ZAFI BIYU

26 1 2
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION✍️

Page_3

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

"Wayyo Allah na naga takaina ni Beelah shikenan rayuwata ta kare akan Naira dari biyu"
Duk mutanan dake wajen nan babu wanda ya damu dani ko kallon mu basa yi bare nayi tunanin zasu taimaka man.

"Ya Allah ka taimake ni na isa cikin tsakiyar Nigeria da ciki na lapia duk abinda zai saman bana son ya sami cikin dake jikina"
A fili nake wannan zancen baki daya jikina sai kyarma yake sai kara zaro idanuwa nane da ka ganni kasan banda gaskiya.
Hannu daya yasa ya makare man wuya tare da dagani sama ya miko man hannu alamun na bashi kudi.
Girgiza kai nake alamun babu, Wasu hawaye ne suka zubo man masu zafi da ciwo ba komi yasa ni yin wannan hawayen ba sai d'ana dake ciki ina son cikin jikina fiye da yadda nake son kai bana fatan wani abu ya same shi  koda komi zai sameni bana son ya samu cikin jikina.
Babu bakin magana sai hawayen dake zubomani ina son nayi ihu koda wani zaiji tausayi na amman babu Daman yin haka saboda makoshi ya rike.

Hawaye ne ke zubo man kamar ruwa saboda ina ganin mutuwa tazo, kallon shi nake ina nuna mashi cikin jikina, Amman yaki fahimta sai kara bude mani manyan idanun shi yake tare da yiman yaren da ban fahimta, duk hawayen dake zuba basu saka shi ya sakeni ba sai ma k'ara wasu  magan ganu yake cikin yaren shi amman nasan komi yake cewa  bazai rasa nasaba da cewa zai kashe ni ba akan dari biyu.
Tun ina ganin mutane har na dena nabar numfashi.

Farkawa nayi na ganni a bakin hanya kwance a kasa, Firgigi nayi na tashi tare da taba cikin jikina naji yana nan ajiyar zuciya na sabke inama Allah godiya,

Tashi nayi nama rasa ina zan nufa kallon mutane na tsaya yi ina kallon yadda kowa ke harkar gaban shi ni ba tare daya kula d'an uwan shi ba.

Zama kawai nayi na fara bin kowa da kallo maganar matar nan ta dawo man;"Yan kasar ku nada banbanci da namu"
Nazari na fara yi shi su Hausawa idan aka haihu babu aure wani abune? To minene aibun inde mutum yasan d'an shi ne kuma ai na farko kuskure ne, Wai hadda tambayar ni musulma ce mtsss a fili nace;"Inde saboda wannan mak'arar da wannan katon yayi man yasa tace kada nazo Nigeria ai dama bata fada ba aikin banza tunda cikina na nan kuma inada rayuwa abinda wannan mutunan yayi man bazai hanani zuwa wajen Baban yaro naba, Kuma ma ai laifi nane duk abinda yayi man ai ni Naja tunda na hana mashi kudin motar shi"

Mikewa nayi zan chanza waje ganin babu ko mai kama da Baban Baby na.

Wani tunani yazo man nace a fili;"Shin waima nan ne yankin Hausawan?"

Wani mai mashin ne yazo ya tsaya inda nake ya fara alwala har zai tafi sai nayi mashi Sallama cikin yare na nace;"Dan Allah nan ne yankin Hausawa?"

Dan kallo na ya tsaya yana yi kana yace;"Tab yarinya kinada aiki Babba nan kudancin Nigeria ne Hausawa kuma na zama Arewa cin Nigeria nima daga chan nake nema ya kawo ni anan amman wane gari zaki Katsina ko Kano ko Sokoto ko Kaduna ko Bauchi?"

Yau ne rana ta farko dana fara jin wadan nan garuruwan dan ni a tunani na waje daya Hausawa suke to inane garin su Baban Baby???

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Hakeem! Hakeem! Hakeem"

Duk wanda ke wajen sunan dayake kira kenan.

Murmushi yayi ya sabko su duka suka sabko suna dariya saboda wasa ne Shahed yace;"Tab lallai Hakeem ka bani mamaki ai ban tunanin ka iya haka ba"

Kamal ne ya sabka ko tsayawa bai yiba yayi gaba Imran na kiran shi yayi kamar bai jiba.

Su duka kowa ne nufar part din su yayi saboda yayi wanka dan duk zufa ta jike rigunan.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now