ZAFI BIYU

30 1 0
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

PAGE_11

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Mamaki tare da al'ajabi ne yasa kowa ya kasa motsi a wajen, Duk masifar Mahaifiyar shi amman yau takasa magana.
Rahama ce da ranta ya baci ganin kowa ya kasa daukar mataki yasa ta yunkurawa cikin zafin nama ta nufi inda Hanah take, Tana isa ta daga hannu ta kaiga fuskar Hanah.
Hanah na kallon ta amman bata  gusa daga inda take ba, Saima wani kallo da take bin su dashi na baku isa ba.

Hannu ta daga zata kai a fuskar Hanah taji an rike mata hannu daga baya.

Su duka mutanan dake wajen ne suka juya dan ganin wacece.

"Nanny!...ke...."

Bata ko kalli inda Hanah take ba tace;"Ko a mafarki kada ki kara tunanin Marin ta"

Tana rike da hannun Rahama tayi maganar cikin kallon ke wacece Rahama take kallon ta kana ta fizge hannun ta tare da tura Nanny din tayi k'asa kana tace;"Ke a suwa? Kin san ni ko wacece da har zaki taba hannun na to bari kiji ko a mafarki kema kada ki kara tunanin zaki rike hannun na ke har kin isa ki dakatar dani?"

A Yanzu hankalin Hanah da Annie basu wajen Rahama dake zuba suna wajen Nanny din Hanah.

Hannah kallon Nanny din ta takeyi babu ko kiftawa, idanun ta akan Nanny din ta suke amman zuciya tana wajen tunanin miyasa a koda yaushe matar nan tana tare da ita ta zame mata inuwa kara kallon ta take domin tabbacin itace ta dade haka kana ta kalli kowa a wajen ta juya tabar wajen.

Annie ce ta mikar da Nanny tana mata sannu tare da bin Hanah da kallo harta shige part din ta, Nanny din kuma tabi bayan ta.

Kamal ma juyawa yayi tare da nufar motar shi ya shiga yabar wajen a guje.

Hajiya Babba da inanun ta sukayi jawur saboda bacin rai tazo inda Annie take tsaye tace;"Wallahi idan d'ana wani abu ya same shi Wallahi kema saikin rasa naki"

Daga haka ta juya tabar wajen su Rahama suka bi bayan ta.

Sai a lokacin sauran mutanan gidan suka fara barin wajen.

Annie juyawa tayi tabar wajen cikin sauri tana zuwa ta shiga Mota sukabar gidan.

A hospital koda aka isa da Abba Abubakar baya koda numfashi saide likitoci suna kan shi kusan thirty minutes kenan amman babu Doctor din daya fito Hakeem da Imran sai Zirga-zirga sukeyi su duka babu wanda yayi ma wani magana kowa ne addu'a yake yi a cikin zuciyar shi.

Kamal ne ya shigo wajen tamkar anjefo shi.

Kallon shi su duka sukeyi kana Imran yayi karfin halin zuwa inda yake tsaye dan a tunanin Imran din rashin lafiyar Abban shine yasa shi cikin halin da suka ganshi yanzu.

✨✨✨
Hanah na isa daki ta iske Iman na karatun wani book fada tayi bisa gado.

"Lapia Hanah ko Sallama babu?"

Sallamar Nanny din su yasa Iman ta rabu da Hanah ta maida hankalin ta wajen Nanny din dake shigowa.

"Ahh Nanny sannu da zuwa lapia naga Hanah haka?"

"Ni kaina ban san mike faruwa ba amman gashi ki bata kice mata inji  Auntyn ta Nadiya tace kada ta fada ma Mummy din ta, ta zabi colour din da take so sannan tace ta bude wayar ta zasuyi magana"

"Ki maida mata kice bana so, Kuma kice daga yau idan zatayi man aike tasan wanda zata ba dan ba kowa ne hannun  zata ba abu ya kawo man ba na amsa sannan...."

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now