Babi na 16

354 84 13
                                    


*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

08146017245.*promo promo  zamuyi muku kyauta inkikasai magani biyu zuwa Sama zamu yimiki kyautar hatsabibiyar hodarmu Domin powder kadai kikai aiki da ita  hmmm zakiji bayani agun  oga*.                    *Hohoho sanyifa yazo Saida gyara Mata azo agyara ina Uwar gida ina amarya ina Mata yan kwalisa kuzo Ku Kankaro  mutunci da kuma daraja  gun oga*.                      *Duk da dayawa kunsan kayan maman haidar toh nakuma kawomuku na kwarai  kayana daga chadi Ake kawon Sudan nijar*.                *Muna da nau in magun guna kuma kayan mu na hausane basa cutarwa  ko illah saidai su gyaraki kisamu farin ciki*.                  Ina me neman maganin sanyi sadidan basai natsaya nayi jawabiba kayan mu Kan kat ne.              Ina me neman maganin Nono da maganin hips da na kiba korage kiba kuzo akwaisu ingantattu         *ina meson maganin matsin ciki Dana waje daciko dagaban mace kaza me allura Dan Shila kasaitacciyar kaza ta yan Sudan   ina meson magani mekarawa mace dadi inameson magani me karawa mace ni ima tamkar tana kogi kuma yasa ki fellin Maza zo Yar uwa kihucetakaici  kayanmu gangariyane  Babu Kar ya aciki kigwada kisha mamaki*.     Akwai na mallaka Kala kala akwai na Yan Mata shima .    08146017245.

*Page 16*

Sintiri kawai Sani yakeyi a cikin cell din ji yake zuciyar sa kamar zata fashe saboda bacin rai da takaici, kamar shi dan kaskanci a ajiyeshi anan? hannun sa yakai jikin bango ya dan nausa yar karamar kara ya saki saboda azabar dayaji ya shige shi, da sauri ya fara yarfe hannun yana shishitu da bakinsa, in yana zaune yana kallo yana ganin yanda yan film ke nausar bango baisan haka zafin yake ba, idanu suka hada da Hajiya Babba wace ke zaune a cell din Zaliha, mazewa yai ya koma ya zauna ya harde kafa sannan ya sakar mata murmushi, itakam ji take zuciyarta kamar zata tsage saboda ɓacin ran dake yawo a cikinta.
Kai ta ɗauke daga inda yake dan haushin har shi take ji, gani take rayuwarta tazo karshe duk a dalilinsa sai dai ba yanda zatai shi ne kadai xai kwaceta.
Wani mugun kallo ta zabgawa Zaliha wacce tai saurin dauke idanun ta daga inda Hajiya Babban take. Kwafa tai cikin takaici tace "Munafuka na tabbatar kece kika basu hanyar yimin kazafi duk duniya kowa ya shaideni ni mace ce wacce ba ruwanta ko sauro ban taɓa kashewa ba, wallahi sai kinsan ni kikawa sharri sai kuma kinyi dana sanin zuwanki duniya. Tsinaniya munafuka...."
Itadai Zaliha kawai kanta ta sadda kasa tana karzar farcenta tsoro sai sake shigar ta yake.
Can Hajiya Babba kawar wacce aka tsokano tai wani murmushin ɓacin rai tace "Sashar banza shi kanshi saurayin da kike haukar a kansa kudi kalilan muka bashi ya yarda aka ɗau video ɗin da muka ce mun kamashi."
Idanun Zaliha ne ya fara zubar da kwalla akai-akai. Kasa magana tai sai neman tsaida hawayen dake gudu a fuskarta, tana yi tana motsa baki.
Tsaki Hajiya Babba taja tace "In an sake ki uban me zakiyi a duniyar? Ke iyayen ki ma basu damu dake ba, saurayi bai damu dake ba, ki amshi laifi kiyi zaman ki a gidan yari yanda nace kinki, to wallahi sai kin san mu kika munafurta."
Muryar Muktar ce ta katseta ganin yana bude cell din da Sani yake ciki, Sani ya fito yana sa hannu a aljihunsa irin issar nan. Na Hajiya Babba aka bude itama ta fito.
Office din shi yai dasu, leda ya ajiye musu akan tabirin ciki ya bude ciki, gashashen kifi ne yasha kayan hadi sai kamshi yake, sai soyayyen dankali sai juice.
Fita yai ya basu guri, yana fita Hajiya Babba ta rungume Sani cikin rawar murya tace "Habibi ya zamuyi?"
Janye ta yai daga jikinsa ya zauna gyara zamansa akan kujera tare da shafar habarsa yace "Haryanzu ban nunawa yaran nan wanene ni ba shiyasa yake tunanin shi din yaci galaba akaina, wayar sa dake kan table ya dauko ya kira wata number, ringing uku aka ɗauka da alama ba'ai magana ba a bangaren, cike da takama yace "Yallabai haka zamuyi da kai?"
Yanzun ma da alama ba magana Sani yai murmushi yace "In har na aka sake kwana to takardar korar yaran nan ta iso, sannan a ajiyw case dina inba haka ba wallahi dukanku ku shirya dan bazan fadi ni kadai ba."
Daga can ɓangaren yace "Mu muka saka zubar da girmanka? Taya ma dan rashin kamun kai zaka bari a kamaka da matar kaninka?"
A fusace Sani yace "Matar kanina kace, kuma haka kawai bazamuyi magana da ita ba sai a min sharri? Ko kuwa ce maka akai ni mahaukaci ne?"
Daga can ɓangaren yace "Maganar kisa fa? Badai kai ne......"
A zabure ya mike tsaye cikin hargagi yace " Wai kai mai ka ɗaukeni? Kaga malam na fada maka kuma baxan sake maimaitawa ba. Ka tabbatar kun fito dani yau shine magana."
Ya kashe wayar yana furzar da wata iska mai xafi a bakinsa, yaɗan shafi saman goshinsa kafin ya waigo ya kalli Hajiya Babba wace tai tsuru.
Idanu ya runtse yana kallanta yace "Karki damu daga sama za'a rufe case din."
Mikewa tsaye tai tace "Yaran nan kana tunanin zai kyalemu? Yanada shaidu akan mu fa?"

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now