Babi na 6

409 80 7
                                    

Binciken Sirri...... 👮🏽
(Labarin dake kunshe da cases na 'yan sanda da yanda suke gudanar da bincike)
*TALAKA DA MAI KUDI*

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

https://arewabooks.com/chapter?id=62854a00ef85a63a21dda994

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

Page 6

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS

+447894142004

IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki

******
Adnan haryayi parking a kofar gidansu, karamin gida ne na masu rufin asiri, a hankali ya sa key dinsa ya bude gidan sannan ya shiga, babu alamun haske na kwan wuta hakan ya tabbatar mai da mutanen gidan sun kwanta, kitchen ya shiga ya dauko abincinsa sannan ya fito ya wuce dakinsa, sai dayai wanka yai sallah sannan ya zauna ya jawo abincin ya faraci, gaba daya fuskarsa haryanzu kamar dazu take ko ince haryanzu kamar yanda na saba ganinshi yake babu alamar fara'a a tattare dashi, har ya gama abincin yana dane-danen wayar sa, gaba ɗaya kwakwalwar sa ta kasa daina hangomai Mukhtar da Sani, uban me Muktar yaje yi? Yaji shi Sani yanada hujja tunda ɗan uwansa ne, amma shi Muktar fa? Gaba daya abinda ya daga mai hankali ko ina ka shiga a media magana ɗaya ce akan wata ta kashe mijinta a daren farkon auransu.
Zumbur naga ya mike zaune sannan ya ɗau key ɗin motar sa ya fito. Kai tsaye station ɗinsu ya nufa duk da baccin dake kanshi kuwa. Duk ma'aikatan dare sun baje sai sharar baccinsu sukeyi, a hankali ya shiga ciki dan dama jallabiya ce a jikinsa.
Kai tsaye ya nufi inda aka kulle amaryar nan, tana zaune ta kwantar da kanta a jikin bango babu alamar bacci a idanunta, ta kurawa kasa ido, ita kuma ba kuka take ba, cikin sanda ya bude kofar hakan yasa ta kalli inda yake, hannu ya daga ya mata alama data fito, ta ganeshi shiyasa batai mai musu ba ta mike ta fito, office dinsa ya nufa tana shiga ya sa key ya rufe.
Gaba daya gani yai jikinta yahau kyarma, tana ja da baya, cikin mamaki yake kallanta sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna ya mata alama data zauna itama, zama tai ta takure jikinta, kallanta yai haryanzu hannunta d'auke yake da jinin dazu, kafafunta babu takalmi.
Kai yadan kauda yana kallanta yace "Yanzu kin shirya magana?"
Kallansa tai sai dai batasan me zatace ba sai motsa baki kawai da tai, gaba daya ta rasa ina muryarta take dan ta kasa magana.
Ya dauko file ya bude ya kuma kunna recoding din wayarsa yace "Ke kika kashe mijinki?"
Ɗagowa tai ta kalleshi haryanzu ta kasa magana, "Okay, tunda kinyi shiru hakan na nuna kece kika kasheshi kenan, to fadamin bayan kinyi kisar me kikai?"
Nan ma shiru, ya kara jinjina kai yace "Okay na gane da kika kasheshi shine kika shiga lungu kika boye kar a ganki? Ko kuwa so kikai ki gudu baki samu dama ba? An ritsaki?"
Haryanzu batai bagana ba sai motsa lebe kawai da takeyi.
Dan desk din gabansa ya dan buga a hankali yana kallanta cikin fada kamar zai daketa yace "Ke ba musulma bace? Bakisan hukuncin kisa bane? Inhar bakya sanshi me yasa kika aureshi? San kudi da buri na duniya ko me? Ko kuwa dama can saboda ki kasheshi kika aureshi? Ko kuwa.........."
Hannu tasa ta rufe kunnuwanta kawai tana girgiza kai sai a lokacin ta fashe da wani wahalalen kuka tana girgiza kai tana cewa "Wallahi wallahi bani bace, ba ni bace wlh bani bace....." kuka ne yaci karfinta sosai ta zame daga kan kujerar tana dukan kirjinta da karfi tana wani irin kuka wanda duk wani mai imani inya saurareta sai ya tausaya mata.
Adnan ya danyi shiru yana kallanta, kuka take mai karfin gaske babu kuma alamar kukan nan zai kare nan kusa, idanunsa yadan runtse kadan sannan ya dake yace " Zaki iya fadamin takamai mai abinda kika sani?"
Ta bude baki a hankali tace "Ni dai nasan na shiga ya shigo hannunshi d'auke da nama to......."
Kamar wanda ta tuna wani abin sai ta mike da sauri cikin tsananin tsoro tace "Nice! Nice babu kowa nice."
Adnan ya mike yana neman yi mata magana kawai yaga ta nufi kofa tanata jijigawa, da sauri ya mike yana cewa "Menene?"
Daga waje kawai yajiyo muryar officer yana cewa "ACP ka bude, ga CP Muktar nan yazo."
