Babi na 11

477 79 9
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*TALAKA DA MAI KUDI*

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

https://arewabooks.com/chapter?id=62854a00ef85a63a21dda994

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

Page 11

Suna fita Zinaru ta kalleta suka sake shekewa da dariya, Hajiya Babba ta daki kafafunta tace "Bazaki bari ba?"
Zama tai tana kallanta tace "Yanzu ya kukeyi? Ga gida kullum a cike? Na tabbatar ya matsu yaganki."
Murmushi tai tana sake amsar juice dinta tana sha tace "Abin sirri ne, barshi yai ta missing dina hakan ne zaisa ya kara kauna ta."
"Inyeeee! Gaskiya kuna kara'i soyayyar da bakuyi ba kuna yara shi kuke morewa yanzu."

Nafeesah kam gaba daya komawa tai lum ta kwanta ta rasa yanda zatai ta tashi ta fita, gashi ba dama ta fito daga bayan gadan saboda suna nan a zaune a dakin.
Wayarta ta zaro a hankali ta turawa Adnan sako akan tana dakin Hajiya Babba kuma ba damar ta fito.
Yana waje lokacin ya saka Garba a mota da ankwa zasu wuce kenan lokacin da sakonta ya shigo wayarsa, shiru yai yana tunanin abinyi, ga Garba a bayan mota yana tsoron inya barshi zai iya gudu ga kuma Nafeesa a ciki.
Ya danyi tunanin sakan ashirin kafin ya bude motar sa ya shiga, sako ya rubuta mata ina zuwa in 20minute.
Garba ne ya katseshi ya dauka ya tura sakon ashe bai tura ba, yana kuka yace "Yallabai na rokeka da Allah ka sakeni wlh ni ne gatan iyayena in aka kuleni bansan halin da zasu shiga ba."
A zuciye ya fincike motar suka hau kan hanya, Garba nata kallan Sani Malumfashi amma sam ko kallan inda yake baiga yayi ba.
Ganin ba haza ya sa ya kara kaimi gun rokon Adnan yana hada hannayensa, sai da suka isa station ya taka birki da karfi wanda yasa shi razana.
Juyowa yai a fusace ya bude mota ya cakumo shi yana mai kallan bacin rai "Hakuri? Kasan da haka kai abinda kai? Ina imaninka yake? Kasan me ka aikata da har kake da bakin magana? A kawo yarinya amarya....."
Yai shiru ya kasa karasawa saboda takaici ya dan tura shi tare da sakinshi yai dan kwafa, nan da nan Garba ya zube a kasa tare da hade hannayensa yana murzasu yace "Wallahi Oga ba laifina bane, ban taba zina ba sai a ranar, shima kudi aka biyani dayawa idona ya rufe saboda inasan gyarawa mahaifiyata dakinta da yake zubar ruwa da damuna, wlh nima ba'a san raina nai ba."
Wuce my shiga ciki ka kuma tabbatar ka maimaita kalamanka in ba haka ba kai kadai abin zai shafa wadanda suka sakaka ba abinda zai samesu."
Ya ka mo kafafuwan Adnan yace "In na faɗa fa? Za'a barni na tafi."
Fizge kafafunsa yai ya tasashi a gaba suka shiga ciki, suna zuwa ya sashi a dayan cell din dake kusa danasu Zaliha ya kulle bai tsaya wani abu ba ya fito.
Auwal yana ganin abinda ya faru ya ruga office din Muktar ya sanar dashi halin da ake ciki, nan danan ya fito a fusace ya fara kiran sunan Adnan sai dai baya station din.
Yana hucci ya koma office dinsa ya dau wayarsa, sako ya tura Sani Malumfashi akan kar ya damu shi zai san abinda zaiyi.
Zaliha yasa aka kira mai office dinshi bayan yasa Auwal ya kori duka ma'aikatan dake ciki.

*******
Nafeesah kam tun tana dauriya har idanunta suka fara lumshewa dan dama ba dadi take ji ba gashi bata sha maganinta ba, ga kuma yunwa da ta dinga cinta, ta jira Adnan har ta ajiye wayarta.
Zinnaru kuwa da Hajiya Babba sai da suka gama shagalinsu sannan suka bude kofa nan fa Hajiya Babba ta koma ta narke akan gado tana jan numfashi tana share kwalla.
Kowa sai tausaya mata yake, matar Sani Malumfashi wato mahaifiyar Nuhu ta zo gaisuwa anan ta sanar da ita Nuhu na hanya zai dawo.
Hajiya Babba cikin dauriya tace "In ya dawo kina ganin ba matsala?"
"Case din gidanku yasa an manta da laifin sa sannan shima bazai iya zama a garin da aka kaishi ba. Ya saba da nan."
Sama-sama Nafeesah taji wannan maganar dan haka bata gane duka maganganunsu ba.
Adnan ya dawo Sani na ganin motarshi ya maida hankalinshi gun mutane haka kawai ya samu kansa da wani irin faduwar gaba, badai Garba ya sanar dashi wani abin ba? Karfa yaran nan yazo cikin mutane ya dizgashi? Gashi yanzu siyasar sa ta fara karfi baya san ko kadan wani abu ya kawo mai matsala.
Sai dayaga Adnan ya shiga gate din gidan sannan ya saki wata ajiyar zuciya yana kauda kansa, tabbas bazai iya da wannan fargabar ba saboda wani dan karamin yaro dole yasan abinyi.
Secretary dinsa ya kalla yace "Tashi kaje ka binciko gidan su yaran nan ka dubo waye ubansa, tun kafin Nuhu ya dawo gwara naiwa tufkar hanci." Ya mai maganar cikin rada nan ya mike cikin hanzari yavar gun.

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now