Babi na 19

296 75 7
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

08146017245.*promo promo zamuyi muku kyauta inkikasai magani biyu zuwa Sama zamu yimiki kyautar hatsabibiyar hodarmu Domin powder kadai kikai aiki da ita hmmm zakiji bayani agun oga*. *Hohoho sanyifa yazo Saida gyara Mata azo agyara ina Uwar gida ina amarya ina Mata yan kwalisa kuzo Ku Kankaro mutunci da kuma daraja gun oga*. *Duk da dayawa kunsan kayan maman haidar toh nakuma kawomuku na kwarai kayana daga chadi Ake kawon Sudan nijar*. *Muna da nau in magun guna kuma kayan mu na hausane basa cutarwa ko illah saidai su gyaraki kisamu farin ciki*. Ina me neman maganin sanyi sadidan basai natsaya nayi jawabiba kayan mu Kan kat ne. Ina me neman maganin Nono da maganin hips da na kiba korage kiba kuzo akwaisu ingantattu *ina meson maganin matsin ciki Dana waje daciko dagaban mace kaza me allura Dan Shila kasaitacciyar kaza ta yan Sudan ina meson magani mekarawa mace dadi inameson magani me karawa mace ni ima tamkar tana kogi kuma yasa ki fellin Maza zo Yar uwa kihucetakaici kayanmu gangariyane Babu Kar ya aciki kigwada kisha mamaki*. Akwai na mallaka Kala kala akwai na Yan Mata shima . 08146017245.

