Babi na 13

417 79 13
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

*Akara Hakuri Dani🙇🏻‍♀️ Alhamdulillah na kamalla abinda ya tsayar dani Isha Allahu zaku dinga jina kamar yanda muka saba🤸🏼‍♂️*

Page 13

Kai tsaye motar shi ya shiga ya bi bayansu, sai dayaga sun nufi gidansu sannan yaja motarsa yai parking tare da kurawa gidan nasu ido yana dogon nazari, yafi minti ashirin a haka ko idanunsa bai ɗauke ba daga gun yana kallan gidan yana murza zoben dake kan dan yatsarsa na hannun dama. A hankali yai dan motsi da bakinsa sannan ya tada motarsa yabar layin.
Yana isa gida ya taradda mutanen gidan nasu sunyi bacci, abincinsa kawai ya ɗauka ya wuce ciki dan bai ma san abinda zai batamai rai a daren nan, haka ya kwanta bayan yayi isha'i ya kwanta yana sakawa da warwarewa har bacci yai gaba dashi.
Washegari da safe yana fitowa ya nufi police station dinsu, kai tsaye ya nufi inda aka kule Garba kallansa yai wanda shima yana ganinshi yai tsuru-tsuru, yana zazzare ido irin alamun rashin gaskiyar nan, ganin yanda yake kallansa yasa ya mike tare da sauke gwiwowinsa kasa yana murza hannayensa alamar neman afuwa, inda Zaliha take ya kalla tana zaune ta cusa kanta cikin gwiwowinta addu'a kawai take a cikin ranta, zuciyarta na ta sake anyana mata abinda ya faru, gyara kanta tai yanzu kila kasheta zasuyi daga anje kotu, Gambo ne ya faɗo mata da sauri ta girgiza kai tana sake share kwallar ta.
Adnan yana kallanta yana tunani, yarinyar nan gobe za'ai transfer dinta dan haka dole koma menene yayi shi yau, gurin zaman Nafeesah ya kalla sai kuma ya maida kallansa gun Garba.
Alama yamai da hannu akan ya fito, Auwalu dama duk abinda ke faruwa idanunsa nakai ya na ganin haka ya juya da sauri ya nufi office din Muktar, yana wuce wa Adnan ya kalleshi ta gefen ido, ai shikam dan kanzagin yana isa ya sanar da CP abinda ke faruwa.
A fusace ya mike suka fito tare dan dama ɓatan Nafeesah duk yabi ya ɗagamai hankali yanzu kuma ga yaran nan na neman sake jamai wani masifar, sai hura hanci yake yana tafiya cikin izza.
Cak suka tsaya suna kallan Adnan wanda ke mikawa Garba wayarsa da wallet dinsa. Muktar ya matso yana haɗe fuska dan ya jawo kwarjininsa ko ya ji shakarsa, yana bubuda jiki yana cewa "Adnan meke faruwa? Bafa nasan shirme, me kakeyi hakan?" Yai maganar cikin kakkausar murya.

Juyowa yai yamai salute sannan yace "CP Mahaifiyarsa ce batada lafiya kuma na fahimci kuskure na, dan ka ma shin danai babban laifi ne saboda bashida masaniya akan abinda ya faru, in fact ma shine ya kawo mana karar abinda ya faru so kaga nayi gaggawa gun kamashi."
Muktar ya ɗan ji sanyi a ransa, bayaso ya nunawa Adnan hakan ya sa ya ɗan daki kafadarsa cikin jin dadi dan dama Sani Malumfashi ya umarceshi daya tabbatar an kori Garba tun kafin ya fadi abinda zai jamai matsala, yana dan murmushi yace "Well done, at least jiya da yau ka fara dawowa hayyacinka."
Adnan ya ɗago yace "CP an samu labarin officer Nafeesa?"
Gabanshi ne yai dum ya dake tare da girgiza kai jiki a sanyaye yace "Haryanzu ba labarin ta gaba ɗaya na rasa meke faruwa, gashi sanda aka turota ance iyayenta a kauye suke so kaga kenan basu san halin da ake ciki ba, ina tsoron kar suji suzo su mana hauka kasan mutanen mu na karkara yanzu zasu zo su tada mana jama'a."
Kai Adnan ya jinjina yace "Kayi hakuri CP jiya raina ya ɓaci ne shiyasa na ɗaurama laifi, ni zan fita akwai aikin da zanyi, zan sake binciken inda ta shiga."
