Babi na 20

353 73 6
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

Not Edited
*Page 20*

Kwanukan abincin ta bude ta zubawa Dadyn nata ta mika mai spoon, kallanta yai tai saurin rike kunnuwanta alamar bada hakuri. Hannun damansa yasa ya amshi spoon din sannan yai bismillah ya fara ci, mikewa tai ta fito daga falan, takunta biyu taji muryar Ummy a bayanta tace "Kije ki kira Khalifa kinga tun dazu yake nemanki."
Kallan Ummy tai kamar zatai kuka tace "Ummy in ya matsu fa zai sake kira, ni wlh....."
Gaba Ummy tai ta wuceta wanda hakan yasa ta kasa karasa abinda take san cewa, haka tabi bayanta har ɗaki, zama tai a bakin gado itama ta shigo fuskarta duk a turb'une "Kirashi in naga ya d'aga sai na fita."
Baki ta d'an bud'e tace "Ummy zan fa kirashi."
Ajiyar zuciya Ummy tai tana kallanta tace "Sai yaushe kikeso ya cigaba da zaman jiranki? Ko kuwa so kike Yaya yazo gidan nan yaci xarafin mu da ni da mahaifinki? Tun yaushe ake sa lokaci kina sawa ana d'agawa? Yanzu ance shekara d'aya kinci wata d'aya a kalla kya bashi kulawar da zaisa yaga shekarar nan batamai yawa ba, amma inaa ke a ko da yaushe sai dai shi yai ta binki ke ko a jikinki, ko ba nan aka tambayeki kin amince ba kika ce eh?"
Kai ta kauda gefe zuciyarta duk ba dadi tace "Nifa Ummy ba cewa nai bazan aureshi ba ni kawai takira ce banaso, ina da abubuwan yi dayawa a gabana banasan sa zancensa akai......"
Yanda taga Ummy na kallanta ne yasata kasa karasawa "To ko me kike tunani dai ki dinga samu a ciki, akanki fadanda yaya sukai da Dadynki ke kinfi kowa sani, sannan duk abinda zakiyiwa Adnan ya zama hallacin da kikai kokari ne kadai, kada ki bari zuciyarki ta fara raya miki wani abin bayan hallacin nan."
Yanayinta ne ya canza, muryarta tai kasa tace "Ummy?"
Kai Ummy ta girgiza mata tace "Ba cewa nai kinfara ba ina dai sanar dake ne, karki jefa kanki a cikin wani hali, sannan ko mu da kike gani zabinki zai iya jefamu cikin wani halin."
Murmushi tai kafin ta kamo hannun Ummy ta d'aura a saman kanta bayan ta kwantar da kan nata a kan cinyarta tace "Kada ki damu Ummy na, ta ina ma zuciyata zata fara wannan abin? Adnan fa? Ta ɗago tana murmushi tace "Ummy wannan fa ko, bazaki ganeshi ba sai kin zauna dashi ai gaskiyarta ne matarshi ta shiga uku."
Rangwashi Ummy ta ɗan mata kafin ta mike tace "Bari naje na ba Dadynki magani, ina Barira?"
Ajiyar zuciya tai tace "Tanacan arewa na hira da ita a gidan tv."
Harararta tai tace "Ke da ita na rasa wayafi shiririta." Ta karasa tare da barin ɗakin, da kallo ta bita sannan ta zauna a bakin gado tana kallan wayarta da ta buɗo sunan Khalifa.
Daurewa tai ta kirashi, ringing biyu ta sa hannu tana neman kashewa dan dama bataso ya ɗauka, hannunta yakai jikin wayar kenan taji ance "Sweet?"
Yanayin fuskarta ne ya canza ta kara wayar a kunnenta tace "Ya Khalifa ina wuni?"
"Duk kin ɗagamin hankali sai nemanki naki ba labari, saura kadan na sai ticket na taho."
A ranta tace "Da yake bakada aikin yi ba inba haka ba daga kin daukan waya sai siyan ticket da tahowa?" A fili kuwa cewa tai "Sorry na fita ne ashe ba da wayar na fita ba."
Ajiyar zuciya yai ya sake kashe murya yace "Ranki ya dade a taimaka a daina wahalar da zuciyata, anya zan iya jiran dogon zangon nan ba tare da ke ba?"
Takaici ne ya sake kamata tace "Ya Khalifa kafamin alkawari."
"To ya zanyi? Zuciyata tana neman gaza hakuri dake?"
"Hmm" kawai tace dan batasan me ma zatace mai ba, haka yai ta kokarin jan ta da hira sai dai duk inda yai kaucewa take har sukai sallama.
Wayarta ta kalla ta duba lokaci karfe uku na yamma, me Adnan yake? Dan ta tabbatar case din nan ne a gabanshi.

