Page 25

631 59 13
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

*Page 25

Nafeesah cike da tsoro ta sake cewa "Ummy yaushe ta rasu? Meya sameta? Ummy nashiga uku..."
Yawun bakinta ta had'iya sannan tace "Bamu da labari muma, amma yaushe ta rasu?"
Cike da jimami dan har idanunta sun fara canza launi ta gyara wayar dake kunnenta tace "Bansani ba wallahi yanzu Adnan ke maganar."
"Subhallah! Allah sarki Allah ya jikanta, yaushe zaki dawo yau?"
Idanunta na lumshe tace "Munzo ganin Hajiya Babba ne in mungama zan taho insha Allah."
Ummy ta sake jingina da kujera tace "To shikenan karki manta da maganinki."
To kawai tace ta kashe wayar, da kyar ta iya takowa, haka kawai takejin zuciyarta ta shiga wani yanayi ga hawaye na neman cigaba da zubowa. Gaba daya tunanin ta yaushe mahaifiyar Fiddausi ta rasu ba wanda yaji labari? Me takeyi ita kuma tsawon wannan shekarun ba tare da ta sani ba?
Tafi minti goma tana sake-sake a ranta kafin ta mike, ciki ta shiga.
******
Hajiya Babba ta jinjina kai tace "Nagode Adnan a gaskiya na fahimci duniyarnan in kayi dakyau zakaga dakyau, na gode da taimakon yarana da kukai."
Ta sake murmushin takaici tace "Tunda aka kulleni banda ku babu wanda yazo ganina bayan ada yan uwa kamar zasumun sijjada yanzu na fahimci duk na karyane."
Adnan baice komai ba ya hade hannayensa yana dan murzasu, shigowar Nafisah ne yasa ya dan kalli gefenta kadan yanayinta kaɗai daya kalla yasan akwai abinda ke damunta, hala tayi waya da kankarar tata ne sunyi faɗa shine zatashigo a haka, ɗauke kai yai kawai ya maidashi kan Hajiya Babba tare da cewa "Nima ba sake gani na zakiyi ba yanzu, shari'arku an maidata Abuja saboda Sani, dan haka zakuje can a gama a yanke muku hukunci sannan a dawo dake inda aka turaki."
Kai ta ɗaga tare da share kwallarta tace "Alhaki ne da hakki, gwara ma a yanke min hukuncin kisa dan rayuwarnan banaji zan iya ci gaba da yinta."
Shidai baice komai ba yana tsaye yana murza hannunsa, kafin daga bisani yasa ɗaya a aljihu, ya maida idanunsa kanta kafin yace "Sai kiyi ta hailala, mungode da taimakonki."
Abinda yace kenan ya ɗan kalli inda Nafeesah take "Ni na fita sai kin gama." Da kallo ta bishi menene inya jirata? Ko yace ta taho su tafi in ta gama? Ai bata gama wani dogon nazari ba yabar gun.
Kallan Hajiya Babba tai wacce ke ta zubar da hawaye tace "Mai afkuwa ta riga ta afku sai dai addu'a."
Kallanta tai tana hawaye tace "Allah ya miki albarka ke dashi, insha Allahu Allah zai kareku daga duk abin ki, nasan laifi nai ba lalai Allah ya amshi addu'a ta ba amma duk da haka bazan kasa yi muku ba na taimakon da kuka min."
Taananin tausayinta ne ya kama Nafeesah nan danan kuwa taji idanunta na neman canza kala, tabbas ita rayuwar nan ba a bakin komai take ba yanzu ina matar da take ji da kanta? Kai ta ɗan ɗauke tana share hawaye tare da yin murmushin karfin hali, tana dariyar dayafi kuka ciwo tace "Bakomai nagode."
A hankali Nafeesah ta jinjina kai sannan ta mata salama ta fito, jikinta ya kara wani mugun sanyin.

