Babi na 21

553 92 11
                                    

*Binciken Sirri*........ 👮🏽👮🏾‍♂️

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️*

Not Edited
*Page 21*

Salute tai tace "Sorry Sir!"
Fuskarshi a daure tamau yace "Am sorry but I need to report this."
Ido ta zaro ta sauke hannunta tace "Daga wasa? Gwajin acting fa nai?"
Kafada ya daga alamar oho yace "Wannan ba damuwa ta bace, baki girmama ni ba a matsayina na oganki, dan haka dole ne nai discipline dinki."
Kasa magana tai ta tsaya tana kallan ikon Allah, wayarsa ya ɗauko ga mamakinta sai ji tai yana cewa "Muna bukatar discipline committee saboda Nafeesa."
Kauda kai tai tana ji zuciyarta na wani irin zafi lalai mutumin nan yaci darajar wacce take darajawa a duniya da wani ne batasan ma mai zatamai ba.
Jitai ya furzar da iska ko kallan gun batai ba saboda takaicin abinda yake neman yi mata "Ashe dai acting din mutum baiyi karfi ba, how far? Ashe dai na fiki iyawa."
Waigowa tai ta kalleshi, wayarshi ya dan jijiga wanda ke kiran wayarta, kafada ya sake dagawa yace "Actress a shiga ai aiki ni ina nan zan tare duk wanda ya rigaku fitowa." Bai jira mai zatace ba saboda yanda ya barta a kame, ya matsa da motarsa gefen gidan Hajiya Babba.
Ta glass ya ke binta da kallo haka kawai kasan ransa yake ta dariyar lamarin.
Nafeesa kuwa murmushi tai tabi motarsa da kallo cikin mamaki, kwafa tai tace "1:1 nima a jira nawa shigar."
Harta shiga gidan idanunsa na kanta, haka kawai yaji ya kasa dauke idanunsa daga kallanta, sai data rufe gate din yai murmushi, mai gadi ne ya taso dan sam bai kula gate din a bude yake ba, dan su Nuhu sun shiga ya tafi fadanci bai tsaya ya kula da gate din ba."
Kallansa tai cike da murmushi kamar ta saba dashi tace "Malam Mamman ai na dauka kana can kana dafa shayin naka da ka saba."
Idanunsa dauke da mamaki yake kallanta yace "Ban gane ki ba?"
Kai ta girgiza tana murmushi tace " Malam Mamman ka manta nike kawo kaya ai gidan nan, yau sukace nazo na amshi kudina saboda rasuwar da akai."
Tunani yakeyi yana dan sosa bayan kai, dariya tai tace "Ikon Allah Mamman kaima dai mutuwar nan ta tabaka, ina Garba? Ai shi yake shiga dani duk sanda nazo, to inata kiransa a waya bata shiga ba."
Jin haka yasashi dariya yace "Ah haba? Shiyasa na kasa ganeki, bismillah."
Ajiyar zuciya tai a bakin kofar gidan tana sakewa gidan kallo da tunanin yanda zata shiga, mayafin abayar ta tagyara sannan ta runtse ido tana karanto addu'a.
Gidan ta kwankwasa, mai aikin gidan tazo ta bude, kallan Nafeesah tai cike da mamaki, ID card dinta ta nuna mata tace "Ni police ce inhar bakyasan ki dau laifi ki barni na shiga ki kuma rufe gidan kamar ba wanda ya shigo."
Yar tsohuwa jin anyi maganar police yasa tsoro ya kamata, shiga tai ita kuma ta rufe gidan jikinta har karkarwa yake, kai tsaye bangaren Hajiya Babba ta shiga tana tafiya cikin sanda, tana shiga falo taji alamun maganar namiji.
