MAKANTAR ZUCI!

17 1 0
                                    

MAKANTAR ZUCI!

🌟✨🌟✨🌟✨🌟
*_TAURARI BIYAR!!! 2022_*
🌟✨🌟✨🌟✨🌟

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
____________________

_EPISODE 2_

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Tsananin tashin hankalin da nake ciki yasa naji tsoron ma ya fita raina wajen Audu na nufa a guje tare da dago shi nace;"Audu! Audu! Bude idanun ka ga abinci nan na samo maka kaji kalli kaga hadda kwan da kake so"

Audu shiru ko motsi bayayi haka nake girgiza shi amman baya motsi.

"Malama bani abinci na barauniya kawai"

Mutane kallon shi sukayi ganin halin da muke ciki amman yana maganar abinci, Kabir daya daga cikin samarin unguwar mu hadda shi tsaye yace;"Haba kaiko bawan Allah baka tausaya mata Satar data yi maka saboda rayuwar Kaninta ne yarinyar nan tana da kokari tun kamin ta kai haka take kula da Kanen nan nata gashi yanzu har sun girma amman tunda muke dasu ban tabajin ance tayi Sata ba sai yau, Gidan su kusan su sha hudu ne kuma kusan kowa da Uwar sa sannan suke cida kan"

Wani dake tsaye yace;"To ina Baban su da Maman su"

Kabir yace;"Ai Baban su auri saki gare shi tunda ya auri Uwar su aka mashi hankali yanzu ya dena saide fa bai zama saboda Driver Tirela ne kullun yana hanya haka zaije ya dawo bako naira sun kare ga mata ga matar shi dake zaune dashi bata da Imani da kowa fada take a Unguwar nan bata da abokin arziki, Maman su kuma tun Audu yana da Shekara daya suka rabu tabar mashi yaran bata kara dawowa ba haka suke rayuwa wasu almajiran ma sunfi su galihu shi kuma Uban su Malam Idie ko a jikin shi"

"Tofa wannan laifin Uba kona Uwa?"

Wani dake tsaye ya fada Duk wanda ke wajen daga mai zagin Baban mu sai mai zagin Mahaifiyar mu nide bata su nike ba taya Audu zai mike nake.

Wanda na daukar ma Abinci ya nufo idan nike cikin azama, Wanda na zubama Indomie a jiki ya fito da sauri daga cikin mota ya tsaida shi baice mashi komi ba ya dauki kudi ya mika mashi da hannu yayi mashi alamar yabar wajen.

Shi kuma ya koma motar driver din shi ya tada sukabar wajen.

Audu ya bude ido a hankali yace;"Ummu ruwa!"

Waige-waige na fara ina zan samu ruwa sai naga anmiko man ruwan Roba na amsa cikin sauri na fara ba Audu yasha kana ya tashi nan na fara bashi abincin yaci kadan yace;"Ummu kema ki ci mana"

"A'a Audu kaci ni zan samu wani zuwa anjima"

Matashin saurayin nan dake aiki pharmacy din da muke gefe shine ya bamu ruwa yace;"Ga kudi nan ki boye Mukhtar Alie yaba ku"

"Mukhtar Alie kuma?"

"Eh wanda kika zubama Indomie a jiki"

Zaro ido nayi shine na jiya wanda na fashe ma glass din mota.

Amsa nayi nace;"Mungode"

Miko man leda yayi yace;"Wannan gashi maganin Audu ne yasha yanzu idan ya gama cin abinci sai kuma anjima da daddare zaiji karfin jikin shi kubar zama da yunwa kunji, yanzu kuzo muje kuci abinci akwai wajen saida abinci nan kusa"

"To shikenan mungode"

"Tare da shi muka je wajen cin abuncin ya sai mana Shinkafa da Miya hadda naman kaza😋

Munci sosai saida muka koshi kana yaban kudin yau a gefen zanena na kulle kana fa muka nufi hanyar gida hankali kwance.

Muna isa muka isa Baba ya dawo yau kwanan Tara kenan baya gida ya tashi kudu kai Albasa.

"Lah Baba yaushe kadawo?"

Kallon da yayi mamu ne yasa nayi shiru muka fara rabewa ga bango.

"Zonan munafuka wannan yarinya da iya munafurci take kamar Uwarta, Ina isowa aka fara mani maganar wai nabarku da yunwa har kinfara Bara a titi saboda kina so ki tona mani asirin gida ko?"

Ya jawoni tare da murde mani kunne.

