ZAFIE BIYU

23 0 0
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page_4

Masu Complain akan rashin post kullun kuyi hakuri yanzu ai aka fara zaku same shi a kullun insha Allah, Maganar kuma kada na wahalar da Beedah sosai kodan cikin jikin ta ba dagani bane daga Labarin ne Nagode🙏

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Dafe kaina nayi da duka hannaye na saboda yadda yake man ciwo baki daya na kure tunanina amman na kasa tuna ina ne yake a cikin State din nan, Runtse idona nayi ko zan tuna wani abu amman nakasa, Duka hannaye na nasa ina  bugun kai na dan ya tuna wani abu amman saima tunanin ya tsaya waje daya kwalwata tabar aiki.

"Malama lapiar kide?"

Bude idona nayi a hankali kana nace;"Ka taimaka man bazan iya tuna komi ba game da wannan garuruwan daka ambata man"

"Tab lallai kam kinada aiki Babba zakije k'asar da baki taba zuwa ba sannan ace ko sunan Jahar da zaki baki sani ba to taya zaki ga wanda kike nema?"

A jiyar zuciya na sabke ina kara runtse ido na koda zan tuna wani abu, Saurin bude idona nayi tare da cewa;"Yawwa na tuna Mom din shi ta kira shi da Prince kenan kaga shi prince ne"

Hawaye ne suka zuboman na dadi saboda na tuna abinda zai taimake ni wajen ganin Baban Baby na.

Dariya Maimashin din nan ya fashe da ita yana kallo na.
Kallon shi nake cikin mamaki ina tunanin miyake ma dariya kuma.

"Prince a Arewa cin Nigeria ai ba daya bane kuma kowa ai ana iya kiran shi da Prince Uwa zata iya kiran d'an ta da Prince"

Bata fuska nayi ganin ya maidani kamar wata marar kai kana nace;"Amman shi ai Prince ne sunada Kingdom ai ya fadaman"

"Idan suna da Kingdom duk garuruwan nan dana lissafa maki sunada Kingdom's bayan su kuma akwai wasu jahohin da yawa a Arewa da suma sunada Kingdom's"

Shiru nayi ina taba cikin jikina baki daya tausayin abinda ke ciki na ya kamani amman de zanyi kokarin nema mashi Baban shi koda zan rasa raina.

Ganin yana niyyar tada mashin din shi yasa nayi saurin rike mashin din nace;"Ka taimaka man ka kaini Nigeria"

"Yarinya nan ma ai kin shigo Nigeria kusa kike da Legos"

"Ina nufin wajen Hausa"

Shiru yayi yana nazari sai chan yace;"Ohhh na tuna akwai wasu kungiyar yan Bara Hausawa ne sun dawo   Bara daga Ghana yanzu gida zasu zan kaiki cikin su saiki bisu Hausawa ne amman cikin su akwai masu jin French kadan saboda suna zama Cotonou ki shiga cikin su zan kaiki ga shugabar su"

Murmushi nayi nace;"Nagode"

Godiya nayi ma Allah saboda wahala ta ta kare Daga yau.

Dauka ta yayi da mashin din shi mukayi tayi mai d'an tsayi kana muka iske wasu mutane duk mata ne kuma mafi yawa tsaffi ne sunkai su ashirin.

"Sannun ku ina wunin ku"

Maimashin dina ya fada yana gyara parking din shi.

"Lapia kalau Tukur  kanada sako ne"

"A'a Babah Indo, Ga bakuwa na kawo maku gida zata itama saide bata jin Hausa saide French"

Kallo na Babah Indo tayi da alama itace Shugabar su tace;"Kai tana iya zuwa Kano a haka kalli fa abinda ke jikin ta kuma mu ai tafiyar mu munayi muna tsayawa a hanya mu kwana biyu saboda wasu wuraren muna tsayawa mu k'ara nema kada ta zamo man kaya fa kuma kaga nima ta kaina nake yi"

ZAFI BIYU Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon