Babi na 23

271 61 5
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

*Page 23*

Sani masifa kawai yake da zage-zage a cikin mota sai dai sam Adnan bai tanka shi ba har sai da suka isa police station, fito dashi yai yana tirjewa kafin yaja tsaki yace "Kai wai shashashan ina ne? Baka gajiya da kawoni ana budeni?"
Murmushi yai yace "Wannan karan ka shigo kenan."
Waya ya dauka ya kira abokinshi dake aiki a BBC a gaban Sani yasa a hands free yace "Bello kasan da suka dau Sani Malumfashi sakinshi sukai ya koma gidanshi? Sai kawai gashi da daddare yayi shigar burtu yazo gidana sata?"
Sata?
Ya kalli Sani da yace "A gidan ubanwa nai sata? Zuwa kawai nai muyi magana."
Murmushi yai yace "Bello kana jinsa? Gashinan na sake kamoshi saboda cin hancin daya kawo gidana."
Bello yace "Gobe da safe zamuzo ai hira dakai akan case din yanzu zan watsa labarai."
Ya kashe yace "Zaka shiga ko kuwa? Gashidai yanzu labarinka zai watsu da dumi-dumi."
Wani mugun kallo yamai yace "Adnan haryanzu kai yarone, mu zuba mu gani ni kuma nace gobe zan bar nan. Ko bakasan wanda yazo jiya ba?"
"Bansanshi ba kuma bandamu dana sanshi ba kowa aikinshi yake."
Haka Sani ya wuce ciki yana irga sau nawa wannan dan iskan yaran ya kamoshi lalai wannan karan shima sai inda karfinshi ya kare dole ya tozartashi.

Haka aka rufe Sani, a zaune ya kwana yana tunanin abinda zaiwa Adnan mafi muni wanda zai sashi nadama.
.........