Baban mu yana da wani abu guda daya bani kade ce bai so ba kusan duk matan gidan nan bai son mu dole tasa yake zaune damu wai baison yara mata yafi son yara maza saboda abinda yake aikatawa akwai lokacin da naji yana magana da abokin shi driver a zaure yace;"Kasan bani kaunar a haifaman diya mace saboda ance idan kayi Zina diyar wani za'ayi da taka ko ba'ayi da diyar kaba cikin zuri'ar kade sai anyi da wata shiyasa ban son yara mata ko kadan banki ida anhaifo suba su mutu a huta"

A lokacin ban san minene yake nufi ba sai a yanzu.

Hakan yasa yanzu ni kade ya jawo banda Audu nikade zai buga banda Audu saboda shi Namiji ne, Wasu lokuttan idan ya matsamana har kuka nake ina cewa miyasa ni ba'ayi ni namiji ba? Shiyasa sauran duk sun koma gidan iyayen su mata saboda matsin Baba daga ni sai Samira itama Samira saboda wajen Mamatar take yasa batabar gidan ba kuma wata na gaba ake bikin ta ni kade zan rage kenan.

Wata kara nayi jin yadda Baba ya murde mani kunne nace;"Baba kayi hakuri yunwa mukeji shiyasa muka fita nema"

"To Wallahi bari kiji bazaki zubar man da mutunci naba a idon jama'a gara ki mutu da yunwa da zubar da mutunci Daga yau ko kofar gida kika taka saina dandake kafafun ki kina jina ko?"

Daga mashi kai nayi ina hawaye.

"Munafukar banza duk halin dana shiga ba Uwar ki taja man ba dana san ke za'a haifoman aida ban aure taba"

Sai a lokacin Inna dake zaune tana yanka alaiyahu tace;"Ai lokacin kwadai ya kaika kai kaga Jar fata yanzu ai gashi nan kana dana sani ta tsallake tabar ka da wahala ga wahalar yara gata dangi bakai kade ba har mu ta shafa saboda ita yanzu ga Samira nan saide Limamin Unguwa ya daura mata aure haka za'ayi bikin ta babu dangin Uba ni tsoro nake ma kada dangin Mijin ta su sani suyi mata gori, Haba wannan aure ko bakin aure babu wani alheri a ciki sai yara data tutsato kuma ta jefar dasu"

"Hmmm kede bari ai kullun cikin nadama nike harmade idan naga yaran nan sun gifta"

Daki mun na nufa na zauna kusa da jikar mu ta kaya.

Hawaye nake son yi amman sunki fitowa shekarata Shabiyu kenan Audu nada Goma da watanni shekara daya da wata biyar ke tsakani mu hakan yasa kan mu daya yanzu ma Audu yana so ya fini girma saboda shi namiji ne a cikin Shekarun nan ban taba samun soyayya ba banma san taba hakan yasa nima ban jin kaunar kowa a zuciyata sai Audu.

Kudina na dauko ina kallo fuskar Mukhtar Alie nake gani a ciki tambaya ce nayi ma kaina nace;"Wai shi kurma ne? Ban tabajin yayi magana ba, Ayyah Allah sarki kila kurma ne, Daman ance mutun tara ne bai cika goma ba Allah ya bashi kyau da kudi amman baya magana"

Audu bacci yake a gefen jikina hakan yasa yasa naki motsawa dan kada ya tashi kudin kawai nake kallo na kasa dauke ido saboda fuskar wanda aka kira Mukhtar Alie nake gani.

Jin motsi yasa nayi saurin saka kudin cikin jikar kayan mu.

Yaya Sabi'u ne ya shigo cikin dakin kallo na yayi da idanun shi jajaye yana tafiya kamar zai fado mana yace;"Kai dallah ku tashi kuba mutane waje bacci zanyi"

"Yaya Sabi'u Audu bacci yake baida lafiya ya sha magani ne"

"Audu dan gwal ne dallah Malama ku fita kona tattakaku"

Tashi nayi nabar Audu saboda baccin da yake yi.

Ina bakin kofar dakin mu naga hayaki na fitowa daga dakin, Cikin sauri na shiga ina shiga na iske Yaya Sabi'u ne ke shaye-shaye gaban shi kuma sabbbin kudi zaro ido nayi tare da kara gwale idanuna naga lallai kudin mu nida Audu wanda akaban.

Wani Ihu ne nayi wanda har makwabtan mu saida suka jiyo ni.

MARYAM ANKUDIE {Qurrah}

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now