Babi na 12

557 80 10
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*TALAKA DA MAI KUDI*

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

https://arewabooks.com/chapter?id=62854a00ef85a63a21dda994

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

*Naji Korafi sosai sannan korafi ya karɓu insha Allahu zaku dinga jina akai-akai! Banyi alkawarin kullum ba amma insha Allahu zakuga canji.*

Page 12

Mikewa yai a kan gado ya ɗaura hannunsa saman goshinsa, a hankali wata ƴar karamar iska ta fito daga bakinshi, anya ba shine ya jawowa yarinyar nan ciwo ba? Daga zuwanta ya takura mata yanata sata aiki? Aikin ma mai wahala, tuno yanayin daya ganta dazu yai, dan juyi yai a kan gadan ya jawo pillow yai sake kwantar da kansa.
Knocking din dayaji ne yasa yabi kofar da kallo, a hankali ya mike ya buɗe kofar bai ko tambayai wanene ba, dan baimasan ranshi ya baci.
Wacce yake tunani da wacce ya gani ba ɗaya bane.
"Adnan mekake aikatawa agun aikin ka?"
Kallan matar yai dan shi sam baima kawo ita zai gani ba ya ɗauka kanwarta ce, fuskarsa a haɗe yace "Ma'aikacin aikin ƴan sanda mai zai aikata in ba kama masu laifi da hukuntasu ba?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta mikamai flask din abincinsa ya amsa yana kallanta, kafin yace "Nagode."
Zai juya tace "To wayar da akawa babanka dazu kuma a matsayin me take?"
Kallan mamaki ya mata tare da ɗan gyara tsayuwarsa yana rike da kofar "Waya?" Ya tambaya yana sake binta da kallo.
"Bansan ya akai suka samu number dinsa ba amma ɗazu sun kirashi akan ya maka gargadi ka fita daga hanyar case ɗin nan, Amarya ta kashe mijinta ranar daran farko basa san wasu kananun maganganu."
"Waye ya kira?"
"Bansan waye ba sai dai ka tuna mahaifinka ya damu dakai tunda harda ka shigo bai sanar dakai ba saboda bayasan ɓacin ranka."
"Kenan ba da saninshi kika zo sanar dani ba?"
Dan kallan gefe tai tace "Banasan na dinga ganinku haka ne, taya kuna ɗa da uba amma......."
Maida kofarsa yai ya rufe kawai bai jira ta karasa ba, komawa yai ya ajiye abincin akan table sannan ya zauna a bakin gado tare da dafa kansa, waye ya kira Babanshi? Lalai mutanen nan tunda har suka san number mahaifinshi to fa ba abinda bazasu aikata ba.
Hannayensa ya haɗe yana tunanin abinda ya kamata yai musu inhar yana san family dinsa su tsira da mutuncinsu, yarinyarce ta fado masa.
Wayarsa ya jawo ya nemo sunan dayai saving din Nafeesah dashi.
_Ya jikin?_ kai ya girgiza da sauri ya goge, ya dan shafi kanshi ya sake rubuta
_In kinsan bazaki iya aikin nan ba...._ gogewa yai da sauri, ya sake rubuta
_Da alama na saki aiki dayawa..._ gogewa yai kawai ya dan kifa wayar kan gado tare da mikewa kawai ya shiga toilet.

