ZAFI BIYU

16 1 0
                                    

Z_B
Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page_8

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION ✍️

Ganin suna kallon kallo nagane akwai wani mummunan abu da ya faru dani kama hannun Hanne nayi nace;"Ki fadaman mana kowa ne dan Adam nada nashi kalar kaddarar kila ni wannan itace tawa, Dan duk macen da akama zindir a titi to babu wani sauran k'iba gare ta a idanun mutane Barar da nake ba komi bane ku fadaman gaskiya mi Babah Indo tayi man"

Hanne sai kyaf ce kyaf ce take saboda bata son mi nake fada ba.

"Kada ki damu Allah ya kawo maki mai taimakon ki akan lokaci Babah Indo ta daga zata debe maki kaya saiga Hakeem lokacin kinma suma bugun da tayi maki a ciki, Imran ne ya rike mata hannu kana Hakeem ya dago ki a lokacin wasu sunyi tunanin ko kin mutu duk wanda ke wajen yaji tsoron hakan yasa kowa yayi saurin tserewa shine suka dauko ki suka kawo ki nan hospital din muna zuwa akace kwana biyu kina nakuda kuma abinda ke cikin ki bai isa haihuwa ba hakan yasa suka ce zasuyi maki aiki a fidda abinda ke a ciki nan Hakeem yayi signed suka biya kudin aiki bayan awa biyu aka fiddo ki keda yarinyar ki Hakeem suka saka mata suna sun tambaye mu nida Hanne ko mun san sunan Baban Baby ki mukace a'a hakan yasa suka saka sunan ki jiki tun safe basu bar nan ba sai yamma kinji abinda ya faru"

A jiyar zuciya na sabke kana nace;"Gaskiya sunada kirki sosai"

"Sosai ma suke da kirki haka Maman su itama take da kirki"

"Kasan su ne?"

"Eh a gidan su Mamana ke aiki kusan shekara sha wani abu"

"Ina son zuwa chan dan Allah Ka taimaka man"

"To shikenan amman kiyi hakurin komi ya zama dai-dai kana"

Doctor ne ya shigo ya basu sallama sannan yace kullun a kawo ta taba yarinyar ta abinci daukar su Maimashin yayi suka tafi.

Tafiya mukayi mai dan nisa kana muka iske wani tsohon gida dake dauke da dakuna da yawa nan naga Maimashin na gaisawa da mutanen dake zaune waje kana ya bude wani daki yace;"Hanne ku shiga ku zauna bari na dawo"

Dakin muka shiga daki ne mai dauke da wata yalolowar Katifa sai Risho da tukunya a gefe kuma bokitin ruwa ne sai jikka ta kaya.

Zama nayi gefen Katifar ina kallon dakin tsab a share kamar ba dakin maza ba.

Jim kadan sai gashi ya shigo dauke da kula ya aje tare da aje mana jikkar PureWater kana yace;"Beedah nan dakina ne zanbar maku shi keda Hanne zan koma dakin Abokina dakin abokina nan kusa ne idan kuna bukatar wani abu saikuman magana"

"To shikenan mun gode sosai"

"Bakomi"

Ya fada yana murmushi nan sukayi magana da Hanne kana ya wuce.

Kwance nayi ina tunanin magan ganun matar nan akan Nigeria mtsw na danyi tsoki nace;"Bata san ya mutanan Nigeria  suke ba sunan tana yan Nigeria indan abinda Babah Indo tayi man bazai sani na koma baya ba ko ina akwai mutanen kirki akwai na banza na sannan ko Babah Indo rashin fahimta ne.
Da wannan tunanin na k'arfafama kaina na akan zuwa Kano neman Baban Baby na.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Kamar kowa ce Jummu'a yau ma parlon gidan ya cika da iyalen gidan yau Hakeem da wuri ya iso dan haka ya zauna ne kusa da Imran inda kowa yake zama sun gaisa da saura Family fira suke kadan tsakanin wajen zaman matan daban da mazan daban hakan yasa tsakanin su da mata saide hange.

Cikin takun K'asaita Kamal ke tafiya komi nashi mai tsada ya k'ara gyara fuskar shi Kamal babu laifi yana da kyau hakan yasa yake karya zuciyar yan mata sannan ga dukiya dake gare su hakan shine ya bashi Daman yin yadda yake so.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now