Mamaki ya rufeshi ya dake ya bude kofar, me zai faru? Amaryar ce ta zube a kasa kawai tana kuka, Adnan yai wa Muktar salute kafin yai magana kawai yaji an sharara mai mari, kallansa yai sannan ya dake ya dauke idanunsa, Muktar ya kalli Auwal yamai umarni ya maidata cell sannan ya kalli Adnan yace "Me kake da ita a cikin office a kule?"
Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Adnan yace "Me nake kuwa? Bayan bincike? Interrogation nake ina san sanin meke faruwa."
Cikin fada yace "Kamin shiru ko sai nasa an cireka daga aikin ka gaba ɗaya?"
Bai jira mai zaice ba yace "Ka maidamu dakikai ne ko me? An taba kiran mai laifi cikin office sannan a kule? Sannan kai namiji ita mace?"
"Me kake san kace?"
Out! Abinda Muktar ya fada kenan yana nunamai hanyar waje, sannan ya cigaba "Akwai witnesses na abinda ka aikata sannan kasan hukuncin ɗan sandan daya nemi yin lalata da mai laifi."
Adnan kallansa yai kawai naga ya sa wata dariya wanda tunda nake ban taba ganinshi yana dariya haka ba, kallan Muktar yai sannan ya dan tafa hannayensa biyu sai kuma ya maida fuskarsa ya ɗaure yace "Bravo! That was really amazing, yau ka tabbatarmin dalilin dayasa ka zama CP at young age, sai dai ya za'ai? Wanda kuke tunanin yiwa illa shima a shirye yake."
Ya d'an sosa bayan kunnensa yana kallan cikin office din, Muktar cikin bacin rai ya kalli office din, Adnan ya koma cikin tsakiyar office din ya kalli sama kusa da celin inda wata ƴar kamera take kawo jan danger tana daukewa, sannan ya karasa saman table ya dan jingina yace "Surprise!"
Muktar ya fara wani huci sannan yace "How dare you talk to me like that."
Adnan bai koyi gizau ba ya ɗau wayarsa da take recording bai kashe ba yace "Sorry amma yau zan faɗi duk abinda ke raina, me kake tunani in mutane sukaji abinda ka aikata? Daga ganina a office sai zargi? Ko kana tunanin in na tura abinda ka aikata a sama baza'a ɗau mataki akanka ba?"
Muktar ya mai wani kallo, Adnan ya ɗan mike yace "Menene na shiga wannan case ɗin? Bayan sau nawa ana kawo karar kisa banga ka taba bi takai ba sai wannan? Sannan trap da kuke kokarin shiryamun fuk akan case din nan ne, me kuke ɓoyewa?"
A fusace Muktar ya daga mai hannu alamar ya dakata yace "Naji nayi kuskure na zarginga amms kada ka kuskura ka kara sakani a cikin wannan kisan, naje gidan jiya ne dan yin gaisuwa saboda nasan wanda ya rasu, sannan ina kara sanar dakai inhar kanaso ka cigaba da aikinka ka dinga sanin kalaman da zaka dinga fada....." yana kaiwa nan ya fita daga office ɗin cikin matukar bacin rai.
Adnan yai shiru yana kallan camera din daya nunawa Muktar wanda a zahiri ta dade da lalacewa, ya siyeta kwanakin banya sai daya saka yaga ashe fake ya siya, gashi danger na kawowa amma ba abinda takeyi. Haushi ya saka yaki cirewa yana fatan inya sake suyo wani sai ya maye gurbin wannan, bai taba tunanin wannan abin zai kwaceshi ba yau. Abinda yasa yake san sawa saboda sharrin da aka dingamai a station din daya zauna a baya, dawowar sa nan ya shirya hakan dan gudun samun matsala irin ta da.
Wannan abin da Muktar yai ya tabbatar mai tabbas akwai babban abu a kan kisan nan.
*****
Muktar kuwa yana fita ya shiga mota tare da sa kansa akan sityari, yanzu duk plan din nan daya hada ya tashi a banza?
Tunowa yai shine yasa duka masu aikin dare suyi pretending akan bacci sukeyi wai zasuga boyayen halin Adnan sai dai maganar gaskiya shi da Sani ne suka hada baki akan wannan shirin, Muktar yafi kowa sanin Adnan yakuma san tabbas sai ya dawo dan tunda yaga Muktar yasan zaiyi ta tunani ne akan akwai abinda suke ɓoyewa, sun shirya sosai akan zasumai sharri suce ai lalata ya nemi yi da ita sai dai wannan dan iskan yaran ya wargaza musu shiri, yanzu menene mafita? Agogo ya kalla karfe biyu na dare, yaja tsaki saboda takaicin shi baije gida ya kwanta ba gashi abinda suka shirya bai yiwu ba.
Wayarsa ya ɗauko ya kira Sani ya sanar dashi halin da akw ciki, ran Sani yayi matukar ɓaci yace "Wannan tsinaniyar yarinyar da take binshi fa? In shi baya san cin hanci ita ai zamu iya amfani da ita cikin sirri ko?"
Wannan maganar ta gamsar da Muktar yace "Shikenan yallabai nasan yanda zan bulowa abin" da haka sukai sallama.
Muktar yana zaune a mota har Adnan ya fito ya shiga motarsa ya wuce gida. Ya ɗanyi alamar bindiga da hannunsa ya saita motar Adnan yace "Bang!!!"

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now