******
Washe gari da safe ya fita kamar yanda ya saba, yana shiga station dinsu ya wuce cell din daya kulle Garba, kallansa yai sannan ya maida cell din ya rufe, ciki ya shiga yana ɗan tafiya a hankali shi kuma Garba duk ya kara rikicewa ya tsuguna yana kallan Adnan tare da haɗe hannayensa yace "Sir dan Allah ka taimakeni ka sallameni wallahi in mahaifiyata taji halin da nake ciki mutuwa zatai."
Tsugunawa yai kusa dashi yace "Kenan Sani bazai kula da ita ba?"
Lebansa na kasa wanda ya bushe ya lasa yace "Ni kaɗai ne ɗanta namiji dan Allah kayi hakuri, zan ba Zaliha hakuri zansa ko marinane ni wallahi ko duka nane in tanaso tayi."
Kai ya jinjina yace "Good! Sai dai ni ba wannan bane ya kawo ni, me Sani yace maka ranar a mota? Sannan me kake dashi akansa wanda har yake baka kuɗi dan karka fadawa wani? Naji matan Marigayi sunsa kawa Zaliha abinda ka mata sai dai Sani fa?"
Kasa yai da kansa yana rike hannayensa, Adnan ya mike yace "Ba matsala karka damu akwai number mamanka a wayarka da muka kwace zan sanar da ita halin da ake ciki da abinda ka aikata tazo tai bailing ka."
Kafafun Adnan ya riko da sauri yace "Wallahi bansan komai ba, ka taimakawa rayuwata karka sanar da ita, ni kawai na taɓa ganinshi ne shi da...."
Sai kuma yai shiru yana tunanin inya faɗa anya bazai jawo masa matsalar datafi wannan ba? Dan Sani ya sanar mai in har ya fadi wani abu to ko mahaifiyarsa bazai sake gani ba."
Kai ya girgiza da sauri yace "Officer dan Allah ka yafemin na tuba dan Allah."
Kwace kafarsa yai ya fito, kusa da cell dinsu Zaliha ya tsaya sannan ya bude ya kalli Goggo wace ke kwance akan kulin kayanta tana ta wani sauke numfashi kai kace mara lafiya ce."
Yana daga tsaye yace "Malam zaka iya fitowa?"
Da sauri ya mike yace "Ai dole nane na fito, Allah dai yasa gida zani?"
Yana mikewa Goggo tai wuff ta mike itama tare da rugowa da gudu har ta riga Malam zuwa bakin kofa."
Kallansu yai ya girgiza kai sannan ya basu hanya suka fito ya nuna musu inda zasu zauna.
Idanunsa ya maida kan Zaliha dake rakube a bango yace "Inhar asiri bai tuno kafin a shiga kuto nan da kwana uku ba bansan ya zakiyi ba, ke ba bailing ki akai ba, sannan ni a ganina ma zamanki anan kafin a shiga kuton shine rufin asirinki, babbar matsalar itace in kuka shiga kuti alkalai zasu naima su basu kudi wanda babu yanda zakiyi, dan haka ki dage da addu'a nan da kwana biyu Allah ya tona asirinsu kafin ayi transfer dinki."
Idanunta ne suka ɗan fara tara kwalla ta ɗaga kai tace "Nagode." Nan ya maida kofar ya rufe.
Bin bayan su Goggo yai wanda suka zauna akan kujera sai murmushin jin dadi takeyi.
Zama yai a sit din Nafeesa ya jawo file din daya ajiye ya kallesu, yace "Kun samu wani yayi bailing dinku, sai kuma na tausayawa yaran da kuka bari a gida."
Goggo ta sa dariya tace "Kai masha Allah! Gaskiya mungode sosai ahh kwanan nan ko kwanan masifa mu bada kisa ba muda kwana a nan?"
Fuskarsa data kalla ne yasata yin shiru ta dan kauda kai, kai ya girgiza cike da takaicin kalamanta yace "Kuma ki kira kanki da uwa ko?"
Bata amsa ba dan itakam tsoron maganar da za'a kara turata ciki takeyi. Wato san zuciya irin na dan adam yanada yawa, bama su damu da waye yai bailing su ba balle yar da suka haifa.
Adnan ya girgiza kai ya kalli Malam yace "In ita batasan abinda ya kamata ba kai a matsayinka na mahaifi ai ka sani, in kunsan bazaku kula da yara ba ku daina tarasu."
Malam ya dan yi murmushin ya ke yace "Ayi hakuri tayi magana ne amma ba har zuci ba."
Rubutu ya farayi ba tare da ya kulasu ba, sai daya gama ya kalleshi ya mika mai number wayarsa a wata takarda yace "Duk sanda Gambo ya dawo kauye ka kirani da number nan ka sanar dani, sannan in har wani ya sake zuwa zai baku kudi shima ka kirani ka sanar dani, basai na fada ba kunsan abinda zan aikata inhar bakubi abinda nace ba, sannan na rokeku da Allah ku kula da ƴayanku."
Ya maida kallansa kan Auwal yace "Ka sallamesu."
Office dinshi ya wuce yana shiga wayar office dinsa na kara? Da alama ba wannan bane kiran farko, karasawa yai ya ɗauka, ya kara a kunnensa dan yasan wanene.
"Adnan me kake nufi da sakon da ka aikomin? Kaine mahaifin Nafeesah ko kuwa a karkashinka kaɗai take aiki?"
Bai amsa mai ba, takaici ya kama Muktar yace "Ina ka kaita? Ko ince ina ka turata? Inka ɓatamin rai wallahi zan maka babban hukunci."
"CP nifa yarinyarnan ba ni na turata aiki ba kaine ka turata aiki dan jiya naga sanda ta fito daga office dinka, na mata magana tace kaine ka sata aiki,
sannan iyayenta sun min waya suna nemanta nima dolene na turama sako akan ka dawo musu da ƴar su. Kaine wanda ya ganta na karshe dan haka zan sanar musu.
Gabanshi ne ya faɗi ina ta shiga? Ya katse wayar tare da mikewa daga kan kujera. Sunyi da ita zasu hadu amma fa shi bai ganta ba haka ya karashi zamansa ya tafi gida shida yazo shan hidima sai jan kafarsa yai ya bar gun.
Nan fa ya hau safa da marwa yana haɗe hannayensa ya zaiyi in ba'a ganta ba? Badai Sani bane yasa a kamata to ai shi ce mata yai karta bari Adnan yasan shi takewa aiki garin ya ta sanar da shi?
Kanshi gaba ɗaya ya kulle sai sake kiran wayarta yake amma ba'a ɗauka....

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now