Babi na 18

322 78 10
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

08146017245.*promo promo zamuyi muku kyauta inkikasai magani biyu zuwa Sama zamu yimiki kyautar hatsabibiyar hodarmu Domin powder kadai kikai aiki da ita hmmm zakiji bayani agun oga*. *Hohoho sanyifa yazo Saida gyara Mata azo agyara ina Uwar gida ina amarya ina Mata yan kwalisa kuzo Ku Kankaro mutunci da kuma daraja gun oga*. *Duk da dayawa kunsan kayan maman haidar toh nakuma kawomuku na kwarai kayana daga chadi Ake kawon Sudan nijar*. *Muna da nau in magun guna kuma kayan mu na hausane basa cutarwa ko illah saidai su gyaraki kisamu farin ciki*. Ina me neman maganin sanyi sadidan basai natsaya nayi jawabiba kayan mu Kan kat ne. Ina me neman maganin Nono da maganin hips da na kiba korage kiba kuzo akwaisu ingantattu *ina meson maganin matsin ciki Dana waje daciko dagaban mace kaza me allura Dan Shila kasaitacciyar kaza ta yan Sudan ina meson magani mekarawa mace dadi inameson magani me karawa mace ni ima tamkar tana kogi kuma yasa ki fellin Maza zo Yar uwa kihucetakaici kayanmu gangariyane Babu Kar ya aciki kigwada kisha mamaki*. Akwai na mallaka Kala kala akwai na Yan Mata shima . 08146017245.

*Page 18*

Nafeesah duk ta rikice jikinta har rawa yake ta fito daga daki, hanyar waje take shirin yi Barira ta rikota da sauri tace "Aunty? Lafiya?"
Waigowa tai kawai taji hawaye sun fara zubo mata, kasa magana tai kawai tasa hannu ta share kwalla bata kula Barira ba tacigaba da kokarin fita.
Barira a rikice ta koma gabanta tace "Aunty fada kukai da Khalifa? Menene kike kuka? Cewa yai ya fasa zuwa?"
Wani kululun takaici ne ya kamata, ji wani zancen shirme da Barira take mata, ta barta ma da abinda ke damunta zatazo mata da shirmen wani Khalifa?
Kawai takalmi tasa tace "In Umma ta dawo daga barka kice mata na fita ba dadewa zanyi ba."
Yau da kanta ta nufi motarta ta bude ta shiga, har a lokacin idanunta sun kasa daina kwalla, ya zatai? Tausayin Adnan na neman yi mata illa, wannan wani irin zalinci ne?
Kai tsaye kotun ta nufa tai parking ta fito tana sauri mai hade da gudu.
A cikin kotu kuwa Lawyer ne ya kalli alkali yace "My lord banso mukaci karo da wannan mumunan labarin ba amma Adnan dashi da yarinyar nan akwai alaka mai karfi wanda suka hada baki suke neman yiwa Hajiya Babba wato matarshi sharri, kaf mutane sun shaida da kyawawan halayenta amma yaran nan yai mata kazafin kasancewa da yayan mijinta. Sannan saboda shi dan sanda ne bayan Amarya tayi kisa ta kirashi ya tattare shaidu ya nemi yake neman lakabawa Hajiya Babba sharrin kisa ita da Sani Manumfashi."
Adnan gaba daya kansa ya rike ya kasa ko gwagwaran motsi, bai taba tunanin akwai ranar da za'a jefeshi da irin wannan sharrin ba, wannan wani kaskanci da cin zarafi ne, yauce rana ta farko daya fara dana sanin yin aikin dan sanda, kallan kowa yake yanda ake mai kallan kyama, Zaliha kam hawaye kawai take tana girgiza kai dan Muktar ya sanar da ita tana magana zasu illata iyayenta.
Shikam sam baiji sanda Lawyer ke cewa "My lord ina bukatar kotu data bani izini dan na kira Adnan dan ya amsa tambayoyin da zan masa."
Tabashi wani officer yai yace "ACP ana magana."
Kallansa yai lalai abinda ke faruwa ba mafarki bane, yawun bakinsa ya hadiya wanda yaji lokaci daya yamai daci ya.
Zaliha ya kalla tsananin tausayinta ya sake kamashi, inda Hajiya Babba take ya kalla nan danan ya fara tunani, wanene da wannan aikin? Sani ko Hajiya Babba? Shiru yai yana binta da kallo wacce tai saurin dauke idanunta daga inda yake tana sharar kwalla.
Kalmar Lawyern mai shigar da kara ne ya sake dokan kunuwansa "A karo na biyu ina bukatar kotu ta bani izini dan naiwa ACP Adnan tambayoyi."
Mutane har sun fara zindenshi, yana kokari dauke idanu daga gun mutane Nafeesa ta shigo, tana maida numfashi, idanu suka hada na tsawon sakan biyar sannan ya dauke ya wuce ya tsaya inda aka umarceshi ya tsaya, cikin hanzari ta shiga ciki mamaki ya kama Muktar matar data kirashi dazu tana cikin wani hali har yaushe ta karaso nan?
Kafin ya gama tunani har ta karasa inda Adnan yake itama ta tsaya a gefe, cike da mamaki Lawyer din ya kalleta dan sam bai santa ba balle labarinta, yace "Hajiya kotu ne nan muke shari'a me kikeyi a nan?"
Salute tai ta kalli Alkali tace "I am Sergent Nafeesa Aminu, ni ce a karkashin ACP Adnan, duk wani bincike da ni akai, sannan nike da evidence din duk abinda ke faruwa, sannan picture din da aka yada I am his witness shine ya umarcenk na sa Cctv a office dinshi sanda zamuyi binciken sirri da wacce ake zargi a office dinshi, komai ya faru dani akai, bansan ya akai aka yanke inda nake ba akai editing picture dinsu."
A fusace Hajiya Babba ta mike tace "Hardake? Meyasa bamu ganki a video..."
Tunawa tai da abinda take aikatawa da sauri ta hade labanta sannan tace "I mean sorry naga bai kamata nai magana ba, zuciyata ce ke zafi saboda abinda ke faruwa."
Nafeesa ta bita da kallo, Lawyer yace "My lord wannan hujja datake kokari sanarwa da baki bata karbu ba, zancen zube takeyi sannan bataba kotu mahimmanci ba, babu izini tahau magana."

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now