Adnan dake zaune a mota ya sake kallan wayar dake hannun motar wacce take ta kara, shi dai bazai ɗauka ba kuma karan ya fara damunshi na yadda ake kira akai-akai, ɗan hannu yasa ya ɗago wayar kaɗan fuskarsa a murtuke ya maida wayar tare da sake ɗaure fuska, in tasan bazasu iya rabuwa da juna ba sai ta dinga yawo da wayarta akan tazo ta takura mishi da karar ringing turn.
Kallan hanyar fitowa yai inda ya hangota ya ɗauke kai tare da ciro wayarsa yana dannawa, har ta karaso bai ɗagoba ta buɗe motar ta shigo tare da kallan inda yake meye ya wani ɗauke kai? Zama tai itama ba tare da tayi magana ba, shima yaki tada motar balle yaja su tafi sai ci gaba da danne-dannen sa na mota kawai da yakeyi.
Sunfi minti goma a haka ga wayarta dake ta kara, sai dai daga ta fara take maidata silent kafin daga bisani ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta sata a jakarta, shiru suka sake yi takaici ya rufeshi shi da motarshi shi zai kaita amma bazata ce mai ta dawo su wuce ba? Bayan ya sanar da ita zai jirata?
Ita kuwa Nafeesah ganin yana danne-danne yasa tai tunanin ko abu mai mahimmanci yake turawa tunda taimakonta akai aka kawota bai kamata tai gajen hakuri akan ta gaji ba.
Ganin da gaske batada niyyar yin magana yasa ya tada motar tare da janta da ɗan karfi, kai ta girgiza a ranta tace "Shi kaɗai ma zafin rai yake." Ta karasa maganar tana maida kanta gefen titi.
Gaba ɗaya duk sanda ta kalli hoton dake lankaye sai taji zuciyarta tayi sanyi, addu'a kawai take a ranta akan Allah ya sada ta da rahama.
Har suka isa ba wanda yai magana, ganin yanda yanayinsa yake yasa yana gama parking ɗin motar tace "Nagode." Ta karasa tare da buɗe kofar, bai tanka ba itama bata nemi ya bata amsa ba, kai tsaye ciki ta wuce jikinta duk ba kwari.
Da kallo ya bita shifa rainin wayau ne bayaso ko dan taga yana neman taimakonta na aiki ne yasa take mai abinda taga dama? Fitowa yai ya wuce ta ya shiga office ɗinsa.
Tana shiga ta tarada su Auwal anyi gang ana gulma, a ranta tace ai inda sano kun saba, yi tai kamar batasan me suke ba ta fara kokarin wucewa ta zauna, cike da san zance ya kalleta ya mata alama da hannu akan ta matso itama taji, kamar tace bazata ba sai kuma ta fasa ta karasa gun tana ɗan murza gwiwar hannunta, Auwal tana matsowa yace "Kinsan wanda yazo jiya?"
Da alamar mamaki a fuskarta tace "Wa kenan?"
Cikin alamun rada ya ɗan matso kaɗan yace "Deputy Inpector General fa Alhaji Lawal Yakasai."
Baki ta tab'e tace "Me zai mana to?"
Auwal ya girgiza kai yace "Ke da alama bakisan wanene hakan ba ko? Ko dayake dama kina yar karamar Corporal wake ta taki? To daga Inspector General na kasa sai shi. A can Abuja yake yana da iyali anan shiyasa ma kike ganin shi."
Kai ta gyada tace "Lalai to amma me ya kawo zancensa?"
Ghali cikin zumudi yace "Zancen matsayinshi da kwarjininshi muke, bakiga hirar da akai dashi ba? Wai ashe ya tura secret agent kan binciken Sani? Ashe tanan ne ma akasan shirye-shiryen sa, sannan shiyasa randa yazo yabi bayanshi dan yaga ba'a samu kwakwarar hujar da yake so a kama Sanin dashi ba." Ya karasa maganar yana nuna mata hirar a wayarshi. Wani murmushin takaici tai shidai bazai taɓa daina halinshi ba, wanda yai gwagwarmaya daban mai ɗaukan credit daban, a yaushe ya turo wani secret agent? Bayan har fada ya mata akan binciken?"
Kai kawai ta girgiza ta juya gun zamanta ita gaba ɗaya yanzu ba wannan bane a kanta tausayin Adnan ne yake damunta.
Har yan duty na dare sukazo bai fito daga office dinshi ba kowa ya tafi banda ita, sai wayancewa take da aiki ne ya tsaida ita.
