ZAFI BIYU

31 0 0
                                    

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page_6

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

UQUBA...!

Zagayeni sukayi ganin haka yasa na saki Doyar dake a hannu na, Zanyi magana Babah Indo ta damki wuyan riga ta tace;"Bani kudina da kika sata"

"Sata?

Na maimaita cikin tsananin mamaki da tashin hankali tare da kokarin ture hannun ta.

"Ohhh tambaya ma kike kenan wallahi ki fiddo mani kudina ko kuma keda  abinda ke cikin ki kutafi lahira"

"Wallahi ban dauka ba"

Na fada hawaye na zuba lokaci guda zuciya ta ta fara harbawa ganin yadda suka zagayeni gashi babu wanda ya damu da mu, Mutane sai harkar gaban su suke.

"Tun da muke zuwa Bara a Qungiyar mu ba'a taba sata ba sai yanzu da kika shigo cikin mu sannan ke kade kika san inda na aje su abu na biyu kuma kinman haka saboda jiya na hana maki kudin da Alhajin nan ya bamu shine kika bi dare kika dauke man kudi to bari kiji ba ruwana da abinda ke cikin ki kode ki fiddo mani kudi ko kuma yanzu muyi maki bugun da saikin fiddo su"

Kuka na aza ina rantsuwa akan ban dauka ba amman Babah Indo idanun ta sun rufe.

"Ku bin ciketa kuyi mata zindir saita fiddo kudin nan, Ana tabani kudin da na samu yau suka fado"

"Iyye kungani sun fara fita ko hadda siyan su Doya da kwai da kudina"

"Haba Babah Indo akan titi muke fa kuma mace ce taya za'a mata zindir muje ko wani Shago mu samu mana"

"Dakatah! Hanne kibar shigar man sabga dan ba kudin ki bane aka sace wata nawa ina wahalar neman kudi ace dare daya wata katuwar banza ta dauke su to bari kiji anan nake so ayi mata Zindir a zazzage komi nata"

"Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un"

Hanne ta fada tana runtse ido tare da juya baya tabar wajen.

Ganin suna niyar cire man kaya yasa na fara ihu ina neman dauki amman babu wanda ya kawo man dauki.
Duka karfina na saka ina kiciniya dasu amman Ina!! Bani da karfin da zan iya hana su.
Kawai saina barma su suyi abinda zasuyi saboda bani da karfin hana su nayi iyakar yina.
Runtse ido nayi tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare inajin yadda wasu ke yakushi na wasu kuma na buguna ana cikin haka naji za'a cire man riga sun riga Daman da sun kwance zane na rigar ce hannu na yake rike da ita saboda cikina nake  karewa.
Nan suka fara kokarin cire hannu na amman naki saki ganin haka Babah Indo dake tsaye tana huci yasa ta saka k'afa ta nushi cikin Nawa.

Wata irin azaba naji wadda tun da nake ban taba jin irin taba hakan yasa na saki wani Ihu da Dukkan karfina da murya ta tare da bude jajayen idanuwana ina kallon Babah Indo dake tsaye tana hushi.

A wannan lokacin ina son nayi kuka mai sauti amman nakasa saboda bugun da Babah Indo tayi man a ciki yasa duka jikina ya saki sannan ga wani irin zafi da nakejin cikin nayi ji nake cikin kamar yana juyawa.

Faduwa nayi k'asa Dummm!! Kaina ya bugu cikina kuma sai kara juyawa yake.
Ina a kwance basu barni ba naji suna lalubata zasu cire mani riga amman ban iya hanawa saboda ko yatsana bana iya dagawa.
Hawaye suke zubar man ta gefen idanuna suna zuba kasa.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now