******
ID card dinshi ya nuna mai yace "Am sure ba wanda ya isa ya hanani shiga ciki."
Kallanshi security din yai zaiyi magana yaga yanda Adnan ya ɗaure fuska tamau.
Buɗemai kofa yai Adnan ya shiga aka kira Hajiya Babba, har yanzu hijab din jiya ne a jikinta ta fito idanunta duk sun kumbura da alama tasha kuka sosai bayan yin video dinta tunda idanta garau yake lokacin.
Murmushin takaici tai bayan ta zauna tace "Dama nasan kaine."
Adnan yana kallanta yace "Abinda kima zaɓawa rayuwarki data ýaýanki kenan?"
Hawaye ne suka ziraro batace komai ba yacigaba "In har ke baki damu da taki rayuwarba saboda san zuciya a kalla kya duba rayuwarsu da halin da kika jefasu."
Ɗagowa tai ta kalleshi bakinta ya ɗanyi rawa kawai sai gani yai ta mike tsaye, wato tafiya ma zatai saboda bata damu da abinda ke faruwa ba?
Gwiwowinta yaga ta sa a kasa, mikewa yai tsaye da sauri yace "Me kikeyi hakan?"
Hawaye ne suka shiga kwararo mata kanta na kasa tace "ACP na rokeka da Allah ka taimaki rayuwata, kaf duniyar nan bayan Allah kai kadai zan iya roka, mutanen nan halakamin ýaýa suke shirin yi."
Da mamaki yake kallanta yace "Kamar ya?"
Ta ɗago taba hawaye tace "Bayan abinda ya faru a kotu kuna fita ashe alkalin ma mutumin su Sani ne, nan aka sanar dani in har ba so nake ai kidnapping din yarana a dawo da gawarsu cikin sauki ba na amshi laifi na kuma ce komai nice nai."
Idanu ya ɗan ware yana kallanta yace "What?"
Ta share kwallarta tace "Bakasan wanene Sani ba, a haka zaka iya kamashi sai dai wadanda ke bayansa zasuyi duk abinda zasuyi suga sun fito dashi dan yasan sirrin manyan mutane sama da yanda kake zato, mutanen da duk abinda suka fada a kasar nan ba wanda zai ce a'a."
Mikewa tai tana kallanshi tace "Laifine na riga nayi saboda san zuciya da idanu na suka rufe dashi, na sabawa Allah wanda yanzu gashi ina ganin abinda na shuka, sai dai inada abinda zan baka wanda in har kai amfani dashi duk wanda yake taimakon Sani bai isa ba saboda hujjar mai karfi ce."
Hannayensa ya haɗe yace "Kinsan kinada shi meyasa baki bayyana a kotu ba?"
Ta girgiza kai tana goge fuska tace "Ko na basu bazasuyi amfani dashi ba, sannan zan iya jefa rayuwar iyalai na cikin bala'i saboda shi."
Idanunsa na kanta haryanzu yace "Ni kuma zaki bani?"
"Kai kadai zan iya yarda dashi a wannan lokacin, kai kadai nake ganin zaka iya sawa a hukun tashi, haka kasarmu take irinsu Sani duk abinda zasuyi babu wanda zai hukuntasu. Sannan a ciki akwai shaida akan Nuhu da abinda ya aikata kafin yabar gari."
Yanayinsa ne ya canza ya ɗanyi shiru alamar nazari kafin yai taku biyu zuwa inda take yace "Ina evidence din?"
Zan fadama sai dai zakamin alkawari. "Alkawari?" Ya maimaita cikin mamaki.
"Yarana Adnan, dan Allah ka tsaya musu subar kasarnan, inada kudin da zasuyi amfani dashi so nake kamin alkawari bazaka nuna komai ba sai sun bar kasar nan, sunada visa dan sunada passport na kasar Uk ticket kawai zasu siya ka turasu su tafi."
Sake yin shiru yai yana dan motsa babban ɗan yatsansa kafin yace "Shikenan, sai dai da sharadi nima bazan yi abinda kikeso ba sai kin bani shaidar a hanuna."
Kai ta jinjina sannan tace "Yana cikin gida sai ka samu wanda zai je ya ɗauko ba tare da sun sani ba."
"Wannan ba damuwarki bace zan san yanda za'ai yazo hanuna inda yake nake san ji."
Murmushi tai ta sani Adnan shi kanshi bawai tausayinta yake ba saboda abinda ta aikata kawai ta kaicin abinda tai ne ya kawoshi.
Nan tamai kwatance wanda ya sake tabbatar mai lalai matarnan, dan shi kanshi sai dai recording din kwatancen yai.
Fitowa yai ya shiga mota yai shiru yana tunanin abinyi, dole ne ya ɗauko evidence ɗin nan ya ajiye tun yau dan ya tabbatar Sani yasan tanada wata shaidar. Kafin su sake sata a gaba gwara yai maza ya ɗauke, amma ta yaya? Garba ne zai kuma an riga an kulleshi a gidan yari an yankemai hukunci.
Iska ya furzar ya buɗo sunan dayai wa Nafeesa saving a wayarsa.
Kiranta yai, lokacin tana kitchen ta ɗauko ruwa hannunta ɗauke da magungunanta.
Barira dake ɗakin ne ta ɗaga tace "Assalamu Alaikum, mai sanyin Aunty ne?"
Adnan yace "Sanyi kuma?"
Tasa dariya tace "Na ɗauka mai sanyin Aunty ne na can waccen kasar. Yama?"
"In ta dawo....."
Tsayawa yai da maganar jin muryar Nafeesah ta fizge wayar tare da yiwa Barira dundu, wayar tasa a kunnenta ta shige toilet.
Barira ta saki baki tace "Aunty waya harda shigewa banɗaki?"
Ta zaro ido sannan ta rufe baki tace "Cin amana take irin na film?"
Sum-sum tai ta nufi toilet ta kara kunnenta jikin kofar.
Nafeesah kuwa tana shiga tace "ACP! Tai salute."
Yace "Akwai aikin sirrin da nake so in saki."
Ta kame tace "Okay!"
Nan ya mata bayani a karshe yace "Ya kike gani?"
Kai ta jinjina tace "Mai sauki ne, nasan yanda zanyi, nan da awa ɗaya zani gidan."
"Good! Ko nazo na ɗaukeki?"
Da sauri tace "A'a zan taho sai mu haɗu a layin."
Kai ya jinjina sannan yace "Kicewa wacce ta ɗau wayar daga gun aiki ne ba kankarar bace." Yana kaiwa nan ya kashe wayar.
Baki ta saki tare da sake cewa kankara?
Kofa ta buɗe Barira duk ta saki jiki sai ji kake luu tabi kofar tana neman faduwa, Nafeesah ta tareta tare da jan kunnenta da ɗan karfi tace "Kankara ko?"
Barira tana kara tace "Kankarar me Aunty?"
Nafeesa ta saketa tana harararta tace "Me kika cemai?"
Barira tai kif-kif da ido tace "Na ɗauka mai sanyin kine fa na ɗaya kasar."
"Wai ke bakida aiki zai zancen sanyi? In sanyi kikeso ki shiga fridge ki zauna."
Tai gaba tana ɗaure fuska, Barira ta bita tana bata hakuri......