"Ahh je kayi aikin ka, ni dai ko yaya inkaji labarin Nafeesah ka sanar dani immediately."
Salute yai sannan ya fita daga station din ba tare da ya kalli Garba ba bare su sa ran wani abin.
Muktar ne ya matso kusa dashi yana dariya yace "Kaga aikin Sani ko? Shine ya umarci Adnan daya sakeka shiyasa kaga ya buɗeka, dan haka ka tabbatar ka mai godiya."
Nan ya rusuna yanawa Muktar godiya, hannu yasa a aljihu ya ɗauko dubu biyu ya matso cikin raɗa yace "Daga nan ka wuce tasha ka koma garinku sannan kada ka kuskura ka sake dawowa, Yallabai zai aikama da sako."
Kai ya ɗaga da sauri yana godiya, sai gumi ke sake keto mai, juyawa yai cikin sauri yabar station ɗin yana hamdallah, dole ya koma kauye su kafin mahaifiyarsa taji shi tsoranshi ma ance batada lafiya Allah dai yasa ba ciwon ta bane ya tashi, sauri kawai yake bazawa akan titi, horn yaji daga bayanshi, bai juyawa dan a gefe yake tafiya, sake jin horn yai, ya jiyo yana san sanin meke faruwa.
Cak ya tsaya saboda wanda ya gani cikin mota, ido ya zaro gabansa ya tsananta faɗuwa, rigarsa ya fara naɗewa yana neman rogawa a guje, "Shigo."
Garba ya kalleshi yace "Officer ba ka sallameni ba? Ai kafafuwana sun isheni."
"Garba akan hanya muke, shigo ko kuma mu koma inda muka fito."
Sauke rigarsa yai daya tattare, zuciyarsa ta fara harbawa, shidai kam an sashi cikin masifa daga kwanciya da mace sau daya yanzu me ya daɗa mai?
Shiga yai gaban mota ya sadda kai kasa takaicin duniya duk ya isheshi.
Adnan baice mai komai ba sai da sukai minti biyar suna tafiya, idanunsa nakan titi yace "In kaje kwaso kayanka ka sanar da Hajiya Babba akan nasan komai, in har ba so kake suce kaine ka sanar dani ba."
Kallan mamaki yamai zuciyarsa kamar zata fito, bakinsa har rawa yake gun cewa "Officer me kake nufi? Me ka sani? Na rokeka da Allah ka barni wallahi Allah bazan sake kusantar wata ba sai matata, dan Allah kayi hakuri ka cireni daga......"
"Sannan kada kasa ran zan barka ka tafi garinku, na fito dakai ne dan in ajiyeka akan zaka zama shaida gobe."
Idanu ya zaro nan danan ya kalli waje ya fara kokarin bude kofa, duk da lock din dake jiki bai hanashi kokarin buɗewa ba, ganin tabbas bazai iya ba yasa ya juyo jikinshi na ɓari yace "Office ka yafemin dan Allah ka barni na tsira da raina."
Adnan bai kula shi ba sai kuna mota dayai, kai tsaye layin ya nufa, dayake anyi bakwai mutane sun daina zama a kofar gidan, daga can farkon layin ya tsaya bai buɗe ba yace "Ka sanar da ita abinda na fada maka, sannan ka ɗora da cewa "Daga alaqarta da Sani har zuwa abinda suka aikatawa mai gidan."
Nan danan jikin Garba ya hau kyarma yace "Officer? Me kake cewa? Ni dai dan Allah ka barni na tafi garinmu wallahi nama alkawari......."
Wayarsa ya ciro ya dan jijigata yace "Inna kuke ce mata ashe?"
Idanunsa ne suka firfito ya fara fifita da hannayensa, a hankali ya hadiyi yawon bakinsa, Adnan ya cire lock din yace "Sai ka fito."
Dakyar ya fito daga cikin motar, yana tafiya kamar mai tatata, jiyake gaba ɗaya kansa na sarawa, shidai kam da alama rayuwarshi tazo karshe daga kwanciya ɗaya, kwanciyar ma da tsoro ya hanashi zakewa yaji dadin abin.
Har ya isa kofar gida bai sani ba sai jiyai an talle mai keya da karfin gaske, sosa wa yai yana juyowa cike da mamaki dan tabbas yaji zafin dukan.
