MAKANTAR ZUCI!

24 0 2
                                    

MAKANTAR ZUCI!

WB_MARYAM_ANKUDIE {QURRAH}
                    

🌟✨🌟✨🌟✨🌟
*_FIVE STARS !!! 2022_*
🌟✨🌟✨🌟✨🌟

https://chat.whatsapp.com/JogcoXUveJmHqX6UA6YT2R

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
____________________

_EPISODE 3_

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Ba 'yan gidan mu ba hatta makwabtan mu saida suka shigo dakin da nake ciki saboda karar da nayi.

Kwance nake bani ko motsin kirki Baba da sauran mutanen gidan da makwabta suka shigo dakin, Ihun da nayi ne ya tada Audu dake bacci a firgi ce!.

"Malam Idie yarinyar nan bata motsi mu kamata mu kaita hospital mana"

Baba yayi saurin cewa;"A'a inaga Iskane(Jinni) suka bugeta dama tana da su idan suka tashi haka suke mata"

Audu yazo wajena inda nake kwance jin abinda Baba yace yasa yace;"Baba  ba gaskiya bane Ummu bata da Aljanu bata taba haka ba ku taimaka muna a kaita asibiti kada ta mutu"

Nan Baba ya fara kame-kame yana sosa kai yace;"Ummm, Ummm inaga de Audu na baka fahim ce niba"

Nan Kabir yace;"Haba Malam Idie wannan ai rashin Imani ne taya yarinya na kwance bata motsi kace mana Jinni ne idan Jinni ne bari nayi mata Rukiyya"

Nan ya fara karanta Ayatulkursiyyu amman shiro babu inda ke motsi har ya gama.

"Kagani Malam Idie maganar Audu gaskiya ce bata da Jinni, Dan duk shedancinJinni idan aka karanta mashi Ayatul Kursiyu saiya motsa dan haka mu kaita Asibiti"

"Kabir bar wannan bayanin dan Idie bai san darajar d'a ba idan ta mutu ai ba ita kade ne dashi ba yana da fiye da goma dan haka wanda zai iya taimakawa to ko ashirin ashirin mu hada a kira Taxi mu kaita asibiti"

"To shikenan Babah Jummai nide ga Naira d'ari"

Nan aka fara kara-kara aka kira Taxi Babah Jummai da Audu suka shiga muka nufi Aminu Kano teaching hospital.

Bude ido nayi na ganni a daki mai rufi mai kyau kara bude su nayi dan nasan rufin dakin mu ba haka yake ba Iskan Fanka ne ya fara bugu na hakan ya bani tabbacin lallai kam ba'a gida nake ba tuna abinda ya faru dani nayi cikin sauri ko na tashi;"Audu kudin mu! Audu kudin mu"

Cikin sauri Jummai ta rike ni tace;"Dakata Ummu kwanta mana jikin ki ba karfi fadaman miyafaru, Dan Likita yace kina bukatar hutu razanar da kikayi saura kadan da zuciyar ki ta buga dan haka kwantar da hankalin ki ki fadaman minene akayi yasa ki razana?"

Nan na share hawayen dake bin fuskata na fada mata yadda akayi.

"To yanzu kwanta kinji bari naje gidan ku na iske Sabi'un zuwa anjima da yamma idan likitan ya shigo zai bamu sallama kwanta kinji"

"A'a Babah Jummai ki tafi dani naji sauki lafiya ta kalau"

"A'a sai Likiti ya sallame ki kiyi hakurin zuwa anjima bari naje na sami Baban ki"

Nan ta tafi ta barni shi kuma Audu sai bacci yake hadda Munshari saboda iskan Fanka ya bige shi.

Tashi nayi daga bisa gadon na maida Audu sama saboda yaji dadin baccin sannan na lullube shi da zanin gado nafito saboda inajin kishin ruwa.

Wani Fanto na hanga na nufi wajen na bude ruwa suka zubo na tara hannu ina sha.

A gefen wata Window Fanton yake cikin dakin naji sha-shaker kuka hakan yasa na dago.

Mata ukku ne a tsaye gaban wata budurwa ko matar aure Ohow, Gaba nane ya fadi ganin dayar matar wadda tace zata kira mani dan Santa itace kusa da wata dattijuwa suna ma marar lafiyar fada tsaye nayi ina kallon su.

Wadda na rotse masu Motar glass tace ma wadda kanta na kasa tana shashaker kuka;"Wallahi kiji wajen bokon da kika kai sunan Mukhtar ya karya asirin da kikai mashi na kin kara aure ko kuma keda zama cikin mu har abada kada ki manta a Jawara ya aure ki ba'a Budurwa ba kin san miyasa Hajiyar mu tabar shi ya aure ki yana Saurayi ya auri Jawara"

Wadda aka kira da Hajiya tace;"Saboda ina son ganin jika da wuri ganin shi wanchan da kike so watan ku Tara kika haifa mashi yaro auren ku keda Mukhtar shekara Biyar kenan ko b'ari baki taba yiba kuma likitoci sun tabbatar man da yaro na yanada lafiya, Ganin wani gidan kin haihu nayi tunanin nanma zaki haihu ashe nan baki shirya hada zuri'a da muba kika shigo cikin mu sannan duk lokacin da nayi ma d'ana maganar aure to sai munyi sabani babu abinda ya tsana kamar kayi mashi maganar aure saboda kin shanye shi to baki isa ba ni ina son ganin jikina ban hana ya zauna dake ba dan haka kema Kada ki hana shi zama da wata"

Suna gama fadin haka suka juya sukabar ta tana kuka.

Duk halin da nake ciki na bacewar kudi na hakan bai hanani tausaya mata b dan kuka take mai sauti wanda duk mai Imani ya ganta saiya ji tausayin ta.

Gaf! Aka bude kofar dakin aka shigo.

"Mukhtar Alie!.."

Na fada bakina yana kyarma to matar shi ko Kanwar shi maida hankali nayi wajen su.

Yana zuwa yayi inda take zaune zai rungume ta tayi saurin daga mashi hannu;"Mukhtar ya isa haka! Kada ka tabani idan har kana sona kayi aure saboda ka haihu Hajiya ta kasa fahimtar ban sha komi ba dan kada nayi ciki sun kasa fahimtar Allah ne bai kawo ba"

Cikin tsawa yace;"Bazan yi aure ba saboda bazan iya son wata diya mace ba a duniya bayan ke"

"A'a Mukhtar hakan zai cutar dani"

Zuwa yayi ya kama kafadun ta duka biyun kana yayi magana cikin zafin rai yace;"Har bada bazan yi aure ba  ki rubuta ki aje babu wadda zan iya so dan haka kada ki karaman maganar aure idan ba haka ba...."

Ya fada yana sakin ta, tare da nunata da yatsa yana girgiza, daga haka ya juya ya fice yabar dakin.

Kuka ta saki mai sauti tare da girgiza kanta.

Daman Mukhtar Alie din nan mugu ne? Baida tausayi kenan? Koda yake haka Baba yake ma matan shi tsawa kenan ko wane namiji haka yake, Dangin shi sun gama yi mata shima yazo yayi mata.

Baki daya jikina ya saki tausayin ta ya cika mani duka zuciya ta tambayar kaina nikeyi kode inje in taimaka mata???

MARYAM ANKUDIE {QURRAH}

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 16, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now