68

367 31 4
                                    

*💔MAFARKINA💔*
         *(MY DREAM )*

       *BY*

          *🤍THE DMK's🤍*
                (MissDmk✍🏻)

ELEGANT ONLINE WRITERS ✊🏻

Page 68

Inna lillahi wa ina ilaihi rajiun nafada ina hawaye

Don ALLAH kiyi kokari kuje ku ceci Sarki dasu Gimbiya mulayfa...na barki lafiya yana fadin haka ya bace, da salati a bakina nafarka na daura idon a sama fuskarsa ya wani kyamkyame ni kamar his whole life depends on me..

Kokarin janye jikina nakeyi amma nakasa da karshe dai sakin mai kuka nayi, cikin voice din barci yace what?

Wanda ya bani rayuwa mai inganci yana can cikin hukuba..
Wanda ya ilimantar dani yabani tarbiyya yana can cikin... Ban karasa ba ya Mike yana kallona cike da mamaki abinda nake...

Ni butulu ce, naci amanar yarda da yayi min, ya nuna min so kamar yadda wa zai wa kanwarsa, ya so ni fiye da yanda miji zai so matarsa, duk wannan wahalar da yashiga sabida nine da ace banyi sakaci Da amanar sa ba, da Yanzu muna tare dashi sabida shi din ba mugu bane nafada magana Ina kuka mai cin rai...

Janyo ni jikinsa yayi yana patting ina, kiyi hakuri in shaa ALLAH zamu saka mai da abinda ya miki...

Yana cikin mayuwanci Hali, Yanzu haka anacan ana azabtar dashi duk sabida ni, yanzu ne yakamata nasaka mai alkhair da yayi min koh da hakan yana nufi rasa rayuwa na ne...

Ina fadin haka naga yaja jikinsa daga nawa yana min wanni irin kallo mai wiyan fassarawa.. can yace da ace Mulayf mutum ne zaki so shi..?

Kallonsa nakeyi ina mamakin Tambayasa...kuma  bance masa komai ba...

Hmmmm! yace nasan da ace shi mutum ne zaki aure shi kuma ki soshi ya fada magana da murmushi a fuskar amma murmushi mai fassara na daban..

A'ah bana jin sonsa a Raina amma nasan yana da matsayi na musamman a rayuwata...

No. Feel free to say what's on your mind, nasan zaki so shi Inda ace shi mutum ne Ma'idah...

No. He needs us now Mr Amazing... Shiyasa but I've no feelings for him..

Jin ta kirasa da Mr Amazing yaji hankalin sa ya dan kwanta, in shaa ALLAH honeydew zamu taimaka mai, Yanzu how do you feel? Koh zaki ga likita?

Ni yanzu kwanciyar hankali na shine naga Ya Mulayf ya dawo yanda yake... Inda ta nine bazan taba samu lafiya ba indai Ya Mulayf yana can yana  wahala sabida ni...

Shiryawa mukayi muka nufa gun Mal. Ayub ya gaya mana abinda yakamata muyi kafin mu shiga yanki,

Adu'oi Ya bamu da ruwan adu'a musha sannan ya umurce mu da yin alwala kafin mu shiga duniyar su....godiya mukayi mai kafin

Muka wuce gun Gimbiya Zayyah muka sanar da ita cewa yau zamu, iya abinda ta sani shine ta gaya mana tabamu mukulin kofar dazai leading in mu...

Nanne da Ummi kam sai kuka sukeyi kamar mutuwa zamuyi, iyayen mu maza kam sun bamu baki dakuma fatan nassara... Abu kamar a film sai gamu an raka mu har secret door din, da bismillah Mr Amazing yasa key kofar ta bude, muna sa kafa aciki kofar ta rufe ba abinda muke gani sai Haske da kukayen tsuntsaye dana dokuna, ba abinda mukeyi sai adu'a har muka fara gani halittu masu ban tsoro, ina boye ajikinsa saide kamar su basa ganin mu... Tafiya mukeyi har muka Kai Zum..

Wannan shine Zum Inda muke haduwa da Ya Mulayf nafada ina nuna mai, tafiya mukeyi a tsorace har muka issa fadar Inda muka ga masu gadin fadar masu rikitarwa da ban tsoro..

💔MAFARKINA💔Where stories live. Discover now