Babi na 8

399 89 9
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*TALAKA DA MAI KUDI*

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

https://arewabooks.com/chapter?id=62854a00ef85a63a21dda994

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS

+447894142004

IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki

Page 8

Adnan ya jinjina kai yace "Wannan aikin mu ne."
Bai jira maganar Sani ba ya kalli yaran yace "Garba ko? Ka jirani na shiga ciki akwai abinda nake san dubawa a dakin mai gidan zamu wuce dakai dan yi maka tambayoyi." Ya mike ya wuce ciki, yana tashi saurayin ya kalli Sani.
Gani nai Sani ya kalli saurayin ya cilla mai key dinsa yace " Wannan key din motata ne gatacan duba bayan motar akwai wasu takardu a envelop ka kwasomin."
Mikewa yai ya amsa ya wuce, ko minti biyu da tafiya baiyi ba dan ko isa baiyi ba Sani ya mike yana kallan mutanen gun yadan ja tsaki kadan yace "ashe a karkashin motar na saka nacemai baya, dole dai sai naje da kaina."
Wucewa yai yabi bayan yaran, yana shiga bayan mota shima ya shiga ya ja ƙofar mota ya rufe, kallan yaran yai yace "Garba!"
Yaran a tsorace ya sunkuyar da kai jikinshi duk ya fara rawa, Adnan dake labe a jikin gate yana kallan abinda ya faru, wannan ya tabbatar mai akwai sa hannun Sani a abinda ya faru sai dai baisan ta ya ya ba.
Mai makon ya shiga ciki kamar yanda yace kawai gani nai ya fito, motar ya nufa kai tsaye, yasa hannu yai knocking din glass din motar.
Sani wanda da alama magana mai mahimmanci sukeyi ya dago cikin wani yanayi, ganin Adnan tsaye a jikin mota yasa yaji gabanshi yayi wani faduwa, shikam baya san yaran nan sam, ya tsaneshi kamar mutuwarsa, yanzu ya zaiyi? Dan ma motarsa mai tint ce, kallan yaran yai yace "Sa kanka a kasa sannan karka fito sai na maka signal."
Yana kaiwa nan ya bude daya bangaren ba gun da Adnan yake ba, hannunsa ɗauke da robar ruwan faro, babbar rigarsa fara ya gyara sannan ya kalli Adnan ya maida kofar ya nufo inda yake, fuskarsa a ɗaure yace "Abinci wannan ban isa inci ba cikin kwanciyar hankali ba?"
Bai kalli motar ba yana kallansa yace "Dama yaran nan Garba nake nema ina san tambayarshi abu akace ka aikeshi."
Tsaki yadan ja yace "Bayanan na turashi siyo abu, da wani abin ne bayan wannan?"
Kai ya girgiza alamar a'a sannan ya juya ya nufi motarsa, Sani yana kallo motar Adnan ta tafi sannan Garba ya fito, sai gumi yake yi kana ganinsa kaga mara gaskiya.
Sani ya mai wani kallan banza yace "Ka hada kayanka yau ɗin nan kabar Kano ka koma ƙauyenku. Zan tura maka kudin da zakai amfani dashi." Da sauri ya daga kai sannan ya koma gun taron mutane.
****
A cikin gida kuwa Nafeesa ta mike sanye da face mask dinta kamar zata fito sai kuma ta koma gun waɗannan mutanen na farko ta zauna, kusa da mai surutun ta zauna cikin abin gulma tace "Can naga matarshi ta biyu tana kuka harda kamar zatai birgima. Oh shidai wannan yayi sa'ar mata."
Ai matar kamar dama jira take a dan tabata, ta juyo saitinta tace "Hmm shiyasa wani sa'in aure-auren nan bashi da wata rana, mata san iya kinibibi, 'yar banzar nan kowa fa yasan bin maza take da kudin mijin kuma, nifa har mata naji labarin tana bi.
Nafeesah ta sunkuyo fuska dauke da mamaki tace Subhanallah"
Tabe baki matar tai tace "Hmm ai kedai ki bari."
Cikin yanayin tambayar da ka matsu kaji amsa tace "Motar data zo jiya ta wanene wai?"
Matar tadan zaro ido tace "Kema kinga motar ne?"
Ta ɗaga kai alamar eh tace "Ai ni ýar uwar Hajiya babbace (wato uwar gidan) jiya nazo kawo mata sako naga motar amma bansamu ganin waye a ciki ba."
Ido matar tadan sake zarewa tace "Haba dai? Ni kuma kinga gidana nan shine ke kallan nasu, ai Hajiya babba mutum ce kowa zai shede ta duk matanshi tafi kowa hankali, kuma darajartane mai gidan nan yakai matsayin da yake dan a koda yaushe karfafa mai gwiwa take."
Ta jinjina kai tace "Allah sarki! Amma kinga mai motar?"
Ta ɗanyi alamar tunani sannan tace "A'a gaskiya dan ciki ya shigo sai dai motar ai akwai irinta a kofar gidan nan anzo da ita gaisuwa, sannan motar ai ta saba zuwa gidan nan, banida tabbas amma daga gidan ɗan uwanshi take, sai dai menene na tambayar motar?"
Tana ɗan dariya tace "Kawai dai, dama na ɗauka ko yaran Hajiya mai neman maza ne."
Ai matar nan ba shiri ta fara kulle baki tana dariya, Nafeesah na ganin haka ta mike, ɗakin Hajiya Babba taje tana kwance sai numfashi har yanzu kawai take saukewa ana kara mata ruwa, cikin tausayawa ta gyara mata bargon dake jikinta, tana neman fita taji ance "Ruwa dan Allah."