Nuhu? Abinda ya fada a ransa kenan sannan yai saurin sadda kai kasa yana cewa "Yallabai ina kwana?"
Sake make kanshi yai yace "Ku dama bayin gidan nan bakuda tarbiyya banda iskanci ina tafe bazaka rusuna har kasa ka gaisheni ba?"
Garba ya dan rusuna yace "Kayi hakuri, daga police station nake."
Tsaki yaja ya samu kafarsa ya taka da karfinsa, kara Garba ya saki saboda irin manyan takalman nan ne na turawa, ya sake murzawa sannan yace "Daga kurkuku kake ba police station ba." Yai tsaki sannan ya shiga ciki yana bubuda kafa, irin tafiyar yan gayu. Kayan jikinshi kadai zaka kalla kasan ya kure gayu an kuma kashe kudi gun siyansu.
Adnan yana kallan sanda motar tazo ta wuce, da ido yabi motar yana mamakin wannan kasar tamu, ace mutum yai laifi amma ya dinga yawo kamar baiyi komai ba.
Garba ya share fuskarsa gaba ɗaya ya rame kamar ba shi ba, ciki ya shiga mutanen gidan kamar ba wanda akawa mutuwa ba, girke-girke da soye-soye ake, masu aikin na ganinshi suka ce Garba, oyoyo.
Murmushin yake yai yace "Su Hajiya fa?"
Zasuyi magana sai ga Matar Alhaji ta uku hannunta ɗauke da waya a kunne tanayi, kallan inda Garba yake tai, bata ce mai komai ba ta ɗauke kai, ta cigaba da wayarta tare da ɗaukan cup tabar kitchen ɗin, sakato ya tsaya yana kallanta wato anci moriyar ganga? Yanzu itace zata ganshi ta mai wannan kallan bayan tasan sune sukaja mai yaje cell?
Ganin bazai iya jurewa ba yasa ya bi ta, zata shiga ɓangarenta yace "Hajiya! Baki ga na dawo bane?"
Wayar ta kashe ta kalleshi tace "Garba baka koma garinku ba? Dan Allah kai maza ka wuce banasan maganar mutane." Baki ya buɗe galala yana kallan ikon Allah, sai kuma ta kalleshi tace "In zaka wuce zan baka kudin mota, kada kuma ka kuskura ka shigo ɓangarena, akwai ragowar mutane ni a gurina."
Bata jira mai zaice ba ta shiga ciki tana daddana wayar. Kasa ko motsi yai saboda tsananin mamaki, yau shi takewa magana haka? Babu tambayarsa halin da yake ciki? Bayan tasan ita ta jefa shi ciki?
Ɓangaren matar Alhaji ta tsakiyar ya nufa a kalla ita ai yana ganin bazatamai haka ba.
Sai dai me? Kofar ta ya gani a kulle, ya daga hannu zai kwankwasa daga ciki ya juyo muryar mai aikinta tana sanar mata akan yazo.
Ya kara mika hannu zai buga yaji Hajiyar tace "Garba? Kayansa yazo kwasa ko me?"
Mai aikin tace "Oho masa can na ganshi yabi bayan Aunty."
Tsaki tai tace "Samin sakata ko yazo karki bude mai, na gaji da hayaniyar yan gaisuwa inaso nai bacci, bana san ɓacin rai, ni yanzu  banida lokacin wasu almajirai irinshi. Daga shi har mahaifiyarsa."
Hannun Garba ne ya hau rawa a hankali ya zare hannunsa daga jikin kofar, wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mai, ya juya a hankali bakinsa har rawa yake saboda kokarin danne abinda ke cinsa a ransa, lalai wato sun manta abubuwan da suka sakashi da yanda ya dinga sadaukar da kansa saboda su?
Tabbas yanzu kam shima bazai raga musu ba, kai tsaye ya goge fuskarsa ya nufi bangaren Hajiya Babba, Nuhu ma ciki dan daga waje zaka juyo maganarsa. A waje ya tsaya dan yasan bai isa shiga yana ciki ba.
Hajiya Babba ce ta fito daga falan fuskarta duk tayi luhu-luhu alamar shan kuka. Yanzun ma idanunta sunyi jaa sanye take da dogon hijab hannunta ɗauke da carbi tana ja. Garba na ganinta ya zube a kasa yana gaisheta. Ta matso idanunta tana maganar da kyar tace "Garba an sakoka?"