Adnan sai wajen 5 ya koma gida haka ya shiga offive dinsa kawai ya zauna a kujera ba tare da ya kunna wuta ba yana sake tuno abinda ya faru a baya, mikin dake kwance ya sake tashi, haka ya mike ya fito, wanka kawai yai ya sake fitowa.
Carko carko ya tada su sunyi da yake yasan dalili bai tsaya ba ya fara neman yin hanyar office dinshi.
A fusace Muktar yace "ACP mahaukata kake san maidamu ko kuwa wanda basu san me suke ba? Yaushe aka saki mutumin nan da zaka sake dawo dashi? Are you out of your mind?"
"An sakeshi ne saboda Ba evidence akanshi yanzu kuwa akwai evidence mai karfi da bai isa ya musa ba."
Wani mugun kallo yamai yace "I need you in mu office."
Bin bayanshi Adnan yai yana shiga yai salute, Muktar ya daga kafa ya makamai a kafarsa, duk da zafin da yaji.
Hannu ya mika mai yace "Bani evidence din."
Adnan ya kalleshi yace "Am sorry but na tura kadan daga ciki gun yan jarida ragowar sai a kuto."
"What?"
Adnan yana kallanshi yace "Babu law din dayace in na samo shaida dole na baka."
Mari ya zabgamai ya nunashi da yatsa yace "Ka manta discipline din ka ne harni zakawa magana haka?"
Shiru yai baice komai ba, ka tattara takardunka you are fired! Zan sa a tura takardar sallamarka."
"Okay!" Abinda yace kenan yana neman fita, Muktar yace "In ka dawo da abin zan maidaka aikinka."
Bai juyo ba yace "Zan tura ragowar gidan tv ka shirya kaima da alama zaka ajiye aikinka."
Jin kalaman Adnan yasa ya rikoshi da sauri yace "Me kake nufi? Kana san cewa shaidar har dani ta kunsa?"
Kai ya daga yace "Na cire part dinka ne sai dai yanzu no need."
Yawun bakinsa ya hadiya yace "Mu biyu ne so maganar korar dana ma ba sai kowa yaji ba."
Adnan ya kalleshi ya daga alamar eh sannan ya sake neman fita.
Da sauri ya sake cewa "Amma part dina kayi alkawari bazaka ba kowa ba?"
Kai ya daga alamar eh yace "Eh in na bada ma mutuncin mu ne zai zube nima banasan haka."
Ya washe baki da dariya yace "Yauwa Adnan nagode."
Fitowa yai ya kalli offive din ido suka hada da Nafeesa wacce tunda ta shigo taga abinda ya faru akace yana office din Muktar ta zubawa office din ido, tana gani sun hada ido ta dauke nata idan ta dau file da sauri, yana shiga tabi bayanshi tare da rufe kofar.
Kallansa tai tace "Meke faruwa ACP?"
Saman goshinsa ya shafa yace "Rainane ya baci sai da na je gida nasan nayi gaggawa, so ba yanda zanyi dole nabi wata hanyar."
Ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajiya Babba zataga bakani alkawarinku ba."
Ya dan hade hanayensa yace "Jiya da daddadare na samu munyi waya da yaranta yasai ticket zasu tafi yau da daddare ashe sunada visa na kasar bansan ya akai idona ya rufe ba jiya."
Cikin magana a hankali tace "Ai dama jiya neman fada kake...."
"Zagi na kikai?"
Kallansa tai tace "Ni?"
Ya kalli file din hannunta yace "Menene?"
Kallan file din tai dan bata ma san me ta dauko ba, da sauri ta girgiza kai.
Hannu ya mika mata tare da daga gira.
Ido ta runtse kafin ta mikamai, ya amsa ya bude file din bama nata bane wani case ne na sata da akai last week.
Kallanta yai yace "Signing zanyi?"
Ta daga kai alamr eh. Ya jinjina kai yana cewa "Case din naki ne?"
Ta sake daga kai alamar eh tare da cewa eh mantawa nai ban kawo kayi signing ba.
Ya jugo dashi gabanta yace "Anan zanyi singing din?"
Kallan takardar jiki tai wanda an riga anyi signing an yi stamp na gama case din.
Kallansa tai da sauri ta runtse ido, baisan sanda yai dan murmushi kadan ba, a hankali ta fara bude ido daya kafin tai ajiyar zuciya ta bude idan gaba daya tace "So nake naji meke faruwa kuma ba naso a gane."
Ya daga kai alamar eh yace "Zama dake yasa na fara koyan acting na karya."
Kallan mamaki tamai tace "Acting?"
Kai ya girgiza alamar ba komai yace "Anjima station din zai zama busy. Kije kafin a fara tunanin meke faruwa."
Fitowa tai ba tare da ta tambayeshi abinda yake nufi ba.
Kallan kofar yai ya sa yatsarsa saman girarsa ya akai idea din yazomin? Ya tambayi kanshi yana murmushi kadan.
Abinda yacewa Muktar ne ya fadomai wanda sam babu ma maganarsa a cikin abinda ya faru.
******

