ZAFI BIYU

17 0 0
                                    


Z_B
Written by_Qurrah
Wattpad _Qurratou
Page_7
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION ✍️
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

A hankali na bude ido na ina kallon saman dakin kara lumshe su nayi ina tunanin ko mafarki nake ko kuma na mutu na shiga aljannah.

"Ciki nah!!"

Nayi saurin fada ina tashi a firge ce sai yanzu na fara tuna abinda ya faru dani.

"Innalillahi Baby na! Baby na"

Shafa cikina nayi naga babu alamun ciki a tare dani cikin sauri na diro daga bisa gadon da nake kwance, Dukkan ilahirin jikina kyarma yake ji nayi kafafuna sun kasa dauka ta wasu hawaye masu dumi ne suka zubo mani.
Faduwa kawai nayi k'asa tare da aza kuka mai sauti ina bugun kasan dakin taushin carpet din dake a kasan dakin ne ya hana hannuna fashewa ganin haka bai isheni saina fara bubbuga kafafuna ina kuka.

Cikin sauri na tashi nayi hanyar fita daga dakin cin karo nayi da Hanne da Maimashin din daya banke ni.

Saurin kama hannun Hanne nayi ina kuka ina nuna mata ciki na nama kasa magana saboda yadda naji wani abu ya tsaya man a makoshi maganar bazata iya fita ba.

Kamani take kokarin yi amman naki barin ta sai hizge hizge nake ina nuna mata cikina ina kuka ina jijjigata daga karshe na duke k'asa ina kuka.

Hanne ta kalli Maimashin din daya bankeni tace;"Kana jin yaren ta ne"

"Inaji amman kadan saboda nayi zama border"

"To kayi mata magana mana ta fahimta"

"Taya zan mata magana gani nake fa kamar bata cikin hayyacin ta fa"

Kamani Hanne tayi tana girgiza man kai kana Maimashin dina ya duka yace;"Beedah kin haihu likitoci suka cire maki Yarinya watan ta bakwai tayi karama shiyasa tana cikin kwalba saita kwana biyu kana a baki ita"

Jikina kyarma kawai yake tare da kafa mashi ido na fahimci miyace haka yasa nayi mashi nuni da hannu ina nufin nikeda yarinya? Daga man kai yayi.

Hawaye ne na dadi suka zuboman tare da rungume Hanne.

"An maki aiki ki koma bisa gado kada a samu matsala bari mu kira Doctor "

Tashi yayi ya fita Hanne kuma ta dauke ni ta maidani bisa gado.

Sai gashi shida Doctor sun shigo nan ya dubani ya fadaman kada na kara motsi zan lalata dinkin dake jikina nayi hakurin kwana biyu zan warke zuwa gobe zan iya komi.
Kai na daga mashi tare cewa;"Ina son ganin Baby na"
Na fada ina lumshe idanuna tare da tunanin ya kamannin ta suke.
Murmushi yayi yace;"Zaki ganta amman sai anjima, motsawar da kikayi yanzu ya dan ja matsala amman zan gyara kinji"

"A'a ina son ganin"

Na fada ina niyar tashi da kwance da nake.

Kwantar dani Hanne tayi tana girgiza man kai amman naki ganin haka Doctor yayi man allura nan bacci ya dauke ni.

Ban farkaba sai cikin dare tashi nayi ina kallon Hanne dake gefena bisa kujera tana bacci.
"Hanne! Hanne"

Cikin sauri ta tashi tana kallo na kana nace;"Hakeem! Hakeem"

"Kin san shine?"

Cikin sauri na daga mata kai sai yanzu na tuna dashi dazun bana cikin hankalina saboda na tashi banga cikina ba hakan yasa na manta da kowa.

Baki daya na dimauce sai tunanin kafafun Hakeem dana gani nake jikina sai tsuma yake sanyin dake dakin bai hanani zufa ba.

Baki daya daren zaune na kwana ina jiran Safiya ta waye naga diyata sannan na kaita ga Baban ta.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now