Kai ya ɗaga, tace "Biyoni ciki."
Tai gaba yabi bayanta har suka shiga ɗakinta, rufe kofa yai ta kalleshi sannan ta jawo drawer ta ciro kudi yan bandir din dari biyar-biyar ta cila mai sannan ta kauda kai tace "Gashi, ka wuce garinku ka kula da mahaifiyarka, in da hali kar ka sake shigowa Kano, sannan abinda ka gani ka tabbatar ka haɗiyeshi har karshen rayuwarka, ba sai na fada ba kafi kowa sanin halinda mamanka zata shiga in taji abinda ka aikata kaima."
Ɗaukan kudin yai ya hadiyi yawun bakinsa, yana jinjina kai alamar to, wani kallo ta watsamai tace "In ba abinda zaka fita ka wuce yanzun nan."
Kallanta yai bakinsa na rawa yana goge fuskasa yana cewa "Hajiya yanzu zan tafi dan nima banasan in jefaki cikin wani hali, sai dai abinda ya sa aka sakeni ba dan Yallabai yayi magana bane, ya sakeni ne saboda yasan komai game daku, yanzun ma sai daya sake jaddadamin da hakan."
Idanunta fa zaro ta hade hannayenta guri daya tace "Yasan komai kamar ya? Me dame ya sani?"
Garba ya motsa baki kafin ya cigaba "Har alakarku da Yallabai........"
Abinda ya ga ya gifta ta kansa ne yasashi yin shiru dan wani azababben zafi ne ya ziyarci kansa, hannu yasa a gun gani yai jini a hannunsa, a firgice ya kara kai hannunsa sannan ya kalli abinda aka jefeshi dashi, mikewa yai yana rike gun yana neman fita. Cikin tsawa tace "Dawo nan."
Komawa yai jikinsa sai karkarwa yake, ta mike zuciyarta na tafasa ta matso tana kallansa tace "Kai ka sanar dashi ko?"
Kai ya shiga girgizawa yana cewa "Wallahi Allah ba ni bane, bansan ya akai ACP Adnan ya sani ba."
Kasan lebenta ta ciza ta dan matse hannayenta tace "Sai me ya sani?"
Kai ya hau girgizawa yanzun ma ba kakautawa, yana cewa "Bansan komai ba Hajiya wannan kadai na sani."
Iska ta furzar ta haɗiyi yawun bakinta tace "Wuce ka tafi, sannan zan sa akaika har tasha aga tafiyarka."
Yace "To Hajiya."
Haka tai wa driver waya ya fita ya shiga mota, sai danne goshinsa yake da kaya daga baya ma vest dinsa ya dauka ya nada a kansa, lalai yayi dana sanin shiga gonar mutanen nan.
Sanda suka zo kusa da motar Adnan kawar da fuskarsa yai da sauri dan baya ma san ya ganshi, sai dai Adnan tun da suka fito yake bin motar da kallo har suka zo inda yake, horn yai hakan yasa drivern ya kalli motar, Adnan ya fito ya zo jikin motar yana kwankwasa glass din.
Zugewa yai yna san sanin abinda ke faruwa. Garba kam ya shige kasan mota ya boye a bayan kujera, ID card din sa ya ciro ya nunamai yace " Mutumin bayan motarka nakeso.
Drivern ya hadiye yawun bakince yace "Officer nima aike na akai."
"Nima aikenka zanyi in har ba so kake kaima ka shiga sawun masu laifi ba."
Cikin sauri yace "A'a kayi hakuri wlh ni bansan komai ba"
Adnan yai murmushi yana kallan Garba yace "Ka wuce ka jirani a Tahir guest palace, am sure kanada kudin hotel ka kwana acan zanzo da daddare, sannan kafi kowa sanin abinda zai faru in ka gudu, indai har ba kasar zaka bari ba kasan babu inda zaka da baxan kamo ka ba."
Lekowa yai Adnan ya ga jini a jikin farar vest din, kai ya girgiza yace "Ka je ka jirani zanzo."
Shikam ba yanda zaiyi an riga an sashi a masifa da bala'i, juyawa yai tare da furzar da iska meyasa wasu mutanen sunsan ba darajasu ake a guri ba amma sai kaga sun nace? Mota ya koma yana kallo suka wuce sannan ya maida kansa kan kujera yana kallan gidan, bashi da tabbas akan zasubi umarninsa sai dai ba yanda zaiyi tunda ba wani ya yarda dashi ba balle yace ya bisu, kuma zamanshi a bakin nan shine mafi mahimmanci.
