ZAFI BIYU

35 1 0
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou
Page_12

YA ALLAH KA GAFARTAMA IYAYEN MU DA KAKAN NIN MU DA MALAMAN MU...AMEEN 🤲

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION ✍️

Bisaimillahir Rahmanir Rahim.

Tamkar matattu haka Hakeem da Imran suka kasan ce a tsaye sai kallon Doctor sukeyi su duka suna jiran isowar shi.
Dai-dai lokacin da Doctor zai iso a gaban Hakeem Kamal yayi saurin shiga gaban Hakeem tare da tura shi baya, Cikin sauri Annie ta riko shi ganin kamar zai fadi.

"Doctor nasan kasan nine yaron Sheikh Abbakar so dani ya kamata kayi magana ina son ka fadaman minene ya faru da Abbana guba aka saka mashi ko?"

Kamal ya rike Doctor yana maganar tamkar wani zararre.

"Kamal inaga ku muje office muyi magana zaifi kaga nan mutane na giftawa"

"Hakane Kamal muje office"

Annie ta fada tana riko mashi hannu da sigar lallashi.

Wani kallo Kamal yayi mata kana ya ture ta yace;"Ya isa haka munafuk......"

Marin da yaji a fuskar shi ne yasa maganar ta kasa ida fita.

Cikin tsananin mamaki yake kallon Hakeem da shima shi yake kallo.

"Imran ko Hakeem wanene ya mare shi?"

Annie ta fada cikin tsananin tashin hankali, Mutane ne suka fara giftawa wajen hakan yasa Doctor yace;"Kuyi hakuri dan Allah ban son mutane su fahimci halin da ake ciki saboda idan suka fahimta yan Jarida na iya zuwa kuma kunga nan Hosp......"

"Malam ya isa haka bani son dogon bayani Marin da akaman zan rama koba yanzu ba yanzude fadaman ya Abba yake"

Sai lokacin ya kalli Imran yace;"Ku kuma bani da lokacin ku yanzu amman zanyi lokacin ku nan kadan sai kunyi nadamar zuwan ku a duniya"

"Abban ka saide......"

✨✨✨✨✨✨

Hanah dake kwance tayi saurin Mikewa daga bisan gadon su daukar karamin mayafi tayi kana ta fito parlon Annie taga ba kowa bata tsaya ba tayi hanyar fita tana fitowa daga gidan Annie nan ta fara cin karo da mutanen gidan duk inda ta gifta da kallo ake bin ta harta isa bakin babban get din gidan wanda daga shi zaka fita waje.

Zufa ne take bin gefen fuskar ta sai maida numfashi take saboda ba laifi daga gidan Annie akwai tafiya sosai zuwa bakin get saboda Annie itace karshe.

Dafa bango tayi kana ta fita daga cikin gidan nan ma mutane ta iske wasu suna zaune bakin Masallacin gidan wasu kuma suna harkar gaban su.

Adai-daita Sahu ne ya tsaya a gaban ta kana wani matashi ya leko yace;"Hajiya ina zaki?"

Bata tsaya bashi amsa ba tayi saurin shiga cikin Adai-daitar tare da cewa;"Wash...!"

Bigewa tayi a kai saboda bata iya shigar taba yau itace rana ta farko data fara shigar ta kana ta dago a wahalce tace;"Nasarawa zamuje"

"To shikenan Hajiya"

Tana zaune a baya kanta a kasa har suka isa unguwar su kana yace;"Hajiya wane Layi?"

Nan ta fara nuna mashi Layin su har akazo kofar gidan su kana ta sabka ta nufi bakin get din Security's din dake kofar gidan su suka fara gaidata bata tsaya amsa ba tasa kai zata shiga, Jin ana kiran ta da karfi kuma muryar Mai Adai-daita yasa ta juya.

"Hajiya baki ban kudin ba"

Lumshe ido tayi tana rike inda ta biye sai a lokacin tayi tunanin ashe ana biyan su fa.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now