Ganin da gaske bashi da niyyar fitowa yasa ta mike tana ɗan kallan office din, ta juya kenan ya buɗo kofar suka hada ido, da sauri ta juga wanda bata kula da tana daf da table ba sai ji tai ya table din ya bugi cikinta, daurewa tai dan tasan yana nuna alamu zai gane kallansa takeyi, waje tai da sauri tare da rataya jakarta ta nufi titi.
Mota ya shiga dan yana ganinta sanda ta gama jiranshi ta fito wato ga direban ta, tana tsaye yazo kusa da ita yai parking, kallanshi tai ta dan kauda kai, glasses din dake fuskarsa bai cire ba yace "Basai kin basar ba lift kike jira sai ki shigo a ajiyeki, sauri nake."
Waigowa tai shi dai duk yanda taso karta rama abinda yake mata bakin ciki baya hanata iya jurewa, tace "Adaidaita ma ta wadatar ga inda zan shiga iska na kadani."
Kai ya jinjina yace "Kumafa hakane at least jijigar da za'ai dake exercise ne."
Takaici ne ya rufeta zatai magana taga ya zuge glass, kai ta sake kaudawa ta harde hannu tace "Kamar nace dole a lalabani na shiga, ai dai in da kara ka sake min magana tunda kana ganin magriba tayi."
Sai kuma tabi motar sa da harara ai dai ko bai kai zuciba kace in shigo tayi na biyu wahala zai maka.
Adaidaita ta tare ta shiga tana babakewa tana cewa "Iskar adaidaita ai rahamace." Ta sake shafar fuskarta tana cewa "Ko ina shiga take."
Adnan kam ba gida yai ba gidan Sani Malumfashi ya nufa tun a hanya yake sauraran yanda ake ta sake sa hirar Alhaji Lawan Yakasai a radio." In da sabo manyan nan sun saba bazaka ga sun yarda akan sunyi kuskure ba su kullum sune da ɗaukan credit ai ta karramasu.
A kofar gidan yai parking daga waje ya wa mai gadi magana akan Nuhu da mahaifiyarsa.
Mai gadin ya sanar dashi ai tun safe akazo aka kwashesu kuma baisan inda suka tafi ba shima an sallameshi ance yabar aikin dan haka gobe zai tafi.
Bai wani yi mamaki ba dan ya tabbatar tunda abin ya hada da siyasa to fa sai dai Allah ya shirya.
  Gida ya wuce yana isa ya tadda Abba a waje tsakiyar mutane suna hira, fitowa yai ya gaishesu ai suna ganinshi suka sake fadada fara'a sai a lokacin ya gane su waye, ganin ya gaishesu yasa daya a cikinsu yace "Adnan kamar kasan zancen ka mukeyi sai gaka."
Zancena? Ya kallesu cikin yanayin mamaki.
Na kusa dashi yai dariya yace "Akan maganar auranku kai da Neerah ance kun daidaita ko?"
Kallan Abba dake tsaye yai baice komai ba, mutumin ya kalli na kusa dashi yace "Kaifa yanzu ka zama sirikin Acp sai ka fara ɗaukan uniform kana sawa kana zama a waje akan kujera mu kuma muna zuwa gaidakai."
Nan sukai dariya shidai baice musu komai ba, kallanshi ya sake yace "Tunda abin duk na kusa ne ai komai sai muyishi a tsakanin mu."
"In har ana aure ba miji kam ai bazai yi wuya ba ayishi ba tare da amincewa ba." Abinda yace kenan ya fara tafiya, Abba yasan halinshi hakan yasa ya kallesu yace "Kaima Aminu ka fiya surutu kana sane Kubrah tunzura ka takeyi ka jira ya amince mana kafin ka fara wannan maganar."
"Amma ko menene ya kamata yai min magana haka? Kaifa duk ka ɓata yaran nan gashinan duk ya raina mutane, tun da mahaifiyarsa da kanwarsa suka rasu yake ganin kowa da gefen ido, sannan ita Kubran ba kanwar mamansa bace? Ai ko dan darajarta ya girmamata, ko kuwa dole sai an haɗa uwa da uba ake zama ya da kanwa?"
Mahmud wanda yake mahaifi ne ga Muneerah ya dafa shi yace "Kasan dai komai a sanu-sanu akeyi ka daina tilasta abubuwa zamanin mu nada dana yanzu ba ɗaya bane, wani sa'in sai an kai zuciya nesa."
Adnan kam shiga ciki yai rataye da jakarsa, Kubrah tana zaume ita da Muneerah suna hira daga tsakar gida kana juyo shewarsu da alama labarin da suke ya musu dadi.
Kai kawai ya girgiza ya wuce part dinshi, wanka yai tare da alwala ya zauna yana hailala lafin isha'i tai ya wuce masallaci.
Addu'a yake sosai akan mutanen da suka rigamu gidan gaskiya....