*Page 19*

Station dinsu suka nufa dan hankalinsa bazai kwanta ba sai ya tabbatar Sani na kule, tafiya suke motar tayi shiru saboda ba wanda yai magana, kafin can d'an gyaran murya yace "Jikinki fa?"
Bata kalleshi ba fuskarta nakan titi tace "Alhamdulila na warke."
Sai kuma ta d'an kalleshi kad'an tace "Kaifa?"
"Nifa?" Yai tambayar yana kallanta, labanta ta hade alamun maida dariya ta cigaba da tuki tana shafar saman goshinta. Fuska ya tsuke dan ya gane wulakancin da take shirin yi wato dan yaje dubata ya bige shine.
Gyaran murya ya sake yi wanda hakan yasa motar ta sake yin shiru. Kamar bazaiyi magana ba dan ya zaro wayarsa yana dannawa kafin yace "Kamar ciwon ba yau kika fara ba ko?"
Murmushi tai kafin tace "Eh! Tun ina yarinya ne amma yanzu na samu sauki."
Kamar zai sake tambaya sai kuma ya fasa, ganin shirin dake tsakaninsu bai kai haka ba ya rasa me yasa yake san sanin abinda ke damunta.
Shiru ne ya biyo baya sai karar radio wanda yawanci labaran zancen Sani Malumfashi akeyi.
Itakam a ranta ji tai hawaye na neman zubo mata sai data dake sosai kafin a zuciyarta tace "Thanks to someone."
A station dinsu tai parking ta kalleshi tana shafar kanta, kauda kai yai kamar bai ganta ba, yana neman bude mota, ganin da gaske fita zaiyi yasa tai saurin cewa "ACP!"
Kallanta yai irin mai alamar tambaya din nan, ta dan kifta ido tana shafar gefen fuskarta, kai ya dan karkatar kadan zuwa inda take shafar fuska yace "What?"
Ganin da gaske yake yasa tace "Zan iya shiga a haka?"
Kallanta yai abayace a jikinta, tayi kyau duk da ba kwalliya tai ba, yana kallanta yace "Gashi ciki gun aiki ne, ba gidan hira ba."
Fuska ta canza dama ta sani, itama me yakaita tambayarshi? Kai ta jinjina tace "A kalla aikin sirri aka sakani banaji akwai matsala."
Karasa fita yai sai kuma taga ya sako kansa ta window, kallansa tai yace "Exactly kin sani why are you asking?"
Kai ta kauda gefe lalai ma mutumin nan ta fito saboda shi amma ya fada mata magana?
Adnan kam ciki ya nifa dan hankalina na kan Sani, tun a bakin hanya mutane ne sunyi cuncirindo haka ya ratsasu ya shiga ciki yaba mamakin me ya kawo ma'aikata nan? CP Muktar na tsaye a gaban wani mai uniform na aikinsu, ko ba'a fadaba kasan babba ne saboda yanda Muktar ke bashi girma, da kuma yanayinsa.
Adnan na karasawa yai salute tare da kamewa, mutumin ya kalleshi ya kalli sunansa yace "Kaine Adnan?"
Sake salute yai yace "Eh!"
Kai ya jinjina kafin ya mika mai hannu suka gaisa, Adnan ya sake kamewa.
"Well done. Sai dai zamu wuce da Sani Mulumfashi acan zamu cigaba da binciken mu, kai kayi iya naka."
Da sauri Adnan ya kalleshi yace "Amma...."
Wani mugun kallo daya makamai ne yasa Adnan kasa magana dan mutumin bayan girma akwai kwarjini, ya kalli Muktar yace "A fito dashi zamu wuce, sannan kowa yasan Hajiya Babba ita ce ta shirya komai so shi a matsayinshi na babban mutum he can't stay here and that's final bana san wasu kananan maganganu, sannan mun fika sanin aikin mu."
Yana kaiwa nan ya yai hanyar waje, Muktar jiki na rawa ya bude Sani suka taho tare yana bubuda kafa, kusa da Adnan ya tsaya ya dan guntse dariyarsa kafin ya bubugi kafadun sa yace "Officer ayi maza aje unguwanin talakawa a kamo masu laifi, ka daina kai kanka inda aka fi karfinka, kaji dan saurayi."
Adnan ya watsamai kallo tare da kallan hanunsa dake kan kafadarsa, cike da takaici yace "Ko dan saurayi baici galabar daureka ba a kalla yaci galabar b'ata maka suna wanda har abada wasu da taban xasu dinga kallanka."
Nan danan Sani ya fusata ya fara huci yace "Me kace? Kai wato bakada mutunci ko?"
Adnan ya kauda kai yace "Mutunci ya wuce a akamani da matar kanina...." Ai Sani bai jira ba ya daga hanu yana neman kaimai mari, da sauri Muktar ya rikeshi tare da janshi cikin rada yace "Yallabai mai kakeyi? Ka manta plan din?"
Saman goshinsa ya shafa yana sauke ajiyar zuciya yace "Na manta wlh yaran nan ne na tsaneshi kamar mutuwata wlh."
Tare suka dawo Adnan ko kallan inda suke baiyi ba, ji yake zuciyarsa kamar zata fashe, wannan wace irin kasa ce? Da safen nan a dawo da mutum amma ko awa hudu baiyi ba su daukeshi?
Sani ya dawo inda yane yace "Yaro watch and see yanda manya ke aiki."
Adnan ya kalleshi baice komai ba.
Daga waje kuwa Nafeesa na kokarin shiga ta hango mutumin nan na fitowa, gefe ta tsaya tana kallanshi, idanunsa ne yakai inda take fuskarsa a d'aure sosai. Karasowa tai gabanta na fad'uwa, salute tamai idanunsa na kanta yace "Nan aka kawoki?"
Ta d'aga kai tare da cewa "Kawu me....."
Katseta yai da cewa "Khalifa xai dawo nan da wata uku kafin ya dawo ki ajiye wannan aikin banasan shirme, dama babanki ne ya bari kika sangarce, ni in kukai aure zan dawo dake daidai."
Yana kaiwa nan ya wuce sukabi bayansa, da kallo ta bishi tare da cizon lebenta na kasa, ba yau ta saba ba shiyasa sam a duniya babu wanda batasan gani irinsa tasan ya tsaneta shiyasa ta kasa gane dalilinsa na dagewa sai ta auri Khalifa. Ta na neman shiga Sani na fitowa, da mamaki ta kalleshi ta kalli Muktar wanda ya buga mata wani kallo ya numata da yatsa yace "Zan dawo zamuyi magana."
Ko a jikinta ta wuce ciki a ranta kawai ta samu kanta da maimaita abinda yace, taja tsaki tana sake kallan Sani. Dama tasan ba mutunci ne ya kawo shi ba gashinan ta gani.
Adnan ta kalla wanda ke tsaye ke kam, kallo daya zakamai kasan ranshi a bace yake, tausayinshi ne ya kamata ace duk wahalar dayasha suna neman maidashi a banza?
Karar maganar dataji ne yasa ta kalli su Auwalu, labarai akeyi akan yanda Hajiya Babba ta cucu Sani, cikin sauri Adnan ya karasa kusa dasu ya amshi wayar yana kallan video din, video ne aka mata daga gidan tv a sanda za'a kaita gidan zama na wucin gadi kafin a sake shiga kotu,
Tana kuka tace "Nayi dana sanin abinda na aikata, Sani ba abinda yai nice nai amfani dashi na yaudareshi, sanda akai kisan nan kiranshi nai a waya wanda hakan yasashi zuwa gidan sannan shine ya tyra Garba police station akan yakai kara a lokacin baisan nice nai ba dan duk a zatanshi Zaliha ce. Sannan zancen zuwa gidansa dukanmu munsan yanda Sani ke da karamci, ni ma kirashi a waya akan akwai abinda nakesan sanar dashi akan case din nan, bai amince da zuwana ba sai dai nai amfani da dansa naji inda yake nai karyar ciwo naje gidan ba tare da saninsa ba."
Tana hawaye tacigaba "Hoto kuma sharri ne, kowa yasa na'urorin yanzu ba abinda bazasu iya ba tinda gashi munga sharrin da tawa ACP Adnan....." Ta sake fashewa da kuka tace "Ku yafemin nayi dana sanin abinda na aikata...."
Adnan ya daga wayar yana neman yarwa, da sauri Auwalu ya cafe yana haki yace "Sorry ACP wallahi banda kudin siyan wata."
Kallansa yai yaga idanunsa sunyi jaa da sauri ya amshi wayarsa yai sum-sum ya matsa. Nafeesa dake tsake saman goshinta ta dafa tana mamakin wannan rashin imanin, lalai Hajiya Babba da alama akwai abinda suka ce mata daya sata yin wannan maganar.
Adnan a fusace ya yo hanyar fita, bayansa tabi tace "ACP ina zaka?"
Bai kulata ba har ya shiga mota, zai rufe kofa ta rike tace "Sorry ACP but...."
Yanda ya kalleta ne yasa ta saki kofar, rufewa yai kawai yaja yabar gun.
Ajiyar zuciya tai, wannan Sanin me zasuyi suga an hukuntashi? Dan ta tabbatar babu abinda za'amai tunda aka daukeshi daga nan.
Mota ta koma ta wuce gida, tana shiga driver dinsu ya rugo da gudu ya gaisheta.
Kallan motar Dady tai ta kalli driver din tace "Dady ya dawo?"
Ya daga kai zaiyi magana Barira ta fito cikin sanda ta tace "Aunty yau zakisha fada."
Ajiyar zuciya tai tace "Fada na uku a rana daya?"
"Ai Ummy ma jiranki take."
Cike da shagwaba ta buga kafa tace "Fada hudu?"
Barira ta sake matsowa tace "Ai mai sanyin ki ma ya kira shima na tabbatar fad....."
Rankwashin kanta tai hakan yasa Barira rike kanta, Nafeesa tace "Ke dadi ma kikeji za'amin fada ko?"
Kai ta girgiza da sauri tace "Inaa a'a kawai dai in aka miki fada gidan kowa fishi yake bana aiki sosai in shige dakin Ummy naita kallo."
Kasan lebenta ta ciza tace "Yau kinji dadi kenan, ki tabbatar kin kwana kina kallo yau in ba haka ba ki gamu dani."
Ta karasa maganar tana shiga ciki rai a bace, Barira kam yar karamar rawa ta taka tace "Allah yasa Ummy tabarni na kwana ina kallo."

