan nacr zanyi abu sai nayi, tana so tayi magana amman ta kasa mai naped na tarar mana muka shiga muka tafi, shiru nayi ina sauraran kukan Dejja wanda nikeji kamar mai dan bansan kukanta ko ya yake, kallonta nayi nace....

*ina kan bakata wallahi mudun bakuyin ruwan comment kamar yanda kukeyi a da ni kuma ba zan kara maku yawan typing ba, kuma next stage bansan abunda zanyi ba😂*

*Yauwa duk wanda take son karanta Izzah ko mulki tayi ma wannan number magana ta private 08160508316 zan tura mata document dinshi dan maganar gsky ban iya posting din shi page page daman sayan maku akayi duk mai ra'ayin karantawa sai tayi magana bye*

Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now