Da sauri ta maida mask dinta sannan ta juyo ta ɗau ruwa a gefen gado ta zuba a kofi ta taimaka mata ta ɗagata tasha, tana shan rabi ta fashe da kuka, tausayinta ya kara kamata, kuka take iya kuka, ta dadw tanayi Nafeesah na lalashinta kafin wata ýar uwarta ta shigo, tana ganin haka tai waje.
Menene ya rage mata a gidan? Wayarta ce ta fara kara ta zarota daga jaka, ganin sunan CP Muktar yasa ta koma gefe da sauri ta sa wayar a kunnenta.
Muktar yace "Kina ina?"
Cikin girmamawa tace "Ina gidan gaisuwa ACP ne ya turoni."
Jin yanda ta fadamai gaskiya yasa hankalinsa ya sake kwanciya, cikin bugar ciki yace "Kun sake samun wani clue din ne?"
Ya ɗan sauke ajiyar zuciya tace "Bamu samu komai ba sai wata black gar da akace tazo bayan ýan kawo amarya sun tafi."
Cikin ɗan sauri yace "Kizo office yanzu ina jiranki."
Ɗan karamin salute tai tace "Okay!"
Kai tsaye ta fito, tana hawa kan titi ta hango motar Adnan a gefen titi, tsayawa tai tana dan tunani sai kuma ta basar ta fara neman adaidaita, gani tai ya juyo da kan motar yazo daidai inda take, glass din motar ya sauke ba tare da ya kalleta ba yace "Shigo."
Batace komai ba ta bude ta shiga, tafiya ya fara ba wanda yai magana sai can tadan daurw tace "CP ne yake kirana, sannan matar tace irin motar datazo jiya yanzu ma tana waje."
Idansa na kan titi yace "Motar Sani ce."
Mamaki ya kamata wanda harta kasa ɓoyewa tace "Da gaske dai akwai sa hanunshi a ciki. Amma ba ɗan uwansa bane?"
Bai tanka mata ba hakan yasata yin shiru itama, dazu baki gan ni bane kike neman adaidaita?
"Naganka amma bansan me kake yi ba shiyasa."
Ya dan jinjina kai kadan, wayarsa ce ta fara kara, a tare suka kalli wayar dake ajiye gaban mota, "Reject Call" abinda aka rubuta kenan akan sunan, da sauri ta maida kanta gefe dan abin na neman bata dariya, tunda take bata taba ganin ansa suna irin wannan a waya ba, tanaji ya kashe kiran, ko minti biyu ba'ai ba number ta sake kira nan ma ya kashe. Sai da akai kira biyar sannan sako ya shigo bai ko kalli wayar ba, kusa da station dinsu ya tsaya yana mata magana, ita kuma ta nutsu tana sauraransa. Nikam duk yanda naso naji banji me suke tattaunawa ba.
Tana fitowa ta shiga ciki sannan ta canza kayanta a toilet ta nufi office din CP Muktar.
Tana shiga tai salute cikin jin dadi ya mata alama data matso, yana kallanta kallo irin na kurulla ɗin nan.
Kanta na kasa sai dai jikinta ya bata kallanta yake haryanzu.
"Ke kadai kika dawo?"
"A'a ACP ne ya saukeni."
Jin ta fadamai gaskiya yasa ya sake yarda da ita, mikewa yai yana dan bubuga kujerar da yake kai ya dawo inda take, zama yai a saman tabirin dake kusa da ita yace "Inada kanwa am sure in kun hadu zaku zama kawaye."
Salute ta sake mai ta kame batace komai ba, yadan yi dariya yace "Tunda naga kina wannan aikin am sure iyayenki ba masu hali bane, right?"
Kallansa tai sannan ta jinjina kai tace "Eh CP! Dani suka dogara gashi ba sana'a shiyasa na zabi wannan saboda in basu jin dadi....."
Dariya ya kwashe da ita wanda ya hadata cigaba da bayani, yadan tsagaita yace "Ashe kinsan abinda ya kamata? Sau da dama matan mu na hausawa basu san sana'a mai kawo kudi ba, kinga wannan aikin? Kudi kake samu hankali a kwance in har ka san takan neman kudi."
Kai ta jinjina sannan tace "CP please ka taimakeni ka daurani a hanya."
Fuska yadan tsuke kadan yasa hannu ya dauko wata karamar jaka ya mika mata, hannu tasa ta amsa ta zuge, ganin bandir din 'yan dari guda biyu yasa ta kalleshi a tsorace sannan ta sake kallan kudin.
Daga yanda naga kina aikinki am sure kanki yana ja, sannan result dinki ya sake nunamin hakan. Inaso kisan yanda kikai kika goge duk wani evidences da Adnan zai samu akan wannan case din, komai ya samu ki sanar dani sannan ki wargaza wannan evidences din, daga bangaran wanda aka kashe kuma zasu bukaci ai hukunci cikin gaggawa yanda komai zaizo da sauki.
Ta fahimci sarai abinda yake nufi amma saboda ta kara sashi ya yarda da ita tace "CP kamar me kenan?"
Ya dan gyara zamansa ya hade tafin hannunsa yace "Komai da yakeyi lokacin aiki ki sanar dani har sai sanda ya tafi gida."
Ya buga kafa tace "Okay."
Yace "Duk abinda ya samu, ko hotuna ko videos ko wani ne ya bada shaida ki tabbatar kin kawomin mutumin ko wannan video din na gani."