******
Mika ya sake yi yana ɗan bubuga bayansa kallan Nuhu yai wanda ke ta kumbure-kumbure a gefe yana cika yana sake batsewa.
Tsaki yai yace "Kai banasan shirme bakaji me nace maka bane? Nace ka wuce gidan matarcan ka dubamin ɓangarenta da mutanen da zan baka ku tabbatar kun bincike ko ina na tabbatar akwai abinda take shiryawa a kaina, a yanda nasanta bazata taɓa yarda ta fadi ita kaɗai ba. Banyarda na tura kowa ba saboda ina tsoron kar wanda na tura ya cuceni, kai kadai na yarda dashi dan haka karka min shirme."
"Amma ya zakai da Mumy datace bazata zauna a gidanka ba?"
Wani banzan kallo yamai yace "Uwarka tanada wani bayan ni a duniyar nan? Iyayenta me suke dashi banda abinda na basu? Ko kana tunanin zasu yarda tai yaji? Wannan dalilin yasa ban taba yin gangancin bata gida ba ashe irin ranar nan tana zuwa."
Nuhu ya kalleshi yace "Nidai kome zai faru karka rabu da ita dan bazan iya jurewa ba."
"Kanaso kaima na huce akanka ne ko zaka wuce kai abinda na saka ka? Banda dai ance karna fita saboda wannan dan iskan yaran da mutane da nima da kaina zani."
Nuhu ya mike yana sake hura hacci yabar ɗakin, ya zaiyi? Dole yai abinda Babanshi ya sashi dan da babanshi yake takama.

******

Tanashan magani ta fito ta sanar da Ummy akan abinda ke faruwa, shiru tai tace "Babanki ya fita dan Allah karki dade, duk da aiki ne kinsan hankalinshi bazai kwanta ba saboda jikinki."
Jakarta ta ɗauko ta fito ta tari adaidaita ta nufi layin.
Motarshi ta gani ta karasa gun sannan tai knocking glass ɗin, yana zaune a ciki ya zuge glass yanawa matar dake sanye da mask da glass kallan ikon Allah, haka kawai yaji ya gane kamshin turaren ta, kallanta ya sake yi yace "Na manta ke din actress ce."
Ɗaga glass din tai tace "Dan Allah kasan gidan Hajiya Babba?"
Da mamaki yake kallan rainin hankalin bai bata amsa ba, tace "Bawan Allah in ana tambaya amsa ake jira."
Fuska ya tsuke sosai yana san gane rainin hankalin me take shirin yi.
Nafeesa ta guntse dariyarta tace "Sorry ACP am just practicing. Irin wannan cin magani."
Haka kawai yaji ya samu kansa da yin dariya har fararen hakoransa suka fito. Kallanshi tai zuciyarta na mata dadi, a cikin ranta tace "Da kasan dalilin wa nake tsaye a gabanka da bakamin murmushi ba."
Ganin yanda take kallanshi yasa ya tsuke fuska tare da gyaran murya tana murmushi tace "Yaushe rabanka da dariya?"
Gefe ya kalla yace "Ni ba mahaukaci ba balle ai tunanin ina dariya ba hujja."
Kai jama'a daga tambaya? Abinda zuciyarta ta fada kenan.....

Ayusher Ce🤸🏻‍♂️

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now