Babi na 1

2K 188 15
                                    

👮🏾‍♂️ Binciken Sirri
(Labarin dake kunshe da cases na 'yan sanda da yanda suke gudanar da bincike)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

Page 1

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai!

Babban office ne wanda a fadin garin Kaduna shine babban officin 'yan sanda, wasu daga cikin ma'aikatan suna zaune akan kujerarsu tare da yin aikin da ke gabansu, wasu kuma daga gefe suna zaune suna hira da alama irin wadanda basa san aikin nan ne, daga can gefe kuma wani ne a kwance akan kujera yana ta tikar bacci, shima da alama irin mutanen nan ne malalata. Wani daga can gefe na hango, mutane biyu a gabansa su kadai ne ke sanye da kayan gida ba shakka zuwa sukai ko laifi sukai, suma magana kasa-kasa, namijin dake zaune kusa dashi ne ya dan mikamai kudi a boye, dan sandan ya kalli gefe da gefe ganin bamai kallansa ya dan sa hannu ta kasan tabirin gabansa yana neman amsar kudin.
Gyaran muryar da sukaji ne daga bakin kofa yasa gaba daya office din ya rikice, wannan na kwancen ne ya tiko daga kan kujera yana muzurai na masu bacci, tare da yin salute da hannunsa, suma masu hirar nan duk sun tarwatse kowa ya mike tsaye yana salute, shi kanshi mai shirin amsar kudin nan baisan sanda ya bige hannun mutumin ba hakan yasa kudin ya fadi a kasa, shima ya daga hannu yana hade kafafuwa.
Kallan mutumin daya shigo nai sanye da sun glasses, a hankali ya zare, kallanshi nai sanye yake da uniform din 'yan sanda, hannunsa ya sa a cikin aljihu ya harde kafa yana kallan kowa 'daya bayan 'daya.
Fuskarsa a d'aure take sosai, a hankali ya karaso ciki tafiyar isa da kasaita, nan fa kowa ya shiga sara mai, gaban mai bacin nan ya fara tsayawa wanda hakan yasa idanunsa firfitowa, hanayensa ya ciro daga aljihu ya gyaramai kwalar rigarsa da ta dan cude garin bacci, tare da dan bubuga kafadarsa, sannan ya nufi masu hirar nan ya dau biro din dake katsa ya nufi inda suke ya mikawa kowa daya, sannan ya nufi gun mutumin nan, kallansa yai sannan ya nuna masa kasan tabirin, idanunsa ne suka sake fitowa ya hadiye wani abu, da ido ya sake nuna masa kasan tabir din, tsugunawa yai ya dauko envelope din jikinsa na rawa yace "Alhaji ka yarda wannan abin a kasa."
Yana neman mikawa wannan mutumin dake sanye da kayan gida yaga an amshe, kallan juna sukai nan ya maida kansa kasa da sauri, bude envelope din yai nan hankalinsa ya sake tashi ya runtse idanunsa da karfi dan yasan shikenan ya gama yawo, mutumin da ke sanye da kayan gida ya mikawa sannan yace "Me ya kawoku?"
Nan danan mutumin ya dan hada hanayensa yace "Dan Allah ka taimaka min kawo kara nai sai dai banasan abin ya fito mutane suji."
Kallan officer din dake tsaye yai da sauri ya kara yin salute sannan yace "ACP Adnan dama 'yarsa ce akayiwa fya......"
Hannu ya dagamai sannan ya kalli mutumin yace "Okay, ka dan biyoni office dina." Nan jiki na bari shida matar nan suka bi bayanshi. Yana shiga lungun da office dinsa yake suka saki ajiyar zuciya a tare, kusa da mutumin nan wanda za'aba cin hanci suka taho, cikin tausayamai daya yace "Lalai ka shirya daukan punishment! Kaima me ya kaika amsar cin hanci a ciki? Ai sai kace ya biyoka waje ko kuma ya turama ta account." Nan danan zufa ta shiga ketomai ta ko ina, yasa hannu ya share yace "Ni wlh kullum a tsorace nake abu saboda wannan Mugyambo din(sunan da suka samai kenan in suna tare)"
Mai baccin nan yace "Ni Allah yasa a canzamai gun aiki, tunda ya fara aiki anan gaba daya bamuda kwanciyar hankali."
"Wlh na tsani Mugyambo din nan ji nake kamar na tareshi a lungu namai tsinanen duka, tunda ya zo na kasa yin arzikin danai daa yabi ya takura mana ya hanamu ansar hakkinmu, ai hakkinmu ne tunda taimako suke nema a wajenmu."
Nan kowa yai tsaki yana hararar office dinshi kafin su koma su zauna a gun zamansu.
*****
A office dinshi kuwa ACP Adnan ne ya zaune tare da kallan ma'auratan yace "Karar me kuka kawo?"
Uwar tana share kwallar data kasa daina zubo mata, shi kuma mahaifin cikin raunaniyar yace "Dan Allah ka taimaka mana, yarinyata 'yar shekara biyar yaran mutumin da nake yiwa gadi ya mata fyade, a kauyen mu suke wancan satin sukazo biki shine na roki alfarma akan zasu kwana a dan dakina, uban gidan nawa ya amince harma ya basu gun kwana a ciki wanda a nan ne ya samu ya illata mana ita, yanzu tana kwance a gadan asibiti, nakai kara police station din dake kusa damu amma an kasa daukan mataki saboda mahaifinsa mai kudi ne, kwana biyar ina binsu amma sunki daukan mataki, shine wani yaban shawarar zuwa nan in gwada sa'ata."
Dayake dama can fuskarsa a daure take shiyasa yanzun ma bazaka gane halin da yake ciki ba, wani file ya ya jawo dake kan tabir din ya fara rubuta bai ko sake magana ba sai can bayan yadanyi rubutu yace "Ya sunanka?"
Nan yace " Salau Garba."
Yarinyar ka fa? Raliya
Mutumin da kake kara fa?
Ya kalleshi yace "Nuhu Manumfashi!"
Bai dago ya kalleshi ba yace "Yaran Sani Manumfashi ne?"
Bakinsa na rawa yace "Eh."
Cigaba da rubutunsa yai jefi-jefi yana mai tambayoyi kafin ya gama, mikomai yai yasa hannu sannan ya rufe yace "Sannu da kokari! Yanzu ka koma gidanka."
Mamaki ne ya kamasu suka kalleshi a tare, sannan suka maimaita kalamansa "Mu koma gida?"
Kudin ya ciro ya mikamai yace "Ga wannan wlh saniyar da nake da ita a kauye ita kadai na saida, dan Allah ka taimakamin."
"Ni kuma kudin da ake ban duk karshen wata a matsayin me yake kenan?"
Ya dan hade hannayensa yace "ka koma gida insha Allahu komai zai daidaita."
Haka suka fito dan basuga fuskar yin magana ba, gaba daya ransu ba dadi suna fita waje matar ta sake fashewa da kuka tace "Wannan wace irin kasa ce? Ace ba wani na gari da zaiji tausayin mu? Da alama wannan yafi kowa wulakanci, shi bai amshi kudin ba bai kuma da niyar taimaka mana." Haka suka taho cikin sanyin jiki suka wuce asibiti inda aka kwantar da yarinyar.

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now