********
Duk yanda taso tai bacci ta kasa sai juye kawai take a kan gado, gaba ɗaya ta cukwikwiye bargon da bedsheets din saboda motsin da take tayi, mikewa tai ta fito da niyyar ɗauko ruwa a kitchen tasha.
"Wayyo aljani dan Allah ban shirya haukacewa ba kar ka aureni dan Allah ka barni nai aure na hayayafa, wayo....." Toshe mata baki Nafeesah tai nan ta gantsara wa hannun cizo tana neman sake yin wani ihun, takaici ya kama da zafin ciwo ta saketa da sauri tana neman makunan wutar corridor din.
Barira kam gudu kawai ta saka sai data kusa shiga ɗakinta Nafeesah ta kunna wutar tare da cewa "Allah Barira kinci bashin cizon nan." Ta karasa tare da zuwa inda take da alama ma batasan me take ba, gani tai tana neman cire wando kuma, saman goshinta ta shafa itafa Barira lamarinta sai a hankali, jijigata tai tace "Naga randa zaki daina wannan magagin baccin." Tai maganar tana janta ɗakinta tai toilet da ita, tana fara fitsari ta ɗebo ruwa ta shafa mata, firgigit Barira ta sake zabura tace "Aljani...."
"Barira Allah zan miki duka in baki bari ba."
Kallan Nafeesah tai wacce tace "Aunty me kike a banɗaki?"
Kai kawai ta girgiza ya fito, ita abinda ke damunta daban ita kuma Barira na neman kona mata rai babu gaira babu dalili.
Ruwa ta ɗauka ta koma ɗaki ta kwanta, ya za'ai tasan meya samu Maman Fiddausi har ta rasu ba wanda ya sani? Wannan tambayar sai sake yawo take mata a kanta, a haka dai bacci ya ɗauketa....
*****
Dady ne ya kalli Ummy wace ke magana, gaba ɗaya yanayinsa ne ya canza yace "Kin nuna mata kinsani?"
Ajiyar zuciya tai tace "A'a sai dai tsoro nake akan zata sani tunda aikin nan tare sukeyi dashi."
Iska ya furzar yace "Bansan ya akai nai saurin yi mata alkawari akan shekara ɗaya ba dan tunda ta fara aikin nan banida kwanciyar hankali."
Kai ta jinjina tana kallansa tace "Ni kaina banida kwanciyar hankali tsoro nake kar kafin shekarar nan ta kare abinda muke ɓoyewa ta sani dan na tabbatar in ta sani ciwonta in bamuyi wasa ba dawowa zaiyi."
Fuskarsa ya shafa da hannu biyu nima na shafi nawa fuskar na fito.

(Muna novel na free dan farin cikin ku, amma in mukai na kudi dayawa basa kara su siya, wanda hakan yake nuna mana cewa masoyan namu san littafan mu a baki yake.)
GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA ƊAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)

ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

KATIN WAYA
+234 706 528 3730

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 21, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now