ZAFIE BIYU

39 1 0
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page_5

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION ✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Gefen wata katuwar bola muke zaune cikin wani Kango, Tagumi nayi ina tunanin yadda zamuyi da sauro zuwa anjima, Gashi  ba'a son mai ciki sauro ya cije ta toni gani a gidan shi.

Ina zaune har dare ya fara nan naga sauran yan Uwana masu bara sun tashi kowa yayi hanyar samun abincin.
Mikewa nayi da katon ciki ina kallon Babah Indo dake kirga kudin ta gasu nan tuli guda a gaban ta mafi yawa duk chanjine.
Mamaki nake yadda ta samu kudin Kuma duk a cikin Bara kasa daurewa nayi nace;"Babah Indo ko kina wata sana'a ne naga kin tara kudi da yawa haka"

Murmushi tayi kana ta fara maida kudin cikin wani ma'ajiyar kudi dake a jikin ta saboda mutane sun fara dawowa kana tace;"Yarinya kenan Bara da kika ganta kudi take kawowa harmade tsallaken Nigeria ada ban yadda ba lokacin da k'awata ta fadaman saida na fara kana"

Shiru nayi ina tunanin nima yanzu haka zanyi kenan?

"To Babah Indo taya nima zan samu kudi?"

"Kada ki damu ki bari gobe mu isa Legos zan nuna maki yadda ake samun kudi da Bara yanzude ga Naira d'ari ki sawo dankali kici gashi chan bakin titi su Hanne sun sawo"

"To nagode Babah Indo"

"Basai kinyi godiya ba duk abinda na kashe maki idan muka isa Legas zaki nema ki biyoni"

"To shikenan duk da haka nagode"

Tashi nayi nabi Hanne muka nufi wajen wani mutum wanda ke soya Dankali da doya da kwai.

Muna isa suka gaisa da Hanne na mike kudi ya zuba mata Dankali sannan ya saka mata doya da kwai a cikin.
Murmushi tayi kana tace;"Nagode "
Tana maganar tana kashe ido kamar tana magana da Mijin ta.

Mika mashi kudina nayi naira d'ari tare da nuna mashi Dankali.
Zubaman yayi kana nima ya saka man Doya da Kwai amman kadan ba kamar na Hanne ba, Godiya nayi kana na mika hannu zan amsa.
Abin mamaki kawai sai mai Dankali ya rike hannu na tare da kashe mani Ido.
Zame hannu na nayi Danklin ya fadi k'asa da Doyar k'asa cikin bacin rai nace;"Minene haka nazo siyayya zaka rike mani hannu na?"

Hanne ta rike man hannu duk da bata jin mina ce saboda bata jin French gaisuwa kawai ta iya amman tasan fada nake.

"Malama dakata Kada ki tara man mutane anshi kudin ki bana saidawa kuma Kada ki k'ara dawowa"

Amsar kudina nayi ina tsoki kana na juyo na taho nabar Hanne tana bashi hakuri.

Ina dawowa na zauna cikin fushi ina tsoki Babah Indo na tambayata Lapia ai ban bata amsa ba saboda yadda raina ya baci Hanne ce ta shigo nan ta fadi abinda ya faru.
Kawai sai naga matan nan na dariya wasu kuma na tsoki irin na basu haushin nan.

Kama hannu na Babah Indo tayi tace;"Beedah Mai doya bashi da laifi kece mai laifi, waya  gaya maki a banza ake samun kudin bari nayi maki misali da Hanne, Hanne da kika gani yarinya ce Haihuwar ta biyu suka rabu da Mijin shine Maman ta ta kawo ta wajen Talatu  kinganta chan itace k'awata wannan shine zuwan ta na farko amman saikinga dukiyar da zata koma ma mahaifiyar ta da ita sannan da kayan amfani kuma ba'a Bara kade ta sami wadan nan  abubuwan ba , d'an haka idan zaki dage ki dage kibar wannan sakarcin cikin jikin ki bazai hana maki komi ba d'an haka ki shirya idan mukaje Legas yanzu na maki Uzuri saboda baki san kan harkar ba"

Hanne ce tazo inda nake ta miko man Dankali biyu da doya guda na amsa nayi godiya.

Bayan na gama ci na kalli Babah Indo nace;"Babah amman miyasa bazaki ba Hanne shawara ba akan ta zauna gida tayi sana'a zaifi naga da karfin ta"

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now