Page 7
*NEW YORK CITY*
5th Avenue,East 41st street,
6:00am: 2012,
Wanni saurayi ne Wanda akalla bazai wuce shekara Ashirin a duniya ba, (bare chest)well build body figure furiously on a treadmill,putting on a headphone, a yanayi fuskar sa kadai zai tabbatar ma dacewa yana cikin fushi.Wanni saurayi ne ya shigo dakin da tab a hanunsa tsaye agaban sa, saurayin dake treadmill Ya cire headphone dake kansa da sigan bacin rai ya daga giransa daya ke nuna alamar mai..? saurayin dake rike da tab yace..
"Your Dad ya fada yana mika Mai tab din hanunsa.. "
Saida ya sauka ya goge jikin sa da small towel yasa black tight body hug insa kafin ya amsa wayan..
"Wani datijo mutum ne ya bayyana a kan screen din wayar with a smile on his face yace;
"Hello son, I've been trying to reach out ya' since hope you're good..?Shuru yayi nadan wani seconds kafin yace good Dad.. "
I called to know if you are ready to... Bai bari ya karasa ba yaron yace I've nothing to do there Dad, Dad that's my final decision..."
Haba Al'ameen Yanzu kana numfi saidai mu zuba masu ido su tafi Scott free? Bayan kawai sheda zaka bada kasan da cewa na boye ka ne sabida ranan irin tayau please ka sake tunanin akai,I Have a say now so you need not worry son.. "
Shuru yayi ya kura ma mahyfinsa ido yana kallon abinda yafaru 15yrs flashing back at him yanayi yadda jijiyoyi sa suka fito baro baro ne zai nuna cewa a hassale yake ganin yadda wayan dake rike a hanunsa yake nima fadi yasa Adams amshe wayar a hanunsa ya dade cikin wannan yanayi kafin ya koma bedroom insa yasa lock zama yayi kasa hanunsa duka biyu a sama kansa sai jagule gashin kansa yakeyi can ya dago da jajawur idonsa mai kama da garwashi wuta bude side drawer sa yayi ya dauko kwalin cigarette insa ya kuna yafara zuka a hankali a haka saida yasha sanda uku kafin yaji Dan dama, wucewa bathroom yayi ruwan na zuba kansa bai San sanda ya furta cewa Get ready for me.. "
*AIDAH*
Can kuma tayi shuru tana kallon saBaiwar ALLAH..." mallam Iro ya kirata dashi "
Shuru tayi Tana kallon sa
Baiwar ALLAH ya sunanki...?
Sunana Ma'idah..!
Kallon dansa yayi yana murmushi kafin yace ma'idah daga wana gari kk
Shuru tayi kafin tace Nima Bansani ba
Toh ya sunan iyayen naki..?
Shima cewa tayi batasani ba komai aka tambaye ta cewa takeyi batasani in banda sunan Mulayf da sunan ta da ta Kira bata sake kira sunan kowa ba
Toh Ma'idah mu zamu tafi kiwo ALLAH ya kara lafiya
Amin baffah..."
Yaji dadin yadda ta kirasa da baffah kamar yadda sauran ya'yansa ke ce masa sai yaji takara kwanta mai rai
Su malam na wucewa Laure ta shigo toh maza ki fito kizo kiyi wanke wanke tunda Yanzu kina iya zama..."
Toh ummah.."
Ke ni ba ummah ki bace kije can ki nime ummah ki amma ba Laure ba..
Da kyar ta mike Tana dafe dafe harta issa inda wanke wanke yake sabida haryanzu ji takeyi jikinta kamar bana ta ba especially kafanta bata wani dauki time ba tagama aikin ta koma dakin da kyar kamar mai koyar tafiya tana kwanciya ba dadaiwa Laure ta sake shigowa
Keee Uban wa zai zo yana miki girki kina kwance? bacin kowa ya tafi talla maza ki fito ki kama min aiki Zanje can in dawo
Fitowa tayi Tana gyara wutan karan da aka daura girkin akai, yau mallam iro da wuri ya dawo sabida wanni cinwo Kai da ya adabe shi da sallama yashigo inda yaci Karo da Ma'idah abakin Murhu
