ZAFI BIYU

21 1 0
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou
Page_9

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Yadda Hanah ke nuna Nanny cikin tsanin tashin hankali zakayi tunanin taga wani abinda zai cutar da rayuwarta ne saboda ilahirin jikin ta kyarma yake harta d'an yatsanta da take nuni nashi,  Duk wanda ya ganta  zaiyi tunanin dodo ta gani hadda zufa ke bin fuskar ta, Da kyat ta dai-dai ta kanta ta samu ta fidda maganar dake a bakin ta.
"Mummy miyasa zaki man haka miyasa zaki kawo man wannan matar Mummy kubar nan bana son ziyarta ku kuma daga yau inde da ita zaki zo to kibar shi na yafe bana so nace please ku fita!"

Juya tayi ta nufi hanyar dakin su Annie dake tsaye tace;"Hanah dakata mana"

Jin muryar Annie yasa ta tsaya tare da juya masu baya.

"Zonan waje na"

Hanah ta juyo tazo inda Annie take ta tsaya tare da sanda kanta a k'asa dan bata son kallon inda Nanny din take.

"Hajiya bari na jira ki a waje" Nanny ta fada tana juyawa.
Tabe baki Hanah tayi tare da jan dogon tsoki mai sauti yadda Nanny din zataji.

"To Maimuna nagode"

Sai lokacin ta kalli Mom din ta kana tace;"Mummy nide ki tafi ban so"

"Kiyi hakuri Hanah mun fito da Nanny din ki ne saboda daukar kaya munje munyi siyayya ne shine nace mu biyo"

"To miyasa Mummy bazata zauna a mota ba tunda kin san bana son ganin koda fuskarta ne"

"Kayan da nakawo maki ne ta dauko ta shigo dashi tunda kinga babu yadda za'ayi driver ya dauko kaya ya shigo dasu saboda nan gidan mutane ne bai dace Namiji ya shigo ba kiyi hakuri kinji kin san bana son b'acin ranki"

Sai a lokacin ta dan saki ranta kana tazo inda Mummy din take tsaye ta kama ta tare da zaunar da ita kwanciya tayi jikin ta tace;"Mummy I miss you so much"

"Same to me My Princess "

Ta fada tana goge mata wasu guntayen hawaye dake makale a idanun ta.

"Sarkin yan kwalliya kinga kin bata kwalliyar taki kuma kila Sirikina akayi mawa"

Rufe fuska ta tayi tace;"Annie kingani tana sakani ina jin kunya ko"

"Ohh Annie dan Allah Kiyi hakuri bamu gaisaba diyar taki ce akwai rigima duk ta rikitani ne"

Annie;"Babu komi Hajiya  ya gida"

Mummy;"Lapia kalau ya dawainiya"

Annie;"A'a babu komi ai an zama daya"

Mummy;"Muna godiya sosai Dad din ta ma yace ayi maku godiya"

Annie;"Babu komi bari na baku waje ku gaisa"

Laure ce ta shigo dauke da tray ta aje gaban Mummy tace;"Yau de naga Mummy din Hanah kullun labarin ta Mummy Mummy de"

"Ahhh kece Laure ai itama kullun Labarin ta Annie Inna Laure sannun ya gida"

"Lapia kalau"

"Mummy inajin dadin zama da Inna Laure Annie tace zata muyasan ya man ku bata Nanny ta baku Inna Laure please Mummy kada kice a'a ko five months tayi man"

Dan Shiru Mummy ta tayi kana tayi yake tace;"To shikenan Naji dadi sosai Inna Laure yadda kike kula da Hanah nagode"

"Ahh babu komi ai"

Daga haka ta mike Mummy din Hanah ta bata kudi masu dan yawa tayi mata godiya ta amsa tabar su nan.
Sun dan dade suna fira kana Mummy din Hanah tace;"Bari naje kinga Bro din kin zaizo Birthday din ki gobe yace zaizo"

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now