Hmmmm kankace ce mumunan labarin Sani ya baza ko ina, Nafeesa ta bude wayarta dan ganin abinda su Auwalu ke kallo akan Sani.
Sani ne zaune shida manyan mutane wanda girmansu a kasar babba ne, gabansu akwatina ne manya wanda zaka dauka abun arziki ne a ciki sai dai suna hirar da ba wanda yakeji saboda kashe audio din da akai, suna bude akwatin sai ka bindigogi wanda ake ganin yan ta'adar kasar na amfani dashi, da alama sune ma suke shigo musu da su.
Video din ne ya tsaya alamar an yanke wani guri sai kuma gasu gabansu da manyan kwalaye cike da kudi suna dariya.......
Muktar wayar hannunsa ce ta fadi bayan ya gama ganin abinda ke faruwa, lalai wannan tashin hankalin ba karami bane, Sani yanzu kam bai isa ya tsira ba gashi ya jawa manyan mutanen dake taimaka mai. Lalai Adnan bashida mutunci sai dai dole yai amfaji da video din nan kar abin ya shafeshi daga baya.
Fitowa yai jikinshi har bari yake, nufar inda aka kulle Sani yai ya dau sanda ya shiga, kallan Sani yai wanda yana ganinshi dadi ya kamashi yace "Muktar ka iso? Ka taimaka na bar nan ni ko kasar ne zan iya bari."
Gani yai Muktar ya nunashi da sandar hannunsa yace "Taka ta kare ni kuma bazan bi bayanka na rasa nawa mukamin ba, kudin da ka min alkawari zaka bani, ka turamin yanzun, zan ma taimako daya in ka karamin million ashirin akai zan taimaki Nuhu yabar kasar dan shima laifin dayai a baya daga an hukuntaka yaran nan zai taso dashi."
Mamaki ya kama Sani yace "Muktar me kake cewa?"
Wayarsa ya zaro a aljihu yace "Faramin transfer kafin azo a tafi dakai dan case dinka ya girmi nan."
Ido ya zaro nan danan gabanshi ya hau faduwa jikinshi ya fara rawa yace "Yaran ya nuna ne?"
Muktar ya ce "ka turamin kudin sai na nunama."
Sani gaba daya kasa komai yai ya koma kasa ya zauna."
Shima tsugunawa yai yace "Turamin yanzu."
Kallansa yai yace "Zan turama in naga akan menene."
Budemai video din yai ai Sani yana ganin su zaune da akwatinan ya tuna, hannunsa ne ya subutar da wayar jikinsa na wani irin rawa, shikenan tashi ga kare, ya akai Hajiya Babba ta musu video din nan? Bayan inda suke haduwa sirrinsa ne da ba wanda ya sani sai su?
Idanunsa ne suka ciko da kwalla ya kasa ko daga yatsarsa, sam baiji maganar Muktar ba akan ya tura kudin dan kanshi gaba daya ya daina aiki......
Ai inhar ragowar video din ya fito yasan shi kenan. Ya zaiyi da rayuwarsa?
Inalilahi wa ina ilaihi raji'un yau wace masiface ta afku mai?
Muktar a fusace ya kwadamai sandar hannunsa, Sani ya dawo hayyacinsa saboda azabar dayaji, kallan Muktar yai yace "Dukana kai fa?"
Wayar ya kara mikamai yace "Nace ka tura kudi kafin a fahimta ka tsaya kana jamin aji bayan kai yanzu ba'a bakin komai kake ba. Na tabbatar tafiya za'ai dakai kai kuma da ganin gari sai dai tsayuwar kotu to me zakai da kudinka? Gwara ka bani na taimaki danka.
Kallansa kawai yake wai har duniyar ta kare an fara dukanshi?

**^^*
Tunda ya shiga cell din Nafeesa ke lekensu, tutawa Adnan text tai ta sanar dashi, fitowa yai daga office dinsa ya kalli inda take zaune, da ido tamai alama me makon yaje gun sai ji tai yace "Nafeesa baki da lafiya ne?"
Kallansu tai tace "A'a lafiyata kalau."
"Oh naga kina wukil-wukil da ido ne."
Takaici ya kamata ta dauke kai, baije cell din ba kawai ya hanyar komawa, kallanta yai yace "File din dazu ki kawomin na duba abu."
Tace to, daukowa tai tana hade rai, gabanshi ta ajiye, kasan lebensa ya ciza yana kallan file din ya dago yaga taki kallanshi.
Rufewa yai yace "Kamar ma bana bukatarshi."
Hannu tasa zata dauka yace "Yanzu kinga evidence din da kikasha wahala gun samowa?"
"Wai dama abin yakai haka?"
Yana bude drawer yace "Ina miki magana jiya ai kika nuna rashin kulawa."
A ranta tace "Batan rai kai."
Flash drive ya ajiye a gabanta yace "Ga copy nan ki ajiye incase wani abu ya sa......."
Da sauri ta katseshi tace "Me kake cewa? Me zai sameka?"
Yanda ta dan tada hankalinta hakan kawai yasa shi dan murmusawa kadan, yace "Yaki na fara so please karki nuna kinsan komai, just stay on alert in wani abu ya faru kiyi spreading ragowar videos din."
Kallan flash din tai, ta kasa dauka dauka yai yasa a saman hannunta.
A hankali ta dago, jikinta duk yai sanyi...
Ya hade hannayensa yace "Thanks."
A aljihunta ta saka ta fito.........

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now