Babi na 7

413 92 10
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️
     
*TALAKA DA MAI KUDI*

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

https://arewabooks.com/chapter?id=62854a00ef85a63a21dda994

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

   *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS

+447894142004

IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki

Page 7

A zaune suke sunyi group da alama gulma sukeyi, tana shigowa suka kalleta kamar abin hadin baki, da sauri tai salute sannan ta gaishesu, alama suka mata da hannu akan ta matso hakan yasa ta karaso tana tunanin abinda ke faruwa.
Cikin boyo kowa ya nuna mata envelop, cike da mamaki tace "Na menene?"
Dan dariya sukai sannan kowa ya maida nashi aljihu, cikin dabara tace "To amma ni fa? Nawa fa?"
Auwal ya sa dariya yace "Ku ai na ɗauka ƴan gaskiya ne, ko dai kin fara ɗaukan kebura ne shiyasa kika sauko?"
Kai ta sunkuyar tana murmushi tace "Ashe ka gane."
Dariya suka sa mata, sai ta ɗan waiga alamar dubawa sannan ta ce "Ɗan Allah ku bani nawa kafin Boss ya shigo."
Tana ɗagawa suka sake shekewa da dariya Auwal yace "Kin makaro sai dai ki bari sai an sake rabo sai a haɗa dake."
"Amma waye yai rabo haka da safen nan?"
Suka kalli juna, Auwal yace "Koma wanene ba ruwanki kedai anyi babu ke."
Taɗanyi yake jiki a sanyaye ta juya tana tunanin waye yazo da safen nan har suka samu kudi haka? Tana zama Auwal ya mike ya nufi office ɗin Muktar dan dama ya sanar dashi su tabbatar sun nunawa Nafeesa sannan ya sanar dashi abinda tace. Yana shiga ya sanar dashi abinda ya faru. Cikin jin dadi ya sallameshi ya fito sannan yai murmushin jin dadi, ba shakka komai yanzu zaizo da sauki kenan. Dan ya kula Adnan ya yarda da yarinyar.
******
A bangaren Adnan kuwa ya ɗan dade a mota da alama waya yake, sai dai ko wace irin wayace kana kallansa xaka fahimci ba dadin yin wayar yake ji ba, yana kashe wayar ya fito, tsayawa yai daga jikin motarsa, yana kallo sanda wata mota tai parking sai kuma ya hango mace da namiji sun fito suna alamar godiya, kallan motar yai wacce ta ajiyesu daga nesa, sannan ya kallesu tare da nufowa hanyar station ɗin, hannun matar ɗauke da kullin kaya a cikin ɗan kwalli, wanda hakan ya tabbatar mai daga kauye suke. Fuskarsu ya kalla matar tana tafe tana share hawaye, cikin hanzari ya nufo inda suke yasha gabansu.
Ganinsa sanye da kayan ƴan sanda yasa suka gaisheshi, Adnan ya gaishesu shima yana musu kallan mamaki yace "Lafiya?"
Hawayen babbar matar ce ya karu sai yanzu yaga tsananin kamar da mutanen sukeyi da matar da suka kulle jiya, zubewa matar tai a kasa tai zaman dirshan tana dukan cinyarta, ganin haka yasa yace "Lafiya? Menene hakan?"
Mijinta ne ya ɗagata tare da yi mata raɗa a kunne akan ta daina kartasa suma a kullesu.
Kuka kawai take tana cewa "Wannan yarinya anyi ƴar banza, ta cuceni..."
Ran Adnan ne ya ɓaci dan a duniya ba abinda ya tsana irin yaji uwa tana mugun furuci ga ƴaƴanta, kallan mahaifin yai yace " Zaku iya zuwa can muyi magana? Ko ba iyayen Zaliha bane?"
Cikin sauri suka kalleshi, ya dake yace "Ni ne wanda nasa a kulleta, sai dai kafin ku shiga ciki inasan muku wasu tambayoyi inhar kun cancanta in barku ku shiga zan barku."
Ai nan danan suka fara tafiya zuwa inda ya nuna musu.
Zama sukai ya kallesu yace "Iyayen Zaliha ne ku ko?"
Da sauri sukace eh, cikin ɗaure fuska yace "Yanzu fisabillilahi abinda kukai me ya daɗa muku? Inhar kunsan yarinya bataso menene na tilasta mata?"
Majina matar ta shiga fyacewa, mijin ya daure yace "Wallahi san zuciya ne, yaran da takeso ba shi da wata sana'ar arziki ɗan karamin shago mahaifinsa ya budemai yake saida shayi da burudi, ita kuma tana bala'in sanshi shiyasa muka hakura muka barsu tare, ganin yanda a koda yaushe yake ɗawainiya da ita yasa muka tsaida mata shi a matsayin miji, anata hidimar shirin bikinta kwatsam Bawan Allahn nan ya shigo Ringim sunzo abin zaɓe da ɗan uwansa ke kokarin tsayawa takara, tunda ya ganta yace yanaso, mu da duk danginmu na kauye babu mai mota, sai dai mu gani a maƙota, shiyasa tunda muka ganshi mukaga uban kuɗin daya bamu muka fahimci lalai abinda muke nema ne muka samo. Shiyasa ko da ya ce mu maida ma yaran nan kayanshi bamu ji kunya ba, sannan ai koshi yaran ya samu alheri tunda dubu hamsin aka karamai a saman kayan lefensa."
Ya ɗanyi shiru sakamakon wani kallo da Adnan ya mai, ɗan hannunsa yasa a matsin idansa yace "To yanzu duk abinda ya baku yana ina?"
Uwar ta sake zubewa a kasa tana dukan cinyarta tace "Yarinyar nan ta rokemu ta rokemu amma muka firr mukace a'a, haka yaran nan har kwana yai a kofar gidan mu amma muka kekashe idanmu mukace bamusan wannan zancen ba."
Adnan ya dan nisa tare da kokarin kwantar da murya dan zuciyarsa har tafasa take saboda abinda suka aikata, yace "Sannan shine da kikazo kike neman tsine mata? Bayan kusan laifin naku ne?
Ta mike tana share hawaye tare da dakewa tace "Malam ɗan sanda duk da laifin mu amma bamusata kisa ba ko? Wannan wani irin bala'i ne? Daga neman arziki sai ta jawo mana tsiya?"
Adnan takaici ya kara kamashi ya kalli mahaifin yace "Amma a matsayin ku na iyaye babu tantama a maganarku? Babu irin kuce anwa ƴarku sharri? Ko kuce kunsan bazata aikata ba?"
Kauda kai baban nata yai yace "Damu ta kwana? Bafa damu ta kwana ba? Wayasan abinda ta aikata? Sannan wannan ɗan iskan saurayin nata ba abinda bazai saka ta ba."
Mikewa Adnan yai zuciyarsa na wani irin zafi, wai waɗannan kuma suna da bakin kiran kansu iyaye?
Har zai fara tafiya ya dan tsaya yace "Waye ya kawoku?"
Kallan juna sukai da sauri yace "Wani ɗan uwan mu ne."
Adnan ya kalleshi sosai, dazun nan yace basuda mota daga shi har danginsu sannan yanzu an kawosu a mota mai tsada yace ɗan uwansu? Sannan wanene yasan inda aka kulleta? Dan haka kawai wanda baisan komai ba sai yayi binciken station din da aka kaita amma su an kawosu da safe kai tsaye? Tabbas akwai wani abu.

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now