Ta sake buga kafa tace "Okay CP."
Yace "Sannan duk wani takunsa ki dinga turomin text kina sanar dani."
Ta kalleshi tace "Ko abinci inya fita ci?"
Ya mata wani kallo sai kuma yai yake yace "Eh ko shi, hatta abincin dayaci ki fadamin." Ya karasa maganar cikin gatse.
Nunawa tai batasan gatse yai ba tace "Okay."
Shiru yadan yi yana kallanta cikin jin dadi ta kalleshi tana sake mai godiyar kudi.
Nan ta fito yabi bayanta da kallo yana shafa habarsa.
*****
Kai tsaye gun zamanta ta karasa ta cusa karamar jakar cikin jakarta ta baya da take zuwa da ita, kallan su Auwal tai tare dayin murmushi dan ta kula sai bin abinda takeyi yakeyi da kallo.
Yau tana zaune har suka gama suka fita wajen magrib dan ko Adnan ma ya tashi aiki, ýan sanda biyu da suke aikin dare ne sukazo, mikewa tai ta nufi cell inda Zulaiha take, zama tai kusa da ita sannan ta mika mata ledar pure water na ruwa, gaba daya bakinta ya bushe kana gani kasan bayan yunwa da wahala harda muguwar kishir ruwa, kallan cell din tai mutanen dake ciki jiya duk sunyi bailing su sai ita kadai.
Nafeesah ta dan dafata tare da kara mika mata ruwan, kallanta Zulaiha tai gaba daya ta canza kwana ɗaya kacal. Ba musu ta amshi ruwan ta bude ta kai bakinta, bata ɗago ba dai data shanye ruwan duka.
Dan kafadarta ta bubuga mata saboda kwarewa datai a karshe, ganin ta daina tarin yasa ta kalleta, haryanzu kayan jikinta jini ne, tausayin ta ya kamata, cikin dakewa tace "A haka kikeso mutane su miki shaida har karshen rayuwarki?"
Ɗagowa tai ta kalleta da raunanun idanunta.
"Kinfi so duk sanda aka tunoki a tunaki a matsayin mai kisan kai?"
Idanunta ne suka fara rau-rau, Nafeesa tana kallanta tace "Naju abar batun baki damu da rayuwarki ba amma a kalla bakyasan iyayenki suyi Allah wadai da haihuwarki ko?"
Hawayen da ke kwance a idanunta ne suka fara gudu, hannu tasa ta share.
Nafeesah ma ta goge nata kwallar da suka gangaro tace. "Akwai yarinya karama da akayiwa fyade shekarar ta biyar sai dai duk yanda mukaso mu kwato mata yanci abin ya gagara, har yanzu in na tuno ji nake na tsani kaina."
Ta dan haɗiyi miyau tace "Ke fa? Da girmanki da komai zaki bari a ɗaura miki laifin kisa?"
Kuka ne ya kwace mata nan ta shiga bubuga kirjinta cikin kuka tace "Da laifin kisan kai da abinda akamin duk ɗaya yake a gurina."
Jin wannan kalaman nata yasa hankalin Nafeesah mugun tashi.
Kanta ta kifa tana kuka tace "Bansan laifin da na aikata ba wannan bala'in ya afka kaina ba, ya shiga wanka yaran........" Kawai ta cigaba da kuka iya karfinta.
Gaban Nafeesah ne ya shiga faduwa, ta share kwallarta ta sunkuyo tace "Yaran gidan?"
Kallanta tai wanda ya bata amsar abinda takesanji, bakinta nadan rawa tace "Shiya kasheshi?"
Kai ta girgiza alamar a'a tace "Bansan waye yai kisa ba, yaran dai ya shigo ya ketamib hadina, wanda na tabbatar akwai hadin bakin wasu daga cikin matanshi."
Cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa tace "Ankaini gidan, a al'adarmu ba'a bude fuska harsai miji yazo, wata daga cikin matanshi Hajiya Babba tazo tamib addu'oi tare da fatan alkairi ta kuma min nasiha, suma biyun sun shigo sai dai dukaninsu gulmar kayan dakina sukai akan mijinane ya saimin, ina jinsu sai dai bance komai ba.
Mai makon miji ya shigo kawai naga yaran ya shigo ya sa sakata, nace "Wanene?"
Yana dariya yace "Ai shine mijin wai dama wancan yayanshi ne shi ya nemo mai aurena amma shine angon."
Ni dama ba san auran nake ba to ban damu dakoma waye ba, mai zai faru? Kawai ya matso ya fara tabani, nan na shiga kwacewa shine ya tsinkamin mari daga nan ya shiga mun karfi har sai da......." Ta kasa karasawa tai kuka da takeyi.
Tashin hankali! Nafeesah gaba ɗaya jitai kanta na juyawa, cikin dauriya tace "Meyasa kike zargin matansa?"
Ina kwance hankalina baya jikina sosai saboda azabar danasha naji ana mai magana cikin raɗa a jikin kofar wai ya fito ga mai gidan nan. Shine ya ja bargo ya lulubeni.
Haka ina kuka na maida kayana da kyar kawai na cusa kaina cikin bargo ina kuka. Inajinsa ya shigo yanatamin magana har ya bude kaza yana min magiyar na sauko naci abinci, kuka yaki tsayamin na mike a gune na shiga bandaki. Wallahi daga nan bansan abinda ya faru ba kawai fitowa nai naganshi akan gado ba rai......
Kuka take iya karfinta kamar ranta zai fita, Nafeesah ma duk yanda taso ta maida kwallarta ta kasa, wannan wani irin bala'i ne? Yau me takeji da kunnuwanta?