Da sauri ta shiga ɗaki ta ɓoye a bayan wardrobe din dakin tana dan sauke numfashi kadan, mamaki ne ya kamata ganin an turo kofar ɗakin, hakan yasa ta sake rage sautin numfashinta, idanunta ne suka sauka akan Nuhu yana bude drawer, takaici ne ya kamashi ya shiga watso da komai na ciki, ganin babu yasa shi yin tsaki, da alama waya yakeyi da AirPods din dake makale a kunnensa cikin fishi yace "Dad nifa na kasa gani, duk na gaji na duba ko ina banganshi ba."
Tsaki Sani yai yace "Duba kasan gado."
Nan Nuhu ya duba, yace "Nan ma fa babu."
Ajiyar Zuciya Sani yai yanajin zuciyarsa na sake tafasa, yace ka kalli dakinta dakyau bakaga gun ajiyar abin sirri ba? Inhar ka nemo na ma alkawarin sai ma sport car din da kake so."
"Dad kayi alkawari?"
Yace "Nayi, har kudi zan karama dashi."
Ya jinjina kai yace "shikenan. Sai ka jini."
Da alama kashe wayar yai nan ya shiga bincike iya karfinsa yake bi ko ina yake bincikawa, banda nishin gajiya ba abinda kakeji duk ya hargitsa dakin.
Bajewa yai a saman gadan dayai kaca-kaca dashi yana maida numfashi dan ya gaji sosai.
Idanunsa ne suka kai kan saman drawer din dakin wanda ke dauke da wani karamin akwati, mikewa yai ya ja kujerar gaban madubi ya kai gun sannan yai tsalle ya dauko akwatin.
Ajiyar zuciya yai ciki dan jin dadi yace YESS! Sai dai basan numbobin da zai bude akwatin ba, tsaki yai yace "Haka nan zan kaimai yasan yanda zaiyi."
Nafeesah dake bayan drawer tunda taga ya dauko akwatin nan ta runtse ido, kallan inda take ta shiga yi tana tunanin abin yi.
Gyara mayafin abayarta tai ta maidashi kamar nikaf a fuskarta, ya juya yanata neman balle akwatin ya kasa, yaja tsaki.
Zai juyo yaji an makamai abu a fuska, a zabure ya gigice ya sake kokarin juyowa, Nafeesa ta sake daga jakarta ta sake makamai iya karfinta.
Zubewa yai a kasa nan danan jikinshi ya hau rawa dan yaji zafin dukan, zai sake juyowa ta sake kwadamai, a rikece ya cusa kansa cikin gwiwowinsa yana neman yin kuka dan shikam yaki shigar dukan nan. Nafeesa ta dauki akwatin sannan ta sake kwada mai jakar nan. Tsoron dagowa yake dan tabbas yanda yaji zafin nan baisan me zai faru ba in har ya dago, yana gani andan tsaya yai sauri ya mike itama tana ganin haka ta futa da gudo ta rufo kofar, rike kofar tai iya karfinta.
Nan da nan ya shiga bugawa yana ihu "Wallahi ko wacece sai na sa an kulle ki, ai naganki sarai macece, wallahi sai kinsan ni kika raina. Dan abu takazar ubanki ni zaki daka?"
Jin ihu yasa matan gidan suka fito, Nafeesah najin alamun mutane ta saki kofar ta boye a bayan labulen falan.
Sai data bari sun wuce hanyar daki sannan tai saurin fita.
Shi kuwa Nuhu sam baisan ta saki kofar ba, yana tsaye ya kama kwankwaso yana zabga masifa "Dan gidan ku bakiji me nace miki ba ko? Ko bakisan ko ni wanene ba?"
Jin shiru yasa yakai hannu kofa zai bude suma suka bude kallan kallo suka shiga yi, mamaki ya kamasu a tare sukace "Nuhu?"
Nafeesah tana ganin sunyi kansa ta karasa ta bar bangaren tai hanyar waje tana maida numfashi, Mamman na mata magana ai bata kulashi ba da sauri ta fita, kai tsaye motar Adnan ta nufa yana hangota yai maza ya bude mata kofar gaba, tana zuwa ta shiga motar shi kuma kawai yaja ba tare da yayi magana ba.

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now