ZAFI BIYU

36 0 0
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page_10

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION ✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim

Kallo daya zaka masu ka gane su duka basa cikin yanayi mai dadi Annie ce ta kalli Hakeem kana tace;"Mi kuka tattauna kaida dattijon gidan nan Allah yasa de ba maganar amsar kujerar Kamal sukayi maka ba, bana son akan ka a chanza tarihin gidan nan saboda d'an mace baya da gado ko kadan akan kujerar gidan nan Kuma Alhamdulillah ina gode ma da yasa bazaka gaji gidan nan ba saboda ban son ka da kujerar bana kaunar wani nawa ya gaji gidan nan a yanzu"

Kama hannun ta Hakeem yayi kana yace;"Ba maganar kujerar gidan nan mukayi dasu ba yanzu de kije ki huta zuwa anjima zamuyi maganar dake dan Allah ki kwantar da hankalin ki"

"Taya zan kwantar da hankalina bayan nasan irin kiyayyar da Hajiya Zubaida da yaran ta ke maka tun kana yaro sannan gashi yanzu wannan matsalar ta kunno kai kaga abin zaiyi tsanani kiyayyar zata k'aru Hakeem ina son ka fahimta ne Imran kayi mashi bayani mana"

Su duka kama hannun ta sukayi kana suka aza kan su bisa kafafun ta, Hakan  yasa tayi Shiru tana shafa kan su tana sabke ajiyar zuciya mai sauti.
Sun dauki wani dan lokaci kana Hakeem ya tashi yace;"Annie nasan komi fa ki kwantar da hankalin ki komi zai zama dai-dai insha Allah"

"To naji ina son kaje part din Hajiya ka fadama abinda ke faruwa"

"Abba Muktar yace nabar komi a hannun shi sai ranar Friday shizai warware komi"

Ajiyar zuciya ta sabke kana tace;"To shikenan amman ban tunanin ina iya hakurin sai nan da sati daya kana zasuji komi"

Imran yace;"Dan Allah Annie ki kwantar da hankalin ki insha Allah ba abinda suka isa suyi mashi"

"Nasani Imran amman hankalina ya kasa kwanciya ne na kasa natsuwa"

"Kada ki damu mu jira kana"

"Okay to shikenan kuje ku huta hakanan"

"To"
Suka amsa su duka kana suka tashi sukabar Annie cikin jimami Hanah ce tayi Sallama Annie ta amsa mata tana kauda damuwar dake bisa fuskarta.
Kama hannun ta Hanah tayi tace;"Annie idan ina ganin damuwar a fuskar ki ban jin dadi saboda nasan yadda damuwa take da ciwo "

Hanah ta fada cikin sanyin jikina tare da sabke ajiyar zuciya.

"Hanah taya  keda kananun shekaru kice man kin san yadda damuwa take, Kamar Iman ta fadaman ke kade ce a wajen Baban ki ya haifa Hanah iyayen ki na son ki sosai ban tunanin kinada wata matsala a duniya sannan a shekarun ki bai dace ki saka wata matsala a cikin ranki ba"

Sadda kai tayi k'asa tana murza hannun ta cikin kankanin lokaci hawaye suka taru a gurbin idanun ta.
"Hanah mike damun ki ne?"

Share guntayen hawayen ta tayi tace;"Babu komi Annie"

"To shikenan naji amman ina son ki cire abinda ke damun ki kinji saka damuwa a zuciya bashi bane zaiyi mana maganin abinda ke damun muba, kiyi kokarin mantawa da abinda ke damun ki kinji"

"To shikenan Annie kema ka cire damuwar nan taki ina son naga kina walwal kamar koda yaushe"

"To shikenan bari naje naga ya jikin Abubakar yake yau ban dubo shiba sai yanzu na tuna"

"To shikenan Annie sai kin dawo"

Daki Hanah ta koma ta kwanta bisa gado tana kallon rufin dakin.

Iman ce ta shigo tana Sallama amman Hanah bata dago ba saboda bata jita ba saida Iman ta matso ta bubbuge ta kana tayi firgigi ta tashi!.

"Hanah tashi muyi magana"

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now