******
Adnan kuwa ko da ya fita yawo yai unguwar kafin ya nufi gida, yana parking din motarsa yaga alamar kwan wuta da alama mutanen gidan basuyi bacci ba kenan, mai makon naga ya fito daga mota sai gani nai ya kishingida akan kujera ya ɗan daura hannunsa akan goshinsa alamar tunani.
Jiyai an bude motar da sauri yadan dago fuskarsa a ɗaure.
Jingina tai da jikin motar yadan kashe mai ido tace "Surprise!"
Keyarsa ya shafa yace "Me kike anan?"
Tadan turo baki cikin shagwaba tace "Sai kiranka nake kaki ɗauka shiyasa na biyoka."
Yana kallanta yace "Makarantar fa?"
Cikin shagwaba tace "Karatu ni baikai matsayinka ba a gurina."
Kafafunsa ya zuro ya fito daga motar ya maida ya kulle bai ko tanka taba ya nufi ciki, bayansa ta biyo har ya nufi bangarensa, ɗan daki ne da bandaki.
Yana shiga yaga tana neman shiga da sauri ya sa hannu ya rike kofar yace "Ina zaki?"
Tace "Ciki mana? Ya Adnan aurena fa zakai? Sannan ni ýar uwarkace menene in na shiga ɗakinka?"
Yana kallanta fuska a ɗaure yace "Da farko ke ba ýar uwata bace, ƙanwar matan gidan ce, sannan na biyu zan aureki kikace shima ba tabbas."
Tana kokarin magana taga ya maida kofar ya rufe, rai a ɓace ya cila jakarsa kan gado sannan ya wuce toilet.

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now