ZAFI BIYU

28 0 0
                                    

Zafi 2

Written by Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page 2

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Kallon dakin na shiga yi cikin tashin hankali miya faru dani ne a ina nake anan?
Ban kara shiga tashin hankali ba sai naga an chanza mani kaya wannan ai ba kaya na bane hasali ma ban taba saka irin su ba kayan atamfa ne amman ba irin dinkin muba wannan zane ne da Riga kallon kayan nashiga yi murza fuskata nake kode mafarkine lallai ba mafarki bane.

Mikewa nayi tare da sabkowa bisa karamin gadon da nake kwance a hankali na fara tafiya duk da ba karfi jikina lekawa nayi waje.

Karamin gida ne da daki biyu da wanda nake ciki da kuma wani daga chan hanyar kofar gidan.

Wata tsohuwa na hanga cikin lambun gidan dake dauke da shuke-shuke tana diban ganye.

Kallon gidan nayi na kasa ne amman anshare shi tas sai daukan ido yake ko ina a gidan a tsabtace.

Tsohuwar dake tsaye kamar tasan ana kallon ta ta dan waigo muka hada ido murmushi ta sakar man ni kuma na dukar da kaina ina addu'ar Allah yasa na iso cikin Nigeria.

Isowa tayi inda nake tsaye ta kamani muka fito tabarma ta shinfidaman bisa gadon karfen dake a kalkashin bishiya ta zaunar dani, Daki ta koma sai gata da pillow ta aza man tayi man alamar na kwanta kwanciya nayi ina nan ina tunani saigata da abinci.

Cikin sauri na amsa na faraci saida nagama kana najini na dawo dai-dai, Zan kwanta tayi saurin dagoni ta girgiza kai.

Alwala nayi ta shimfidaman abun Sallah na fara jero sallolin da suka kubce man, Saida na gama kana na zauna ina tunanin a ina nake nan?

Wata matashiyar budurwa ta shigo gidan rike da leda a hannu tana cin cingam, kallon ta nake sosai mai Abincin nan ce ta jiya.

Banyi magana ba saboda banga fuskar magana ba to idan ita ta temaki miyasa take halin ko in kula dani dan daga kallon fuskarta zaka gane bata da mutumci.

Sallama akayi suka amsa ina nan zaune matar nan nan ce datace man zataje Ghana zata maidani gida zaro ido nayi ita ta taimake ni kenan??.

Tab ai ban san lokacin dana zabura ba na mike nama manta banda lapia.

"Nasan zakiyi mamaki nina saka aka dauko ki jiya lokacin da zaki fadi daman neman ki mukaje yi na shirya na samo mana masu mashina zasu tsallaka mu zuwa Benin saboda..."

Kamin ta ida fadar haka nayi saurin katse ta;
"A'a babu inda zani minene yasa zaki shigan man rayuwa ni Nigeria zanje ki kyaleni ban son taimakon ki ko zan mutu saina ida shiga Nigeria komi zai faru dani koda zan  rasa raina"

Ga mamaki duk magan ganun da nake gaya mata ranta bai baci ba saima murmushi dake a fuskarta.

"Bari kiji ban shiga rayuwar mutane kema abinda yasa na shiga taki saboda ke yarinya ce sannan bakijin yaren su zaki wahala sosai kuma hadda cikin dake jikin ki yasa nake tausaya maki"

"Naji dadi nagode tunda na fito gida ke kade kika tausaya man amman bazan koma ba"

"Miyasa kike da kafiya ne irin ku wahala suke sosai bani number Baban ki ko Maman ki na kira"

Kallon gidan na farayi ina tunanin ta ina zan rabu da matar nan.

Marata na dafe kana nace mata zan zagaya bandaki.

Wani waje aka gwada man na nufi wajen saida na kai kofar shiga toilet din kana na waigo na hade hannaye na nayima tsohuwar nan godiya murmushi tayi kana na shiga.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now