*****
Sumi-sumi ta shiga ciki Ummy na zaune a falo ita da Dady, ko abincin da aka kawo mai ma baici ba da alama ma ko budewa baiyi ba.
Tsugunawa tai a kasa ta sunkuyar da kanta tace "Dady ina wuni? Ummy ina wuni?"
"Kin kyauta, wato mu bamu isa mu fada kiji ba ko? Na dauka na sanar dake karki fita yau?"
Ta kalli Dady cikin rarauniyar murya tace "Dady kayi hakuri wallahi banyi niyyar fit ba nima, ganin Adnan na neman shiga tashin hankali ne yasa ni fita."
Fuskarsa ya shafa yace "Nafeesah ma fahimceki amma dan me zaki fita ba izini? Harda tuki bayan ba lafiya gareki ba?"
Kanta na kasa tace "Wlh ban kawo komai ba sanda na gani, kayi hakuri Dady."
"Nafeesah nasan me kike kokarin yi amma ki sani bakida hakki akan abinda ya faru, iyayenshi sun sani bawai mu mukai dole na, komai munbi ta hanyar da akebi wannan guiltiness din da kikeji yana neman jefa rayuwarki cikin wani hali, sai yaushe ne zaki ajiye komai kiyi rayuwarki?"
Muryarta na rawa tace "Ta ina zan iya Dady? Bayan nasan da taimakon Allah da taimakon ta nake numfashi cikin kwanciyar hankali? A koda yaushe ko fuskarku na gani in na gode wa Allah sai inji adalilina wata kuma ta rasa ranta...."
Ummy ce ta katseta "Nafeesah na dauka munce miki ba a dalilinki bane?"
Hawayenta ta share tace "Ummy!"
Falan ne yai shiru Dady ya danyi gyaran murya yace "Duk inda zaki ki sanar damu, bakisan halin da muke shiga ba in kika fita ba tare da sanin mu ba."
Kai ta d'aga tace "Kuyi hakuri insha Allahu na daina."
Kusa da Ummy ta koma, Dady yace "Khalifa yanata kira ki tashi ki kirashi."
Kamar tace taga Kawu sai dai batasan abinda zaisa a sake matso da auranga, hakan yasa ta mike.

Ayusher Ce🤸🏻‍♂️

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now