ZAFI BIYU

112 1 0
                                    

ZAFI BIYU

Written by Qurrah

Page 1

Golden pen writer's association ✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim

Mutane zasu iya kirana da karamar mahaukaciya a irin halin da nake ciki, Kuma zan iya cewa duniya nafi kowa ce mace rashin sa'ar rayuwa rayuwa ta tana tafiya ne da kaddara ta tunda na bude ido na ganni ina rayuwa ina rayuwa cikin tsananin kunci, A rayuwa ban taba samun mako guda cikin farin ciki ba mi nayi ma rayuwa take tafiyar dani haka? kode ba dai-dai nake bauta bane kullin nake cin karo da jarabta, Anya ni mutum ce kamar sauran mutane shin wai minayi rayuwar nan ne?

Farin ciki daya ne na taba haduwa dashi a rayuwata kuma ya tafi yabar ni dole ne na nemo farin cikana a duk inda yake idan ba haka ba kenan zan tabbata cikin wahala da kuncin rayuwa.

A kasan bishiyar nake ina wannan tunanin kuka mai sauti kawai na saki ina bugun kasa  da duka hannayena tamkar mahaukaciya, Duwatsun  da suke a cikin kasar suka cigaba da fasaman hannu jini na zubar man amman idanuna sun makance bana gani zuciyata ce a yanzu ke gani ita kuma a kuncin da nake ciki take gani.

"Rayuwa minayi maki kike man haka! Minayi maki! Minayi maki!"

A gefen hanya nake wannan abun amman babu wanda ya kulani kowa harkar gaban sa yake.

Cikin sauri na tashi ina gyara guntun Siket din dake jikina wanda cinyata kade ya rufe man, Kaina babu dankwali saboda askin dake kai bandamu da saka kallabi.

Sai kusan karfe ukku kana na mike ina rike kaina dake mani ciwo kamar zai fado wajen wani mai saida kifi na nufa ina isa wajen kamar na fada a cikin mai saboda yadda naji ina kwadayin kifin.

"Malama lapia kikayi man tsaye?"

Kuuuut na hade wani miyau inajin kaman na fada kana nace;"Ka taimaka kabani kifin nan wallahi ji nake kamar na fada"

Na fada ina kara matsawa kusa da wutar.

Kallo na yayi daga sama har kasa zaiyi magana wata mata ta iso zata sayi kifin.

Ganin matar cikin cikakkun sitira yasa nayi tunanin musulma ce.

Bai kara kula ni ba hankalin shi ya koma a wajen ta.
Ni kuma nayi tsaye a wajen ga zafin wutar na buguna ga tsanin ranar da ake amman duk da haka ji nake kamar na shiga cikin nan na dauka.

Kifin ta siya mai dan yawa harta juya sai kuma ta juyo ta kalleni taga yadda nake hada miyau ga ido dana kura ma kifin gashi kara matsawa nake kamar zan fada.

Hannu Maikifin yasa ya banga jeni cikin yaren French yadda zanji yace;"Nabar nan kada na saka mashi datti a kifin shi"

Matar ta juyo tana kallo daga sama har k'asa kana tace;"Kai ko mai kifi miyasa zaka mata haka baka ganin abinda take tare da shi"

Tayi maganar cikin wani French wanda take hada kalmomin da kyat.

Kallo na yayi da manyan Jajayen idanun shi kana yace;"Ban son miyasa ba yaran yanzu suke sha'awar daukar ciki da kananun shekara, Kuma baki ganin jikin ta da datti irin su kashe maka kasuwa suke Mtwss"

Ya ida maganar cikin kosawa da jin haushi.

Matar ganin haka yasa ta tabar maganar dashi, Ta juyo wajena tana kallon yadda nake nishi nakasa tashi saboda marana ya rike.

Kama ni tayi na mike ina rike katon cikina daya bayyana.

Batayi man magana ba ta kama hannu na muka isa wajen wata bishiya muka zauna.

"Yarinya Miya kawo ki nan daga ina kike? Minene sunan ki?"

Ta jeroman wannan tambayoyin tana kareman kallo.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now