Nafeesah ce ta fado masa a rai, da tana nan da ta yi handling aiki ɗaya shi kuma yaji da ɗaya. Haka kawai yakejin kasan zuciyarsa nasan sanin halinda Nafeesa ke ciki, bata samu waya ta turo sako ba balle yasa ran jikin da sauki.
Sunan ta ya kalla a wayarsa sannan ya maida wayar kawai ya ajiye, yana bin gidan da kallo da fatan dacewa da abinda yake yi.
****
Hajiya Babba kuwa tunda ya tafi ta kasa sukuni, waya ta ɗauka ta kira Sani yana dauka yace "Baby na!"
(Nikam Ayusher dariya ce ta kwacemin su Baby manya)
Hajiya babba bata amsa va tace "Habibi muna cikin tashin hankali, wannan dan iskan dan sandan da alama yasan alakar dake tsakanin mu. Ina zan ganka? Inaso mu hadu muyi magana."
Idanu ya runtse da karfi, ji yake zuciyarsa na tafasa ". saboda bacin rai lalai sai yasa an yiwa yaran nan duka hankalinsa zai kwanta, yaro guda ɗaya yabi ya addabesu? bayasan ya daga mata hankali hakan yasa yace "Ni na ɗauka missing dina ne yasaki nemana? Kinfi kowa sanin yanda nake ji a raina."
Iska ta dan furzar daga bakinta ta zauna a bakin gado tace "Bakaji me nake ce maka bane? Yaran nan....."
Katse ta yai yana murmushi "Kizo gidan da muka saba haduwa, ni ganinki kawai nake san yi."
Goshinta ta ɗan murza kadan tace "Daga yin bakwai jiya in aka ga na fita yau a maimakon zaman takaba kaima kasan magana za'ai. Duk da ba mutane amma akwai wasu a gidan."
"In kuma asibiti kikaje fa? Ko Babyn tawa ta manta ta iya acting?"
Bata san sanda tai murmushi ba tare da yin fari da ido tace "Kai ana magana serious kana wani zancen."
Ya shafi sumar kansa yana sake kishingida sai kace wani yaro, yace "To ni wannan kananan abun ai ba sune a gabana ba, ke kadai nake san gani."
Harara tai kamar yana gabanta tace "Nuhu na nan so kake yasan wani abu?"
"Ko shine kiyi amfani dashi nidai plz ina jiranki."
Dariya tai sosai tace "Lalai Habibi bakada dama ɗanka zaka sa ya kaini ma?"
Yana sake cusa hannunsa saman kansa yace "To me za'a fasa? Ni duminki kawai nake san ji, sati guda fa?"
Kashe wayar tai tana dariya kafin ta canza fuska tai kwafa, lalai yaran nan yaga gurin baccinsu ne shiyasa har yake cigaba da bincike akansu.
Gyara hijab dinta tai ta kuma ɗaukan carbi ta fito daga ɗaki tana tafe dakyar tana tari, tana zama Nuhu yace "Umma Babba dan Allah ki sa tawakalli a ranki duk kin rame kin canza wlh, nasan rasuwar kawu tazo a ba zata shiyasa wannan tsinaniyar yarinyar data kasheshi wallahi sai munga bayanta, nasa abokaina sun sai kayan aiki randa zata fara zaman kotu ranar mu kuma zamu shekata lahira ai dana ance wanda ya kashe a kasheshi ehe."
Itadai matsar kwalla kawai take, hannunta tasa saitin kirjinta kawai ta rikw ta fara neman jan numfashi tana farfari da ido, hankali a tashe suka mike sukayo kanta, faduwa tai daga kan kujera tana sake rike kirjinta, cikin tashin hankali Nuhu yake kallanta shida abokinsa yace "Umma Babba! Lafiya?"
Cikin murya dakyar tace "Nuhu ku kaini asibi......."
Kasa karasawa tai saboda numfashinta daya rike, da gudu ya fito yana kwallawa matan kira, nan suka fito dan dama sun kori kowa jiya akan wai basa san hayaniya suna san suwa mazajinsu addu'a daga su sai masu aikinsu.
A rikice suka sata a mota, shi kuma yaja suka fito daga gidan.

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now