page 19

264 24 0
                                    

*💔MAFARKINA💔*
         *(MY DREAM )*

       *BY*

          *🤍THE DMK's🤍*
                (MissDmk✍🏻)

ELEGANT ONLINE WRITERS ✊🏻

Page 19

Can kuma sai yaji tafiyan dogarai da sauri ya riske su kafin su karaso kwasan gaisuwa sukayi kafin sukace ana bukatar ka a fada Kira ne na gaggawa...!

Kallon su yayi kafin yace lafiya dai...?

Jikin Mai martaba ne yatashi yana...Bai bari ya karasa magana ba kamar kyabtawar ido sai Gashi a fada,

Gimbiya mulayfa daman tana boye a bishiyan Ganin ya tafi shine tasamu damar shiga mafarkin Aidah inda ta tura Ainee dauko zoben harta samu damar sakamata a yatsa (don't be confused guys, nan farkon labarin yadda Gimbiya mulayfa ta shigo mafarkin Aidah harta dawo mata da zoben..)

Mulayf kam na dakin mai martaba tare dasauran yan uwansa jikin Sarki Malik yatsanata Sosai da kyar yasamu ya kira sunan Mulayf yace lokacin Hutuna yayi Mulayf Yanzu Lokacine dazaka daura daga inda natsaya, Mulayf inaso kazama mai adalci da kamanta Gaskiya Sarki Ansa sa da jarumta ta da kwazo wajan mulki karka bar son zuciya takai ka ta baro Ɗana Don nasan tunanin ka shine yadda zaka dawo da Junaid da kawun ka yanki mu, karka yi haka yin haka zai ja zalunci da kashe kashe a wannan yanki sannan kazama mai iya tsabtace Zuciyar ka dakuma kokarin toshe duk wacca kofar na Rudun Zuciyar ka, sabida kasan Yanzu kana da karfin da koh tunanin kayi baka aikata da hanu ba zai aiwatar nasan duk kasan komai tunda ankoyar dakai komai acan, dafatan zakayi afanin da abinda nace..?

In shaa ALLAH mai martaba, Kara adu'a yayi a zam zam dake kofi yashafa mai aduk jikinsa yana sauke ajiyan zuciya yaga kowa Annan amma banda kakarsa..."

Suna zaune wasu da zan iya Kiran su da malamai sarauta, kallon mutane ciki sukayi kafin sukace lokacin hutun mai martaba yayi Yanzu Lokacine dazai gana da sauran yan'uwa sa sarakuna, Kubamu waje zamu shirya shi izuwa dam-dam kai kuma magajin Sarki ka tsaya! kowa ya watse masu kuka nayi..."

Mulayf na tsaye yana taya malamai shirya mahyfin sa kowai yaji heartbeat insa ya karu lumshe ido yayi kafin ya daura hanun sa daidai setin Zuciyar sa ya furta Aidah under his breath yaji duk wanni bacin rai ya gushe sai wanni farinciki ne mara misaltuwa ya ziyarce shi da murmushi yake kallon mahyfin sa yace Abbah zanyi kewarka Sosai.. "

Murmushi Sarki Malik yayi yana rike da hanun Mulayf yace watarana zamu sake haduwa ai amma kafinan sai ka zama jajirtace mai kaifin basira can yace ku bani gu zanyi magana da da'na duk suka fice suka rufo masu kofar,
Sarki Malik yace ina jin bugun Zuciyar ka ɗana, banso ka fada soyayya wannan bugun Zuciyar alamu ne kana kokarin fadawa soyayya... "

Shuru Mulayf yayi yana kallon mahyfin nasa can yace Abba ai zabin dakayi min ne dukkan su biyu inaso son su... "

Murmushi karfin Hali Sarki Malik yayi yace banga haka a idonka ba akwai Wacce dai take shirin mallakar Zuciyar ka, karka bar hakan tafaru zai iya zama ma babban kalubalai agare ka..."

Nagode Abba in shaa ALLAH bazan hakan tafaru BA, A hadaden gado da yasha kwaliya aka tafi da sarki Malik ba wanda suka ga tafiyar sa sai Mulayf, sati daya akayi ana shagalin biki auren Sarki Mulayf ga cousins insa Gimbiya zahira da shunum(sati daya Annan shine wata daya aduniyar Aidah kar wacca tace tayi confused 😜)

Gimbiya mulayfa da Ainee kam sunata shirin su batare da kowa yasan abinda suke shiryawa ba sake Komawa gun Aidah tayi don Ganin Aidah bata yada zoben ba sannan ta kara mata kaishedi(zuwanta na Biyu shine sanda Aidah ke barci a class)duk a kwana biyu Gimbiya mulayfa tayi komai tagama amma a duniyar Aidah kuwa kwana hudu kenan da zuwan Gimbiya mulayfa ..."

💔MAFARKINA💔Where stories live. Discover now